Abubuwa 5 da ke samar da mai
Mutane
da yawa na amfani da mai a babura da injina da motoci da sauransu, wanda a
yanzu komai zai iya tsayawa cik idan har aka ce babu mai, hakan ne ma ya sanya a
shekarar bara da Shugaba Jonathan Goodluck ya kara kudin mai al’ummar Najeriya
suka rikice, komai ya balgace, inda kuma kasashen Yamma ke fafutikar mamaye kasashen
da suke da arzikin mai. Shi mene ne mai? Da yaya ake samunsa kasancewar mutane
da yawa suna amfanin da shi ba tare da sanin ko ta yaya aka same shi har aka hake
shi ba? Me ya sa ake samun mai a wani wuri ko kasa amma kuma ba a samu wani
wuri ko kasa?
A
wannan mukalar zan yi gamsasshen bayanin da zai amsa wadannan tambayoyin da na
zayyano a sama ga masu karatu har su fahimci yadda abubuwa biyar ke haduwa su
samar da mai. Idan aka samu hudu daga cikin biyar din to ba za a kai ga hakar
mai ba.
Da farko ina so masu karatu su sani,
ana samun mai daga dutse ne, kuma duwatsu a duniya sun kasu kashi uku ne, akwai
dutsen igneous (igniyos) da dutsen sedimentary (sedimentari) da kuma dutsen
metamorphic (metamofik), ba za a samu mai ba sai a dutsen sedimentary. Ba wai
daga an samu dutsen sedimentary za a samu mai ba, a’a sai idan muhallin ya zama
sedimentary basin (sedimentari bazin), wato an samu kwayoyin duwatsu da suka
zama shimfidu daga dutsen mafari (misali, shale) zuwa dutsen tafki (reservoir
rock, misali sandstone) da sauran shimfidun duwatsu.
Ba lallai ne daga muhalli ya zama
sedimentary basin kuma ya samar da mai ba, a’a sai an samu abubuwa biyar a
muhallin, wadannan abubuwa biyar sun hada da: (1) Dutsen mafari (Source Rock)
misali, ‘shale’ (shel), sai (2) Dutsen Tafki (Reservoir Rock), misali sandstone
(sandsiton), sai (3) Zafi (Geothermal heating) yadda za a furta- (Jotamal
hitin) da (4) Kaura (Migration) yadda ake furtawa- (Maigireshin), sai kuma (5)
Tarko (Trap).
(1)
Dutsen mafari (Source rock)
Shi
ne dutse na farko da yake zama matakin samuwar mai. Misalin wannan dutse shi ne
shale. Idan dutsen shale na kunshe da sinadaran Hydrocarbons (sinadaran da ke kunshe
da carbon) ya zama mafarin dutse. Wasu kan tambaya da yaya ake samun shale?
Akan samu shale a lokacin da kwayoyin duwatsu da ake kira sediments suka hadu a
wuri daya daga karshe kuma sai su dunkule su zama dutsen shale. An fi samun
wannan dutsen a muhallin da ake kira Lacustrine (lakostarain) ko Deltaic
(deltaik), wato muhallin da ya hada da tafki da korama da kududdufi da teku da
sahara da sauransu.
Wannan
dutse ya karkasu zuwa kashi uku bisa ga bambancin sinadaran hydrocarbons da
suke kunshe a cikinsa. An kuma yi rabe-raben ne bisa ga sinadarin kerogen da
sauransu.
1
Dutsen shale kan zama dutsen mafari (source rock) ne a lokacin da kwari ko
dabbobi da ke rukunin algal suka makale a wurin da babu iska sosai (anodic), an
kuma fi samun irin wadannan duwatsu a karkashin tafki.
2
Na biyu, dutsen shale kan zama mafarin dutse (source rock) idan kwayoyin
bakteriya suka ruvar da halittun cikin teku da ake kira planktonic a kuma wurin
da babu iska, sukan bayar da iskar gas da kuma mai idan akwai zafi, idan kuma
suka shige cikin karkashin kasa.
3 Dutsen shale kan zama mafarin dutse
idan kwayoyin bakteriya da na fungi (fungai) suka ruvar da dabbobin tudu kamar
su kakan kadangaru (dinosaur) da tsire-tsire a cikin kasa, kuma idan ba su rika
samun iska ba. Irin wadanan duwatsu kan samar da kwal da sauransu.
Kafin
dutsen shale ya zama dutsen mafari sai idan yana dauke da sinadarin kerogen
kashi 0.5 a cikinsa, amma kuma yakan zama dutsen mafari mafi kyau idan yana kunshe
da kashi 12 zuwa sama a cikinsa. Misalin dutsen shale a Najeriya shi ne, Fika
Shale.
(2) Dutsen tafki (Reservoir rock)
Shi ne dutse na gaba wanda yake zama ma’ajiyar mai bayan ya
yi kaura daga dutsen mafari (source rock). Yana kunshe da kofofi da tarko masu
yawa da ke hana man yin kaura bayan ya shiga cikinsa. Misalin wannan dutse shi
ne, sandstone, a Najeriya akwai Gombe Sandstone.
Wannan hoton na nuna yadda mai yake kaura daga dutse mafari zuwa dutsen tafkin mai.
(3) Zafi (Geothermal Heating)
Akwai wani zafi da ke taimakawa wurin samuwar mai, shi
wannan zafin ake kira geothermal heating. Zafin da ke samar da mai ya fara daga
60 zuwa 150 a ma’aunin degree centigrade (digiri sentigiret), ana auna ma’aunin
degree centigrade ne bisa ga nisan dutsen a cikin kasa.
Masana binciken kasa sun ce wannan zafin na samuwa ne a karkashin
kasa tun lokacin da aka samar da duniya, wanda a yanzu kuma zafin rana da ake
kira solar (sola) da kuma ruvewar sinadarai a cikin kasa ke samar da shi. Zafin
da aka samu wurin dutse mai aman wuta da girgizar kasa na taimaka wa zafin da
ke samar da mai. Masana sun ce zafi a cikin kasa daga kafa 10 zuwa mita 3 yakan
kai 12.8 a ma’aunin degree centigrade.
(4) Kaura (Migration)
Kaurar mai na taka muhimmiyar rawa wurin samuwar mai har a
kai ga hakarsa. Akwai hanyoyi da yanayi da suke sanya mai ya yi kaura. Akwai kaura
ta farko da kuma ta biyu. Ta farko ita ake kira primary (firamari maigireshin)
migration, ta biyu kuma ita ce secondary migration (sakandare maigireshin). Kaura
ta farko takan faru daga dutsen mafari zuwa wani dutsen mafari, kaurar mai ta
biyu kuma takan faru daga dutsen mafari zuwa dutsen tafkin mai. Masana sun ce
samuwar kwayoyin da suke ba da shimfidu (layers) ta hanyar bisnewa na haifar da kaurar mai, samuwar
bisnewar ake kira burial (buriyal).
Misalin tarko, a tsakiya mai ne a taskance
Zayyanar shimfidun duwatsu da ke samar da mai. A kasa dutsen mafari ne, sai ruwa da mai a cikin dutsen tafki, a saman dutsen tafki kuma tarko ne (dutsen Rock seal)
Ga yadda kaurar mai ke faruwa daga mashimfidar dutsen mafari
(source rock) zuwa dutsen mafari ko zuwan dutsen tafki (Reservoir rock):
Idan zafi ya rika karuwa zai sanya sinadaran hydrocarbons su
rika motsawa. Kamar yadda ruwa yake motsawa idan aka dora shi a wuta sakamakon
zafi. Inda kuma masana suka ce hakan na faruwa a sakamakon bisnewa da ake yi kwayoyin
da suka samar da shimfidun duwatsu walau na mafari ko na tafki.
Idan zafi ya karu sai sinadaran hydrocarbons su narke, inda
wasu kuma sukan zama kamar gas. Hakan sai ya sanya su mamaye dutsen. Misali, za
a tuna yadda idan aka dora tukunya a wuta aka kuma sanya danwake a ciki lokacin
da ya tafasa yakan cika har ya fi karfin tukunyar har sai an rika fifitawa. To
kamar haka ne yake faruwa ga sinadaran hydrocarbons.
Idan za a iya tunawa mun ce dutsen mafari (source rock) na dauke
da kofofi (Pores), to ta cikin wadannan kofofin ne sinadaran hydrocarbons wadanda
suka narke suke yin kaura zuwa ko dutsen mafari ko kuma dutsen tafkin mai.
Yawan samuwar kofofi ake kira High Porosity (hai forositi) hakan kan kawo mai
mai yawa ya yi kaura cikin kankanen lokaci.
Baker (1980) wani masani kan mai, ya ce ruwa na taimakawa
wurin samar da kaurar mai, kasancewar a kowane lokaci idan aka hada ruwa da
mai; mai na kasancewa a saman ruwa, kuma idan ruwa ya rika motsawa mai ma zai
rika motsawa. Ya bayar da hujjar cewa kowa yana tabbacin akwai ruwa a cikin kasa
wanda ake kira (underground water), wanda kuma shi ya sa ake samun ruwa idan an
tona rijiya. To ruwan da yake cikin kasa ne a lokacin da yake motsawa sai ya rika
motsa mai har ya sanya ya yi kaura.
Wasu masana sun ce ruwa ba ya taka rawa wurin samar da kaurar
mai, suka ce a lokacin da zafi ya narkar da sinadaran hydrocarbons, akwai
sinadaran da suke fara narkewa inda kuma kasancewar sinadarin kerogen ne ke
samar da mai, to sai wadannan sinadaran da suka narke su rika tafiya da
sinadarin kerogen, wadannan sinadarai kuwa kan yi kaura ta kofofin da ke jikin
dutsen mafari. Masanan da suke yarda da hakan akwai Tissot da Welte,
1978 da Hunt, 1979 da kuma McAuliffe 1979.
Wadansu masana
kuma sun ce idan zafi ya turara sinadaran hydrocarbons sai su fara karo da juna
hakan ne kuma zai sanya su rika yin kaura ta kofofin da ke jikin dutsen mafari,
masana da dama sun amince da wannan hanyar sai dai Dickey 1975 da Magara 1980
ba su yarda da wannan hanyar ba.
Amma dai koma
wace hanya ce duka masanan sun yarda idan har babu kaura to kuwa ba za iya hakar
mai ba, sun kuma yarda zafin ne yake sanya mai ya yi kaura.
(5) Tarko
Jama’a da dama
kan yi mamaki shin me ya sa ba a samun man fetur a kowane wuri, ba ya ga haka
kuma tun da mai kamar ruwa ne me ya sa ba ya tafiya daga wannan gari zuwa
wancan? Ko kuma me ya sa ya tsaya a wurin daya kawai? Amsar dukkan wadannan
tambayoyi ya ta’allaka a kan abu daya wato samuwar tarko. Tarko ne ke taimakawa
wurin taskance mai a wuri daya ba tare da ya motsa zuwa wani wuri ba. Akan
samun tarko ne ta hanyar girgizar kasa da tsunami, an samu tarko lokacin
samuwar duwatsu da ake kira orogeny, sannan an samu tarko lokacin da aka samar
da duniya kamar yadda masana suka ce. Su wadannan tarko su ake kira faults da
folds da kuma dutsen cap rock (kaf rok). Sakamakon abubuwan da na lissafo a
sama sai a samu mafarin dutse ko tabkin dutse ya lankwashe wato ya rika hawa da
sauka har ya bayar da surar folds, ko ya karye ko kuma ya rubza. Karyewar ko
rubzawar dutse ko shimfidar dutse ake kira faults, lankwashewar dutse kuma ake
kira folds. Wani lokaci a kan samu tarko idan dutsen cap rock ya kasance a
saman shimfidar ko dutsen tafki. Dutsen cap rock kan hana fitar mai bayan ya
shiga shimfidar ko dutsen tafkin mai. Wannan dutse baki ne, suwal-wal kuma ba
shi kofofi a jikinsa.
Samuwar mai
A nan zan yi bayanin yadda wadannan abubuwa biyar da na
lissafa suke haduwa su samar da mai. A lokacin da dutsen mafari ke shigewa
cikin kasa sakamakon samuwar sabbabin kwayoyin duwatsu (sediments) a samansu,
yanayi kan canza, wanda a lokacin da suke waje akwai iska, amma a lokacin da
suke kara shiga ciki babu iska, sannan yanayin yakan kara zafi, wannan zafin da
kuma rashin iska sai ya sanya sinadarin Kerogen da ke cikin dutsen mafari ya
fara dagwargwajewa. Wannan dagwargwajewar ake kira cracking (kirakin).
Masu magana sukan ce idan gyada ta sha matsa sai ta yi mai,
don haka a lokacin da aka kara samu wadansu duwatsu a saman dutsen mafari
(source rock) sai nauyi ya sanya sinadarin Kerogin ya fara fitar da mai,
musamman ma idan akwai isasshen zafi.
Wani abu da nake so mai karatu ya fahimta shi ne, akwai kofofi
a jikin dutsen mafari, inda kuma sai mai ya rika ya rika naso walau zuwa wani
dutsen mafari ko kuma dutsen tafki. Wannan nason da yake yi shi ake kira kaura
(migration). Bayan ya yi kaura ne sai ya shiga dutsen tabki, wanda kuma da ma
yana dauke da tarko, wannan tarkon ne zai taskance man. Daga nan sai a gudanar
da bincike bayan an tabbatar da samuwar mai sai a hako shi.
A shekarun baya an yi ta samun jan-kafa wurin aikin hakar
mai da ke yankin Tafkin Chadi, inda wadansu suka yi hasashen babu mai a yankin.
Hakan ya sanya zan yi bayani kan samuwar mai ko akasin hakan a yanki Tafkin
Chadi (Chad Basin) da ke Jihar Barno, zan yi bayanin ne bisa ga abubuwa biyar
da na lissafo a sama.
Dutsen mafari
Tafkin Chadi na kunshe da dutsen mafari da ake Gongila ko
Fika Shale. Shimfida ko dutsen Gongila na dauke da sinadarin hydrocarbons kashi
1.5 a cikinsa, inda kuma dutsen ko
shimfidar Fika Shale ke dauke da sinadaran hydrocarbons da ya kai kashi 0.9 a
cikinsa. Masana sun ce idan har shimfida
ko dutse mafari ya samu kashi 0.5 na sanadarin Hydrocarbon to zai iya zama
dutsen mafari.
Dutsen Tafki
A bisa ga bayanin da masana suka yi sun bayyana dutse ko
shimfidar dutsen Gombe Sandstone da Keri-Keri na da inganci ko nagartar da za
su zama dutsen tafki. Wadannan shimfidun
duwatsu suna dauke da kofofi da kuma tarko da za su iya taskance mai.
Zafi
Sakamakon bincike da aka gudanar an gano
dutsen mafari yana da nisan mita 300 a karkashin kasa, sannan akwai zafin da ya
kama daga 60 zuwa 120 a ma’aunin digiri centigrade (Degree Centigrade), idan ba
za manta ba na ce zafi daga 60 zuwa 150 ne ke iya sanya sinadaran hydrocarbons
su fara narkewa. Idan kuwa haka ne tafkin Chadi ya cika sharadin zafin da zai
iya narkar da wadannan sinadarai.
Kaura
Bincike ya bayyana akwai kofofi (pore spaces)
a jikin dutsen mafari na Fika Shale, don haka bisa ga tabbatacin akwai isasshen
zafin da zai iya narkar da sinadaran hydrocarbon, to kuwa akwai kofofin da wadannan
sinadarai za su iya kaura. Baya ga haka a jikin dutsen tafkin mai Gombe
Sandstone da kuma Kerri-Kerri akwai hanyoyin da man zai iya shiga.
Tarko
Alkaluman bayanai kan samuwar duniya sun
bayyana an samu tarko a Tafkin Chadi cikin shekarar Jurassic da kuma Santonian.
Santonian da Jurassic wadansu shekaru ne da suka taka rawa wurin samuwar
nahiyoyin duniya. Wadannan shekaru suna cike da ayyukan samuwar duwatsu da
zaizaiya da lankwashewa da kuma karyewar shimfidar duwatsu, wannan ayyukan ake
kira tectonic activities (tektonik aktibitis). Wadannan ayyukan ne suka samar
da tarko a tafkin Chadi.
Wannan ita ta kawo karshen takaddamar walau
akwai mai a Tafkin Chadi ko babu. Ina ba mai karatu tabbacin akwai mai a Tafkin
Chadi sai dai kawai a hako shi.
Bashir Musa Liman
07036925654