Wednesday, July 23, 2014

Dalilan da marubuta littattafan Hausa suka koma rubuta labaran fina-finai



Ga wadanda suka dade suna bibiyar fina-finan Hausa, sun kwana da sanin irin yadda harkar ta fuskanci matsalar ingantattun labarai. A lokacin ba a rubuta labarin fim (script), sai dai a rika maganganun cikin fim da ka, inda darakta zai rika fada wa jaruman fim din abin da za su ce.
Jarumi Ali Nuhu ya ce, ba wani abu ya sa ake kiransa mai girman ba, face ya ce ba zai yi fim ba tare da an ba shi labarin fim a rubuce ba, ya ce ba ’yan kallo ba ne suka fara kiransa da mai girman kai ba, a’a, wadansu ’yan fim ne bayan ya ce sai an ba shi labari a rubuce. Dalilinsa na cewa hakan kuma shi ne, don a samu labarai masu inganci.
Ya ce ba a dade ba sai ’yan fim suka fara ganin fa’idar a rubuta labari. Wadanda suka kira shi mai girman kai, suka ba shi hakuri domin sun fahimci dalilinsa.
Aminiya ta tattauna da wadansu marubuta kan dalilan da ya sa suka canza akala daga rubuta labaran littattafan Hausa zuwa na fina-finai.
 Jamil Nafseen
Ado Ahmad Gidan Dabino
Ado Ahmad Gidan Dabino, shahararren marubucin littattafan Hausa ne, inda ya rubuta littattafan da suka hada da ‘Inda So da kauna’ da ‘Kowa Da Ranarsa’ ya ce ya fara rubuta labaran fina-finan Hausa ne, bayan masoyansa sun bukaci ya yi hakan.
Ya ce: “Da farko ni marubucin litttattafai ne, bayan jama’a sun karanta litattatafaina sai suka ba ni shawarar in mayar da wadansu fim, akwai wadanda suka ce za su dauki nauyin mayar da su fim ma.  Hakan ya sanya na rubuta labaran fim da suka hada da ‘Inda So da kauna’ da ‘Kowa Da Ranarsa’ da ‘Mukhtar’ da kuma ‘Cinnaka.”
 Ibrahim Birniwa wanda shi ma fitaccen marubuci ne ya ce ya fara sha’awar rubuta labaran fina-finai ne don ya yi wa jama’a hannunka mai sanda, har a samu al’umma tagari.
“Dalilin da ya sanya na koma rubuta labarin fim shi ne, sakamakon wani mataki da fim din ya kai, wanda masu shirya fina-finai suka fara tunanin, ya kamata su rika amfani da ingantattun labarai, wadanda suke cike da tsararrun maganganu wajen shirya fim dinsu. Baya ga haka yanzu idanun mutane suna kan harkar fim.
“To, tun da ana bukatar kwararrun marubuta sai abokina Nazifi Asnanic ya sa in rubuta masa labarin fim din ‘Labarin Zuciya’, wannan ce ta sanya na shiga harkar fim, har ma na kasa ci gaba da rubuta littattafai.” Inji Birniwa.
 Jamil Nafseen ya ce ya fara kwadayin kasancewa marubucin fim tun lokacin da ya fara rubuta litttafi.
Fauziyya D Sulaima

Ya ce: “Harkar rubuta littattafai da fim, danjuma ne da danjummai, duk hanyoyin adabi ne mikakku da marubuci zai isar da sakonsa. Na fara kwadayin kasancewa marubucin fim tun sa’ilin da na fara rubuta littafi, amma ban samu damar haka ba sai daga baya.”
Nafseen wanda ya ce ya rubuta fina-finai 280, wadanda suka hada da ‘Rarrashi’ da ‘Ameera’ da ‘Sawun barawo’ da ‘Jarrabi’ da ‘Shakka’ da ‘Ka So A So Ka’ da ‘Ba Zan Bar Ki ba’ da ‘Ni Dake Mun Dace’ da ‘Halwa’ da sauransu  ya ce a Najeriya ne marubucin littafin Hausa ne za ka same shi mafi kololuwa a rashin samun kudi.
“Sakon murubuci ba zai isa inda yake so ba, sai akwai kudi. Kuma a kasuwa ake tarwatsa kudin marubuta, duk marubucin littafin da ya yunkuro kasala ta farko da take nannade jikinsa ita ce, rashin samun taimako don ya wallafa ayyukansa. To duk yadda ya kai ga son fitar da rubuce-rubucensa don jama’a su karu, sai ya zama babu damar yin hakan.”
Fauziyya Suleiman ta ce sha’awa ce ta sanya ta karkata akalarta daga zuwa rubuta labaran fina-finan Hausa.
 “Sha’awa ce ta sanya na fara rubuta labarin fim. Na jima ina sha’awar ganin yau na rubuta labarin fim, amma sai nake ganin ba zan iya ba. Wata rana Ibrahim Birniwa ya zo taron marubuta, sai ya ce mana ana bukatar marubuta a masana’antar fina-finan Hausa. Kamar da wasa ya fara koya mana yadda ake rubutawa. Da haka na koya, har na zama marubuciyar fina-finan Hausa.” Inji ta.
Ta ce ta rubuta fina-finai 40, a cikinsu akwai ‘Maijego’ da ‘Uwargida’ da ‘Lubna’ da  ‘Zarge’(sabo) da ‘Bagidajiya’ da ‘Alkawari’ da ‘Dare’ da ‘Rumaisa’ da sauransu.
Yanzu abin tambaya a nan shi ne, shin harkar rubuta littattafan Hausa ta mutu ke nan, tun da tuni sauran marubuta irin su Rahma A Majid da Nasir Nid da Bala Anas Babinlata da Nazir Adam Salih da Maje El-Hajeej da Dauda Shafi’u Giwa da sauransu suka koma rubuta labaran fina-finan Hausa?

Bashir Musa Liman
07036925654