Friday, May 4, 2012

A hoton sama: Bashir Musa Liman ne yake zabga kirarin Hausawa a garin Issele-uku da ke Karamar Hukumar Aniocha ta Arewa.
Hoto na kasa: Bashir Musa Liman sanye da doguwar riga ciki kabilar Ibo, a lokacin da aka gabatar da ranar al'adun gargajiya ta masu yi kasa hidima (NYSC) a Jihar Delta.
Alayin gaba daga dama na biyu, Bashir Musa Liman, bayan ya gabatar da wata lacca mai taken: Hausa People Rite de Passege: Pre, Syn and Post Jihad in Northern Nigeria. Venue: College Of Education Azare.  

Matakan da ake bi wajen rubuta karbabbiyar waka


MATAKAN DA AKE BI WAJEN RUBUTA KARBABBIYAR WAKA (POEM).
Ba tun yau ba, na lura da irin kura-kuran da suke ta faruwa a wakokin mawakanmu. Da na yi bincike da nazari ne, na gane hakan yana faruwa ne, a ta dalilin yawancin mawakan haye suke yi wa waka, ma’ana ba sa tsayawa don fahimtar yaya zubi-da-tsarin waka yake (Peotics), ya  dokoki da kuma hanyoyin da suka  jibanci waka suke (Lyricism).
Wasunsu ba su san mene ne yake sanya waka ta zama karbabbiya ba, a lokaci guda ba su san mene ne ke rusa waka ba. Shi ya sa wani lokaci za a ji wakoki sakakaka, marasa kan gado, ba tare da an fahimci ina suka dosa ba. Da na kara nazari ne, sai na fahimci cewa wasu mawakan damuwarsu abin da za su samu, wanda hakan ne ya rufe musu ido, wajen neman ilmi a kan waka. Na kuma sake fahimtar cewa mawakan suna da lalaci wajen yin bincike da kuma nazarin ya za su inganta wakokinsu.
            Rubutun da zan yi a yanzu, yana dauke da matakan da ake bi ne wajen gina ko rubuta ko kuma shirya karbabbiyar waka. Ga matakan kamar haka:
(1) KARIN WAKA (Mood and Tone)
            Ana so mawaki ya kasance ya samu karin waka na musamman, wanda ya tabbatar zai gamsar da masu saurare ko karantawa. Ya kuma tabbatar da karin wakar ya dace da wakarsa. Bayan mawaki ya samu karin wakarsa, to ana so wakar ta ci gaba da shi ba canzawa  har zuwa karshenta. Idan mawaki ya yi waka ba karin waka, to ba ta da maraba da tadin baka ko abin da ake kira zube (prose). Wanda yanzu mawakanmu suna cikin waka da karin waka, sai ka ji kuma sun canza, sun ci gaba da wani kuma. Wani ma sai ka ji an yi amfani da karin waka uku ko fin haka a cikin waka daya. To a nan, ina shaida wa masu yin hakan cewa, yin hakan kuskure ne, wato sun karya dokar waka, walau rubutacciya ko kuma wakar baka.

(2) JIGON WAKA (Theme).
             Tilas ne, mawaki ya tabbatar da wakarsa tana da jigo, ma’ana ginshikin ko kuma muhimmin abin da wakarsa za ta yi batu a kai. Ana so mawakin ya tabbatar da cewa wakarsa tana da manufa, wato ta zama tana da muhimmin sakon da take isarwa ga jama’a. Misali, wakar Mu’azu Aliyu Hadejiya mai taken MU YAKI JAHILCI, wanda jigon wakar shi ne, illolin da jahilci ke haifarwa.

(3)  MABUDI DA MARUFI (Introduction and Conclusion).
            Ana so, mawaki ya tabbatar da wakarsa, tana da mabudi da kuma marufi. A nan ana nufin wakar ta fara da yabon Ubangiji da kuma salatin Annabinsa (SAW), a lokaci guda kuma a rufe ta da su. Misali, a wakar Mu’azu Aliyu Hadejiya ta GASKIYA BA TA SAKE GASHI:           

MABUDI:
   Ya Allah Sarki mai rahama,
   A gare Ka muke son albarka.

Domin tsarkin Dakin Ka’aba,
Albarkar Annabi manzonKa

MARUFI:           
Ya Allah taimaki bayinka,        
 Duk wanda yake son manzonka.

 Mu’azu Hadejiya nan ya tsaya,
V.T. mai neman albarka.
(4)  MA’AUNI (Metre).
Ana so, mawaki ya sama wa wakarsa ma’auni. A nan ana nufin ma’aunin da zai kasance ya auna wakarsa, wanda ta hanyar amfani da ma’auni ne, za a iya yayyanka waka, kana baitotinta su kasance kai-da-kai, ba kai da gindi ba. Idan muka koma ga tarihi za mu ga cewa, wakoki a kasar Hausa sun samu kafuwa ne daga wakokin larabci, kasancewar ba a san wakoki a kasar Hausa ba, sai bayan zuwan musulunci da ilmin larabci kasar Hausa. Waka ta samu tagomashi sosai lokacin Shehu Usman Danfodiyo, shi ya sa tun daga lokacin har zuwa yanzu, za ka samu ma’aunan wakokin kasar Hausa suna da nasaba da ma’aunan wakokin larabawa. Ma’aunan wakokin larabawa goma sha uku (13) ne, wanda ga su kamar haka: (1) Dawil (2) Madid (3) Basid (4) Wafir (5) Kamil (6) Hajaz (7) Razaz (8) Ramal (9) Munsarih (10) Hafif (11) Mukutalib (12) Mutakarab (13) Mutadark

(5)  AMSA-AMO (Rhythm).
Ana so, mawaki ya yi wakarsa da amsa-amo, wanda a larabce ake yi wa lakabi da kafiya. Ma’ana ana so waka ta kasance tana da harafi iri daya, wanda da shi ne baitukan waka za suna karewa. Amsa-amo ko kafiya ta kasu kashi biyu ne: karama da kuma babba. Karamar kafiya, ita ce ake samu a tsakiyar baitin waka, yayin da babbar kafiya take zuwa a karshen baitin waka. Karamar kafiya tana iya sauyawa a kowane baiti, amma babbar kafiya ba ta sauyawa, da ita ake tafiya har karshen waka. Misali, a wakar IMFIRAJI, littafi na daya, Juzi’i na daya, na Aliyu Namangi:

            Gaisuwa ko ta dace,
            Gun Ma’aikin nan da an ce,
            Ran Musulmi kar shi sance,
            Bisa sonsa mu ko amince 
           Mai sonsa ba zai bakin ciki (ba).
Idan aka lura za a ga na ja layi ga wasu haruffa; harrufan da na ja wa layin su ne karamar kafiya, idan za a lura harrufan sun kare da ce ne. Babbar kafiya kuma za a gan ta a cikin baka-biyu.

(6) SHIRIN BAITOCIN WAKA (Versification).
Ana matukar so mawaki ya shirya baitocin wakarsa, bisa ga dangogin wakoki, wanda sun kasu zuwa bakwai (7) ne. Amma waxansu sun ce ba su da iyaka, ya danganta da irin yadda mawaki ya tsara baitukan wakarsa ne. Ga waxansu misalai kamar haka:

− Gwauruwa (Single):
Kamar yadda aka ji daga sunanta, ita wannan waka tana da baiti mai dango dai-dai ne hade da babbar kafiya. Ma’ana duka baitukan za su kare da harafi iri daya ne, tun daga farko har zuwa karshen wakar. Ma’ana tun daga yabon Ubangiji, salatin annabi har zuwa inda ake ambaton sunan mawaki (singer’s name) ko kuma tarihin waka (poem’s history) ko yawan baitin waka (total number of verses of the poem) da kuma rufe wakar. Misali, wakar Malam M. S. Sulaiman Zariya, mai taken YABON MANZO (SAW), wanda aka buga a jaridar Aminiya (Juma’a 20, ga watan Nuwamba, 2009):

            Jalla Ya saukar da shi tsararre ba gauraya.
            Gagara gasar makwaikwaya yau ma har da jiya.
            Rabbi ya aiko shi du kana yaki Nahiya.
            Bautar gunki kuma ana kashe jaririya.
            Ya hana bautar gunki Allah Wahadaniya.
            Ba ya son raina dai mahaifi da mahaifiya.

Idan an lura da kyau za a ga cewa duka baitukan wakar da ya suka kare, hakan ne ya nuna cewa wakar gwauruwa ce mai baiti dango dai dai.

  − ‘Yar tagwai (Twin):
Wannan waka ce mai baiti dango bibbiyu, tana dauke da karamar kafiya da kuma babbar kafiya. Karamar kafiyar kan canza a baitukan wakar, amma  babbar kafiya ba ta canzawa har zuwa karshen wakar. Misali, wakar Mu’azu Aliyu Hadejiya, mai taken ILMIN ZAMANI:

     Kar su fara fadar da-na-sani
     Da mun yi karatun zamani
     Allah Shi zai gyara mana,      
     Ya fitar da mu kunyar zamani.

− ‘Yar uku (Triplet):
Wannan waka ce mai baiti dango uku-uku. Tana dauke da karamar kafiya biyu, kana da babbar kafiya a karshen baitin wakar. Misali, wakar Bashir Musa Liman mai taken  MU RIBACI LOKACI:

            Ubangiji ke da lokaci,
            Mai kuma canza lokaci,
           Cikin mutane ba mai ikon hakan.
─ ‘Yar hudu (Quadruplet):
Waka ce mai baiti dango hudu-hudu. Tana dauke da karamar kafiya uku, sai kuma babbar kafiya a karshen kowane baitin wakar. Misali, wakar Haruna Aliyu Ningi, mai taken SIYASA:

Siyasa riga ce, tsayinta iyakacin mama,
Mai wandon gilashi, tsiraici ba ta kare ma,
Tana sa mutum teba, ta sa shi yai rama,
Ta sanya mutum ya ci bai gode Allah ba.

─ ‘Yar biyar (Pentatonic):
Ita kuma wannan wakar tana da baiti dango biyar-biyar ne, tana dauke da karamar kafiya hudu da kuma babbar kafiya daya a karshen kowane baitin wakar. Misali, wakar Mu’azu Aliyu Hadejiya ta BIRRUL WALIDAINI:
                Bin iyaye wajibi na,
                Babu mai raina batuna
                Barakal lahu alaina,
                Arziki ba ya gudu na,
                Sai da birrul walidaini.

─ Tahamsi:
Wannan wakar ta bambamta da sauran wakoki. Waka ce mai dango bibbiyu da wani mawaki daban ya yi, ana cikin haka sai wani mawaki kuma daban ya zo ya kara mata dango uku, wanda daga karshe za ta koma mai dango biyar. Wannan wakar idan har ba an yi wa jama’a bayani ba ne, ba za su iya gane tahamsi ba ce, domin za a dauka ‘yar biyar ce, kasancewar ba ta da bambanci da ‘yar biyar indai a bisa ga saurare ne ko karantawa. Ana gane wakar tahamsi ce, ta hanyar samun bayani daga wanda ya yi wa wakar tahamsi. Misali, wakar MA’AMA’ARA ta Shehu Usman wanda Maibodinga  ya yi wa tahamsi:
            Idan na yi shu zucciya ba ta fashi,
            Garin yin tunani na so na gane shi,
            Idan sallama nij jiya sai in tuna shi,
            Tutuf gaisuwata awa ni da shi,
            Awa na yi zamne ga fuska tasa.

─ Tarbi’a:
Wannan wakar ma ta bambanta da sauran wakoki, domin asalinta mai baiti dango bibbiyu ce (‘yar tagwai), ana haka sai wani mawaki kuma ya kara mata dango bibbiyu , sai ta zama mai dango hudu (‘yar hudu). Ita ma idan ba an yi wa mai saurare ko karantawa bayani ba, da ganin ido ba zai iya gane ta ba, domin zai dauka ‘yar hudu ce, kasancewar ba ta da bambanci da ‘yar hudun. Misali, wakar Isa dan Shehu, wanda Muhammad Awwal ya yi wa tarbi’i.

            ‘Yan musulmi kui mana hanzari,
            A mu zam ka yabo gun gafiri,
            A mu gode badini, zahiri,
           Jama’ag ga karimi kadiri.
Don haka ne ake so mawaki ya gina wakarsa daga daya daga cikin cikin shirin baitocin da na zayyana a sama, don gudun samun nakasu a wakarsa

(7) AMBATON JIGON WAKA
Ana so mawaki ya ambaci jigon wakarsa, tun a farkon wakarsa. Ma’ana ya sanar da masu saurare ko karantawa makasudin wakarsa ko kuma abin da wakarsa za ta yi magana a kai. Misali, idan a kan auren dole ne, sai ya bayyana wa da jama’a jigon wakarsa shi ne, illolin auren dole ko kuma a guji auren dole ko kuma ya nuna rashin amfanin auren dole dai sauransu.
An fi so mawaki ya ambaci jigon wakarsa tun a farkonta, wato bayan ya kammala yabon Ubangiji da kuma salatin Annabi (SAW). Misali, a wakar Bashir Yahuza Malumfashi mai taken BARKA DA SALLAH:

Yau kam muna murnar Sallah,
Babbar rana godiya ga Allah,
Ranar masoya ga Jallah,
Dole muyi kwalliya Wallah,
Farin ciki burin zuciyata.
Malam Bashir ya kawo wannan baitin ne, bayan ya yi yabo wajen Ubangiji da kuma salatin Manzon Allah, wanda hakan yake nuna wakarsa a kan bikin Sallah zai yi.

(8) WARWARAR JIGO (Theme Treatment)
Ya zama dole mawaki ya warware jigon wakarsa a cikin wakensa, ma’ana ya yi bayanin jigon wakarsa daki-daki kuma filla-filla, wanda hakan ne zai bai wa masu saurare ko masu karantawa damar fahimtar mai wakar mawaki take karantarwa. Misali, idan wakar a kan ilmi ne, sai mawakin ya yi warwarar jigon wakarsa ne, zai bai wa mutane damar ganewa, shin yana kira  a nemi ilmi ne, ko kuma rashin neman ilmi ga abin da zai haifar da dai sauransu.
Ana so mawaki ya ci gaba da warwarar jigon wakarsa har zuwa karshenta, amma an fi so mawaki ya tsaya a baiti na kusa da na karshe, saboda a baitin karshe ne, ake ambatar sunan mawaki, tarihin wakarsa ko kuma yawan baitukan waka da dai sauransu. Misali wakar ILMIN ZAMANI ta Mu’azu Aliyu Hadejiya, mai baituka 77. Idan za a lura tun daga baiti na biyu (2), ya fara warwarar jigon wakarsa har zuwa baiti na saba’in da uku (73). Misali:

            Baiti na biyu (2):
            Ilmi shi ke gyaran kasa,
            Har a santa a wannan zamani.

Baiti na saba’in da bakwai (73):
            Ilmin addini na gaba,
            Ilmi na bin sa na zamani.

(9) SUNAN MAWAKI
A nan, ana so mawaki ya ambaci sunansa, yawan baitukan wakarsa da kuma tarihinta a karshen wakarsa. Amma wasu masana da kuma manazarta waka sun ce, idan mawaki ya ambaci sunansa da kuma tarihin wakarsa, ko kuma sunansa da kuma yawan baitukan wakarsa ma ya wadatar. Abin da yawancinsu suka yi magana a kai shi ne, mawaki ya ambaci sunansa a waka, kuma an fi son ya ambaci sunansa a karshen wakarsa. Amma wasu sun ce ko da zai ambaci sunansa a farkon wakarsa da kuma karshenta ma babu laifi. Misalin inda  mawaki ya ambaci sunansa, wakar  Mu’azu Aliyu Hadejiya, mai taken ILMIN ZAMANI:

            Shi Mu’azu Hadejiya shi ya wal-
               llafi, wannan wakar zamani.

Baiti saba’in da guda bakwai,
Tammat da nufin Babban Gwani.

A wakar Bashir Musa Liman kuma mai taken AUREN DOLE, ya ambaci sunansa ne da kuma tarihin wakarsa, ma’ana shekarar da ya kirkiro wakar. Misali:

            Bashiru dan Musa ne,
            Ya tsara wakar auren dole.

Wallafar shekarar 2004 ce,
            Da nufin a guji auren dole.

(10) SALON WAKA (Style)
Ana so salon wakar mawaki ya kasance mai karfi, ma’ana ya kasance bayaninsa ya zama mai kama hankali da gamsarwa da kuma ankararwa. Ana son salon waka ya zama babu kakale ko ci-da-karfin kafiya, wato ya karya kalma ko ya cusa kalma don baitinsa ya tafi daidai da salon wakarsa. Ana so mawaki ya kasance mai karya waka a wajen da ake karyawa, mai kuma dora waka a wajen da ake bukatar yin hakan. Ba a so mawaki ya wahalar da masu saurare ko karantawa, wajen gano abin da yake nufi; ana nufin ya yi amfani da kalmomin da za a iya saurin fahimta, kasancewar burin mawaki shi ne, a fahimci sakon da yake son isarwa. To matukar ya yi amfani da kalmomin da  za su wahalar, to karshe ko an fahimci sakon da yake son isarwar, zai zamana  masu saurare ko karantawa za su ji wakar ta gundire su.

(11) NUNA GWANINTAR HARSHE. (Folk sayings and Diction)
Ana so mawaki ya rika nuna gwanintar harshe a wakarsa, wanda zai iya hakan ne, ta hanyar lakantar kalmomi; iya furta su ta hanyar gwalan-gwason zantuka da dai sauransu. Misali ana so mawaki ya kamanta wani abu da wani irinsa wanda ya fi shi kyau ko karfi ko girma ko kuma ban mamaki. Zai iya amfani da tagwan kalmomi ma wadanda ma’anoninsu suka bambanta. Ana so mawaki ya rika aron ma’anar wata kalma ya bai wa wata. Ana so mawaki ya rika jefa karangiya (Rhythm/Rhythm), ma’ana sassarka wasu kalmomi masu sauti iri daya cikin baitin waka, misali, Danko miko tarko da koko a loko...  Idan zai yiwu a wakar da ta jibanci wani, to ana so mawaki ya rika yin gugar zana, ma’ana bayyana aibin mutum a gabansa a fakaici. Ana so mawaki yana jefa karin magana (Proverbs) a cikin wakarsa. Ko amfani da siffatau kai-tsaye (Personafication) ko siffatau mai-kama (Simile) da sauransu.

(12) AMFANI DA KA’IDOJIN RUBUTU (Orthography)
Yana da matukar mahimmanci ga mawaki ya yi amfani da ka’idojin rubutu, wanda hakan ne zai sa a fahimci wakarsa ba tare da ya darsa tunanin shin me mawaki yake nufi ga ma’abocin karantawa ba.  Ma’ana ta hanyar yin amfani da Alamar Motsin Rai (!) ne, za a gane cewa abin da mawaki ya rubuta ya shafi motsuwa ko sosuwar rai ne, wanda a nan za a gane, razana ce ko mamaki da dai sauransu. Hakazalika ta hanyar alamar Tambaya (?),  za a gane mawaki yana yin tambaya ce ga ma’abocin karanta wakar,  kamar yadda idan ya yi Wakafi (,) yana nufin a dan ja numfashi a wakar, kafin a ci gaba. Idan ya sanya Aya (.) kuma na nufin baitin wakar ya kare. Har ila yau, idan ya sanya alamar Zancen Wani (“ ”) na nufin abin da ya rubuta din nan wani ne ya fada ko ya rubuta ba shi ba. Da dai sauran ka’idojin rubutu da za su fitar da ma’anar waka. Don haka yin waka ba tare da ka’idojin rubutu ba tamkar manomi ne yake tafiya gona babu fartanya.

(13) RABA KALMOMI DA KUMA HADA KALMOMI (Words Margin and Divisions).
Ana so mawaki ya kasance ya nakalci kalmomi, wanda ta haka ne zai iya sanin yadda za a hada kalmomi da kuma wajen da za raba kalmomi. Abin da nake nufi a nan shi ne, wasu mawakan rashin iya bambancen yadda ake rubuta gajeriyar mallaka da kuma doguwar mallaka na damunsu. Yayin rubuta karamar mallaka ana hade kalmomi ne, misali: Farin ciki ya ziyarci zuciyata, maimakon a rubuta: Farin ciki ya ziyarci zuciya ta.  Yayin rubuta doguwar mallaka kuwa raba kalmomin ake yi, misali: Farin ciki ya ziyarci zuciya tasa ba Zuciyatasa ba. Da dai sauran misalai makamantan wadannan.

(14) A GUJI ABUBUWA MASU BATA KYAWUN WAKA
Akwai abubuwan da suke bata waka, wanda ko da waka ta samu jigo mai kyau, warwarar jigo mai inganci, salon waka mai gamsarwa, wakar tana daga cikin bakwai na shirin baitoci, an nuna gwanintar harshe, an ambaci jigon waka, ta bi salon mabudi da marufi, kuma ta bi daya daga cikin ma’aunan wakoki, to za ta baci in har an yi dayan cikin abin da zan yi bayani a kasa:

(1) ARON KALMOMI
Yawan aron kalmomi daga wani harshe daban kamar na Turanci, Faransanci ko kuma Larabci kan sa waka ta baci. Don haka sai mawaki ya guji yawaita aron kalmomi. Za a iya aron kalmomi daga wani harshe daban, amma abin da ake so a sani shi ne, a tabbatar harshen Hausa ya hadiyi kalmomin da za a yi aron don amfani da su wakar. Misali, a wakar Bashir Yahuza Malumfashi, mai taken BARKA DA SALLAH, ya aro kalma daga harshen Turanci, amma kuma harshen Hausa ya hadiyi kalmar da ya aro din. Ga misalin wakar a kasa:

Ya Allah ka dado salati,
            Ga Muhammadu baban Fati,
            Wanda ba ya bushasha da party,
            Nufinsa a yi Sallah da salati,
Ga Allah nai nufin addu’ata.
Kun ga ko wanda bai je makarantar boko ba, ya san ma’anar kalmar ‘party’.
A wakar Mu’azu Hadejiya mai taken MU NEMI ILMI, ya aro kalmomi daga larabci, amma kuma yaren Hausa ya hadiye su, don haka wakarsa ba ta baci ba. Misali:
            Ilmud duniya, ilmud dini,
            Su ne rabbai biyu don ilmu.
Kun ga  ya ambaci ilmud da larabci ne, amma Hausawa sun san cewa ilmi yake nufi. Hakazalika dini ma da larabci ne, yayin da Hausawa suke kiran dini da addini. Lura da hakan za mu fahimci harshen Hausa ya hadiyi kalmomin, kuma ba za su wahalar da masu saurare ko karantawa wajen gane wakar ba.
(2) MAIMATA KALMA (Repetitions).
Ba  a so mawaki ya yi ta maimata kalma a cikin wakarsa, domin hakan yana sa wa masu saurare ko karantar wakar su ji wakar ta gundire su. Ko da mawaki zai rika maimaita kalma iri daya a wakarsa, to ba a son ya zama kalmar da zai rika maimatawar ta wuce goma (10), ko da kuwa ma’anarta a kafiyar waka ce, sai dai in da niyya aka yi, wato an dauke shi a matsayin sabon salo. Shi ya sa idan mawaki yi yi hakan da niyya, sai ya sanar da masu saurare ko karantawa, don ka da a yi masa mummunar fahimta.

(3) KARYEWAR MA’AUNIN BAITI
Ba a son wakar mawaki ta zamana akwai karyewar ma’aunin baiti ko kuma karuwarsa, yiwuwar hakan zai sa waka ta baci, ma’ana ba a so idan ya fara auna wakarsa da wafir ne, sai kuma ya zo wani waje kuma yana aunawa da basid ko kuma madid. Yin hakan zai sa wakarsa ta baci wanda a karshe wakar za ta gundiri jama’a.

(4) RASHIN DAIDAITUWAR KAFIYA
Wani abu da yake bata waka shi ne, rashin daidaita kafiya a waka, misali a ce babbar kafiya tana karewa da ya ne, sai a zo wani waje kuma tana karewa da ba ko da, hakan na bata waka. Hakazalika rashin amfani da karamar kafiya a baitukan tsakiyar waka ko da kuwa baitin karshe na wakar na karewa da babbar kafiya iri daya ne. Nan ina magana a kan waka ‘yar uku zuwa sama ne. Misali:

            Ke ce jigon ganina,
            Silar farin cikina,
            Ke ce kuma rayuwata,
            Daure ki rike ni masoyi.

Shamsiyya ta yi min nisa,
Domin ta tafi gari mai nisa,
Jama’a yaya zan yi da raina?
            Fatana ki rike ni masoyi.
Kun ga a nan babbar kafiya tana karewa da yi ne, amma idan an koma ga karamar kafiya kuma, sai a rasa gane inda ta dosa. Ga shi dai wakar ta bayyana cewa , wani saurayi ne yake nuna kewar da yake yi wa budurwarsa mai suna Shamsiyya, kuma mai saurare ko karantawa yasan jigon wakar soyayya ce, amma rashin daidaituwar karamar kafiya, sai wakar ta baci, aka kuma rasa hankalinta. Don haka ake son mawaki ya kasance mai daidaita kafiyarsa (babba ko karama) a cikin wakarsa.

(5) NACIYAR AMFANI DA KALMA A WAKA.
Ba a so mawaki ya yi amfani da kalma a wajen da bai dace ba, domin neman kafiyar da ta dace ko kuma don gudun karyewar ma’aunin waka. Duk  da cewar an dan bai wa mawaki damar karya wata kalma ko bata ka’idar Nahawun Hausa (Grammar), ko kuma jirkita tsarin kalmomi (Alphabatization) ko baudar da ginin jimla (Synthax), don ya samu mikakken baiti ko kuma kafiyar da za ta dace da wakarsa. Sai dai abin da ake so mawaki ya sani shi ne, damar da aka bashin tana da iyaka. Idan kuwa mawaki ya sake damar da aka bashin ta rude shi, har ya wuce makadi da rawa, to zai kasance a karshe wakarsa ta baci.
        Wadannan su ne matakan da ake bi wajen gina ko shirya ko kuma rubuta karbabbiyar waka. Fatana Allah Ya sa wannan mukalar ta zama wata hanya ta kawo gyara a wajen mawakanmu. Allah Ya yi mana jagora, Amin.



                                                BASHIR MUSA LIMAN.

                                                070-36925654; diddigi@yahoo.com