Tuesday, November 13, 2012

Goyon ciki: Hanyoyin da ya kamata mata su bi
Sau da dama mata sukan shiga tsomomuwa a lokacin da suka samu juna biyu, inda za ka samu wahalar yau daban, ta gobe ma daban, saboda da hakan ne zan yi wannan mukalar don na fito da hanyoyin da ya kamata mata su bi a lokacin da suke goyon ciki.  Allah Ya sa bayanin ya zamo mai amfani, amin.
Babbar matsalar da mata masu juna biyu suke fuskanta ita ce, gudanar da aikace-aikacen gida da sauran ayyuka, walau na ofis ko kasuwanci da sauran sana’o’i. Wani lokaci kuma masu juna biyu suna da saurin gajiya.
A lokacin da mace take da juna biyu, abin da yake sanya ta cikin tsomomuwa shi ne, yawaita yin amai, wanda yake faruwa a dalilin tashin zuciya ko hawa da saukar wadansu sinadaran jiki.

Yadda mai juna biyu za ta magance yin amai
Kamshin abinci da duk wani abu mai sanya kyankyami yakan sanya a yi amai.
Hanyar da mai juna biyu za ta magance yin amai ita ce, kaurace wa duk wani abincin da yake tayar da zuciya. Cin kayan marmari da kuma biskit, misali biskit din ‘Crackers’ na hana tashin zuciyar da kan sanya a yi amai. Shan shayi da aka yi da citta ko da lemon tsami na magance yin amai. Ya kamata mai juna biyu ta rika yawaita shan ruwa mai tsafta, hakan na kwantar da zuciya har a magance yin amai.

Yadda mai juna biyu za ta magance yawan gajiya
Wani abu kuma da yake ci wa mai juna biyu tuwo-a-kwarya shi ne, yawan jin gajiya, walau ta yi aiki, ko kuma ba ta yi ba. Yadda mai juna biyu za ta magance yawan gajiya sun hada da:

Yawaita cin abinci mai dauke da sinadarin ‘Iron’ da kuma mai nau’in sinadarin ‘Protein’ na magance. Yawaitar gajiya ga mai juna biyu na nuna alamar karancin sinadarin ‘Iron’, amma idan mai juna biyu tana cin abincin da ke dauke da sinadarin ‘Iron’ zai taimaka mata kwarai da gaske. Ya kamata mai juna biyu ta rika cin jan nama da kaji da ganyayyaki da suka hada da alayyahu da zogale da salak da kabeji da sauransu. Haka ya kamata mai juna biyu ta rika cin wake.
Wata hanya da mai juna biyu ta rika samun karfi da kuzari ita ce, ya kamata mai juna biyu ta rika hutawa. Ma’ana idan ta yi aiki sai ta shiga daki, sannan ta kashe fitila, ta rufe idanunta, ta kuma mike kafafunta har zuwa wadansu mintuna, hakan zai sanya ta samu karfi da kuma kuzari a jikinta.
Ana so mai juna biyu ta guji aikata ayyukan da suke bukatar karfi mai yawa. Idan so samu ne mai juna biyu ta samu wanda zai rika taya ta aiki.
Ana so mai juna biyu ta rika motsa jiki, hakan zai kara mata lafiya da kuma kuzari.
Ya kamata mai juna biyu ta rika kwanciya da wuri, kuma an fi so ta kwanta a rigingine, yin hakan zai sanya jini ya rika zaga jikin jaririn da mai juna biyu take dauke da shi. Idan mai juna biyu tana son samun natsuwa da jin dadi a lokacin da take kwance, to ta sanya karamin matashi a tsakanin kafafunta da kuma karkashin cikinta.

Yadda mai juna biyu za ta rika zama da tashi:
Sanin kowa ne daga lokacin da ciki ya fara girma zama da tashi da kuma tafiya har da kwanciya kan zama wane kayan Gabas da ke bai wa mai juna biyu wahala, hakan yakan sanya rashin natsuwa da kwanciyar hankali ga mai juna biyu.

Zaman mai juna biyu
A lokacin da mai juna biyu za ta zauna, ya kamata ta zauna a kan duwawunta biyu, ma’ana ba a so ta rika bada karfi ko kuma zama a kan duwawu daya. Sannan ya kamata ta zauna a wajen zama da zai ba ta damar jingina ko kishingida, a lokaci guda bai kamata mai juna biyu ta zauna a wajen da yake da tauri ba, ma’ana wajen zaman da ba shi da laushi ko kadan. Idan kuma kujerar da mai juna biyu take zaune ba ta da laushi, to za ta iya sanya karamin matashin kai, sannan ta jingina a kai.

Tsayuwar mai juna biyu
Ba a so mai juna biyu ta dauki lokaci a tsaye. Yin hakan na sanya taruwar jini a kafafunta, wanda zai iya haifar da radadi a kafafun mai juna biyu, ko kuma ya sanya jiri ko hajijiya. Sannan dadewa a tsaye yana sanya wani nauyi a bayan mai juna biyu, ko ya haifar da ciwon baya. Idan har ya zama dole mai juna biyu ta dade a tsaye, to ya kamata ta rika dora daya daga cikin kafafunta a kan karamar kujera, ko wani abu mai dan tsawo. Haka ya kamata mai juna biyu ta rika canza kafafunta a kan karamar kujerar, sannan kuma ya kamata ta rika hutawa lokaci zuwa lokaci. Kuma a duk lokacin da mai juna biyu za ta tsaya, to ta rika sanya takalma masu kyau, wadanda ba sa haifar da tara jini a kafafu. Ko ta sanya wadansu takalma da ke yin tausa a kafafu wato ‘massaging shoe’, ko kuma ta rika daura ko sanya wani tufafi da ake kira ‘supporting hose’.
Sannan idan mai juna biyu za ta daga wani abu, to abin ya zama kusa da jikinta, ma’ana kada ta bayar da tazara sosai tsakaninta da abin da za ta daga, domin yin hakan zai iya sanya nauyi ya rinjaye ta, wanda idan haka ta faru, zai iya haifar da wata matsala. Ya kamata kuma mai juna biyu ta guji jujjuya jikinta a lokacin da za ta daga kayan.

Wadansu abubuwa da mai juna biyu za ta kauracewa:
Ya kamata mai juna biyu ta guji aikata duk wani abu da zai rika sanya mata gajiya. Ana so mai juna biyu ta rika aikata aikin da ba zai bukaci karfi da yawa ba.
Ya kamata mai juna biyu ta rika hira da mutane domin cire mata gajiyar kwakwalwa, wanda gajiyar kwakwalwa na haifar da gajiyar jiki, yakan kuma sanya mai juna biyu ta rika jin kamar ba ta da lafiya (queasy ko nausea). Ya kamata mai juna biyu ta rika hutawa, sannan ta rika motsa jiki a hankali.
A lokacin da ciki ya fara girma kamar daga wata biyar ko shida. Ya kamata mai juna biyu ta guji:

-      Kusantar sinadarai masu cutarwa.
-      Daukar lokaci wajen aiki.
-      Dadewa a tsaye.
-      Daga abu mai nauyi.
-      Zama a wajen da ake yawaita hayaniya ko surutu mai karfi.
-      Zama a wurin da akwai injina masu kara.
-      Zama a muhallin da ke da sanyi da yawa. Ya kamata mai juna biyu ta guji shan ruwa mai sanyi, ko yawaita zama a karkashin na’urar AC na tsawon lokaci.

Hanyoyi 6 da mai juna biyu za ta magance ciwon baya:
Da yawa masu juna biyu kan yi fama da ciwon baya, domin na tava satar zancen wadansu mata suna hira, inda daya daga cikinsu take cewa, ba yin ciki ba ne matsalar, ciwon baya ne yake takura mata, inda dayar ta ce, daga ta samu juna biyu za ta fara jin fargabar yadda za ta kaya da ciwon baya mai tsanani.
Ciwon baya ga mai juna biyu yana faruwa ne, sakamakon, tafiyarta da zamanta da yadda take gudanar ayyukanta sukan canza, wato ba kamar a lokacin da ba ta da juna biyu ba, wadannan canje-canje wajen tafiya da zama da tashin mai juna biyu ne ke haifar da ciwon baya.
A dalilin haka ne zan yi wa mai juna biyu bayanan wadansu hanyoyin shida zuwa bakwai da za su rage zafi da radadin ciwon baya.

Hanya ta farko
Daga lokacin da jariri ya fara girma, wurin zaman jaririn mai juna biyu (Center of gravity) na canzawa.  Hanyar da mai juna biyu za ta guje wa hakan ita ce, ta rika yin goho ko doro kadan yayin da take tsaye ko tafiya. Yin hakan zai saukaka wa jijiyoyin baya damawe ko takurewa, wanda hakan na daya daga cikin matsalolin da ke haifar da ciwon baya ga mai juna biyu. Domin guje wa ciwon baya ga mai juna biyu, idan za ta tsaya sai ta tsaya a kan kafafunta, sannan ta daga kirjinta sama, ta kuma mayar da kafadunta baya, sannan kada ta hade gwiwowinta wuri daya. Idan kuma tsayuwa ta kama mai juna biyu zuwa tsawon lokaci, to ta samu karamar kujera ta dora kafarta daya kai, sannan lokaci zuwa lokaci ta rika caccanza kafafunta. Haka ana so idan mai juna biyu za ta tsaya, to ta jingina da wani abu, hakan ma zai magance ciwon baya.
Zama kan abin zama mai kyau zai magance ciwon baya. A lokacin da mai juna biyu za ta zauna ya kamata ta kwantar da bangaren bayanta na sama,  a lokaci guda ta mike wuyanta, sannan ta bude kafafunta.

Hanya ta biyu
Hanya ta biyu ta magance ciwon baya ita ce, mai juna biyu ta guji sanya takalmi mai tsawo, wanda ake kira ‘high-heel’. Sannan sanya wani dan kamfe da ake kira ‘maternity pants’ yana magance ciwon baya. Haka idan mai juna biyu tana sanya tufafin kwankwaso ‘Waistband’ zai magance mata ciwon baya.

Hanya ta uku
Yayin daga wani abu mai nauyi ko marar nauyi, ko kuma yayin tashi daga zaune ko kwanciya, kada mai juna biyu ta yi amfani da kwankwansonta, domin magance ciwon baya sai ta yi amfani da gwiwowinta. Ya kamata mai juna biyu ta guji daga abu mai nauyi.

Hanya ta hudu
Idan mai juna biyu za ta kwanta ya kamata ta kwanta a rigingine, ba wai ta kwanta a kan bayanta ba. Sannan mai juna biyu ta tankwasa kafarta ko kafafunta. Yana da kyau mai juna biyu ta sanya karamin matashin kai a tsakanin kafafunta. Idan kuma mai juna biyu za ta kwanta a bayanta, to ta sanya karamin matashin kai a daidai karkashin cikinta. Ko kuma ta kwanta a kan dogon matashin kai.

Hanya ta biyar
Yana da kyau a rika yi wa mai juna biyu tausa a dukkan gavvanta, musamman jijiyoyin bayanta da kwankwasonta da kuma cinyoyinta.

Hanya ta shida
Idan mai juna biyu tana yin kananan aikace-aikace zai magance mata ciwon baya. Yana da kyau mai juna biyu ta rika tafiya mai ‘yar tazara ko kuma iyo a ruwa, idan ta mallaki kududdufin iyo na zamani a gidanta.
Yana da kyau mai juna biyu ta mikar da bayanta, sannan ta dora nauyinta a kan tafin hannuwanta da gwiwowinta, sannan ta tafiyar da kanta zuwa kallon kasa, a lokaci guda ta motsar da cikinta na dakiku, sannan ta sake cikin. Za ki yi hakan kamar sau goma kowace rana. Yin hakan na magance ciwon baya.
Idan bayan mai juna ta bi wadannan hanyoyi 6 da na lissafo sama, sannan kuma ciwon bayan na damunta, sai ta tuntuvi likita.
Mai juna biyu za ta iya shan magani don magance ciwon baya, misali, ta rika shan maganin ‘acetaminophen’ (Tylenol) lokaci zuwa lokaci, sai dai wadansu masana kiwon lafiya sun ce hakan bai cika maganin matsalar ciwon baya ba.
Ya kamata mai juna biyu ta fahimci idan ta rika yawan jin ciwon baya, musamman ma idan juna biyun ya girma sosai, to alama ce ta zuwan nakuda. Amma idan ciwon bayan yana hade da zubar ruwa daga gaban mai juna biyu ko jini, to hakan na bukatar a gaggauta ganin likita.

Ko yin jima’i na haifar da matsala ga mai juna biyu?
Idan har yin jima’i ba ya haifar wa mai juna biyu matsala, to za ta iya jima’in. Sai dai duk da haka akwai bukatar mai juna biyu ta rika hutun jima’i.
Daga farkon girman ciki, akwai gajiya da caccanzawar sinadaran sha’awa da rashin lafiya da sauransu, inda suke kawar da sha’awar yin jima’i ga mai juna biyu, har ila yau idan juna biyu ya girma sosai, ciwon baya da kara girman jiki ko nauyi yakan dakusar da sha’awar jima’i ga mai juna biyu, to abin ya kamata shi ne, mijin mai juna biyu ya yi mata uzuri.

Ko yin jima’i na haifar da zubewar ciki?
Da yawa daga cikin masu juna biyu sukan kaurace wa yin jima’i a lokacin da suka samu juna biyu, ko kuma juna biyun ya fara girma, don suna tsammanin yin jima’in na haifar da zubewar juna biyu. Ina so su gane juna biyu na zubewa ne, sakamakon matsalar sinadaran da ake kira ‘chromosome’ da dai sauran matsaloli.

Ko yin jima’i na haifar da matsala ga jaririn da ke ciki?
Yin jima’i ba ya haifar da matsala ga jaririn da ke ciki, domin akwai wani ruwa da ake ‘amniotic fluid’ a kokon da ke rike da jariri har zuwa mahaifa, wannan ruwa na kare jariri daga dukkan wani abu da zai kawo masa matsala.

Ko yaya za a yi jima’i lokacin da juna biyu ya fara girma?
A lokacin da juna biyu yake girma, bai kamata mijin mai juna ya zama a samanta a lokacin yin jima’i ba. Haka bai kamata mai juna biyu ta kwanta a bayanta ba. Idan har yin jima’in ya zama dole, to mai juna za ta karkace don kare nauyi a kan juna biyunta.

Ko yin jima’i na haifar da haihuwa kafin lokaci?
Sau da dama masu juna biyu suna tunanin yin jima’i na haifar da haihuwa tun kafin lokacin haihuwa ya yi, ma’ana tun kafin wata takwas ko tara. To, ina so masu juna biyu su fahimta yin jima’i ba ya kawo hakan.

Ko wane lokaci ya kamata a kaurace wa yin jima’i?
Babu wane takaimaiman lokaci da mai juna za ta kaure wa yin jima’i, sai idan har ta tava fuskantar matsalar haihuwa tun kafin lokacin haihuwa ya yi, kuma haihuwar ta zo da matsala. Mai juna biyu za ta kaurace wa jima’i idan har jini yana fitowa daga gabanta. Haka ya kamata mai juna biyu ta kaurace wa yin jima’i idan akwai matsalar yoyon ruwan da ke ba da kariya ga jariri (amniotic fluid). Ko kuma idan kwaroron cervid yana yawan budewa a-kai-a-kai.

Bayan haihuwa ko zuwa wane lokaci ya kamata a fara jima’i?
Ko mai juna biyu ta haihu da kanta ko kuma a asibiti, ko kuma ta hanyar fidar C-section, mahaifa da gaban matar da ta haihu yana daukar lokaci kafin su warke. Sai dai yawancin masana kiwon lafiya sun yi ittifakin matar da haihu ya kamata ta kaurace wa yin jima’i har na tsawon mako shida ko bakwai. Wannan yana sanya mahaifa ta rufe sosai, haka duk wani ciwon da aka ji yayin haihuwa ya warke sosai.

Ko ya kamata mai juna biyu ta rika shan magungunan da ke dauke da sinadarin Vitamin?
A zahirin gaskiya cin ganyayyaki da ‘ya’yan itatuwa da sauran abincin masu gina jiki da kuma ba da kuzari sun fi bayar da sinadaran Vitamins, maimakon shan magunguna da suke ba da sinadaran Vitamins, wadanda a Turance ake kira prenatal Vitamins. Sai dai wasu masana kiwon lafiyar sun ce, ko kana da kyau to ka kara da wanka, ma’anar hakan shi ne, ko da mace tana cin abincin da ya kamata, to ya kamata a rika shan magungunan prenatal Vitamins, musamman ma idan mace tana da matsalar daukar ciki ko tsoron zubewar ciki.

Me ya sa sinadaran Vitamins na prenatal suke da muhimmanci?
Sinadaran Vitamins na prenatal suna dauke da sinadarin ‘Folic Acid’ da kuma ‘Iron’. Sinadarin ‘Folic Acid’ yana kara karfin kwaroron kashin baya. Matsalar sinadarin ‘Folic acid’ yana haifar da matsala a kwakwalwa da kuma kashin baya.
Sinadarin ‘Iron’ yana hana kamuwa da cutar karancin jini (anemia). Kuma kowa ya san mai juna biyu idan ta zo haihuwa akwai fargabar zubar jini daga gare ta.
Haka ya kamata mai juna biyu ta rika shan magungunan masu dauke da sinadaran ‘Calcium’, da kuma ‘Vitamin D’.  Ya kamata ta rika shan wadannan magungunan ne a lokacin da take aji na uku na girman ciki, wato a lokacin da kasusuwan jarirai suke haduwa sosai. Wadannan sinadaran suna taimakawa wajen ba da kwarin kashin jariri. Haka ya kamata mai juna biyu a wannan lokacin ta rika shan madara da duk wani abinci da yake kunshe da sinadaran ‘Calcium’ da ‘Vitamin D’.
Idan mai juna biyu za ta sha magungunan da suke dauke da sinadaran da ke taimaka wa juna biyunta to ta sha:
Mai Sinadarin ‘Folic Acid’ da ke da nauyin miligiram 400-800, ko na sinadarin ‘Calcium’ mai nauyin miligiram 250, ko mai sinadarin ‘Iron’ mai nauyin miligiram 30, ko mai sinadarin ‘Vitamin C’ mai nauyin miligiram 50. Ko ta sha mai sinadarin ‘Vitamin B-6’ mai nauyin Miligiram 2, ko ‘Vitamin D’ mai nauyin 400.
Sai dai ina son na ja hankalin mai juna biyu ta sani cewa, za ta ji dadin amfani da wadannan magungunan ne idan tana cin ganyayyaki da ‘ya’yan itatuwa da kuma abinci mai ba da kuzari da gina jiki.

Ko yaushe ya kamata a rika shan magungunan firinatal (prenatal)?
An fi son mace ta rika shan magungunan tun kafin ta samu juna biyu. Haka ana so mace ta rika shan magunguna a lokacin da juna biyu yake da wata daya, wanda  a lokacin ne ake halittar kwakwalwar jariri da kuma wani kwaroro, inda daga karshe yake zama kwaroron kashin bayan jariri.
Wani lokaci mata sukan fuskanci matsalar hadiyar magunguna, idan wannan matsalar ta afku sai a gwada wadanda ake taunawa. Ko kuma a tuntuvi likita domin karin bayani.

Ko har zuwa wane lokaci ya kamata a rika shan magungunan?
Ya kamata a rika shan magunguna tun kafin daukar ciki har zuwa lokacin haihuwa. Amma kafin a rika sha ana tuntuvar likita, don kauce wa faruwar wata matsala. Haka za a rika shan wadannan magunguna lokacin da ake shayarwa.

Ko akwai matsalolin da magungunan ke haifarwa?
Wadansu matan sukan yi rashin lafiya idan sun sha magungunan, wadansu kuma sukan ji kamar ba su da lafiya. Idan ana jin kamar za a yi rashin lafiya, to kafin ko bayan an sha magungunan a rika cin ‘ya’yan itatuwa.
Sai dai wani lokacin magungunan da suke dauke da sinadaran ‘Iron’, kan haifar da kumburin ciki. Don magance kumburin ciki sai a rika shan jus mai tsami-tsami ko a rika shan ruwa da yawa. Sannan ya kamata a rika cin ganyayyaki.
A karshe ina fata wannana mukalar za ta zamo wata fitila da za ta haska matsalar da ta dabaibaye masu juna biyu har suke afka wa wadansu matsalolin da ke yin lahani ga lafiyarsu ko ta jariri, inda wani lokaci akan yi asarar jariri ko mai juna biyu ko kuma duka. Allah Ya taimake mu, amin.

Wednesday, November 7, 2012


KA’IDOJIN RUBUTUN KALMOMI DA YA KAMATA A SANI, KAFIN RUBUTU CIKIN HARSHEN HAUSA.
 
Tun lokaci mai tsawo da ya shude, na lura da kura-kurai wajen rubutu cikin harshen  Hausa. Na lura da hakan ne, sakamakon karance-karancen mukalolin da aka rubuta cikin harshen Hausa, littattafan Hausa, littattafan hikayoyin da aka rubuta cikin harshen Hausa, wasikun da aka rubuto mini, rubuce-rubucen da ake yi a jikin motocin hawa, irin su manya motoci, misali, rokoki, Daf-Daf da dangoginsu. Bas-bas har zuwa mashina da kekuna da muke hawa. Na sake lura da kura-kuran ma a rubuce-rubucen da ake yi a gaban shaguna don talla, da kuma rubuce-rubucen da ake yi a jikin allunan kan hanya.
            Kura-kuran sun hada da: Rubuta kalmomin Hausa barkatai, hada kalmomin Hausa ba a wajen da ake hadawa ba, ko raba kalmomi ba a wajen da ake rabawa ba (Word margins and divisions), ko kuma kalmomin su kunshi bakake iri daban-daban, wanda a ka’ida ba haka ya kamata su zo a rubutu ba, da kuma cusa kalmomi ba a muhallin su ba, wani lokaci kuma rashin amfani da ka’idojin rubutu (Orthography) a wajen da suka dace, ko kuma rashin amfani da su ma kwata-kwata da matsaloli da suka yi cacukwi da rubutu cikin harshen Hausa.
            Kodayake wannan ya faru ne, sakamakon ba asalin Hausawa ne, suka fitar da Manhaja ko Jadawalin rubutun Hausa ba. Idan aka koma ga tarihi za a ga irin su Farfesa Neil Skinner, Daraktan Hukumar NORLA da George Percy Bargery, Mawallafin Kamusun Hausa da Hanns Vischer, wanda ake kira Dan Hausa da Dokta R. M. East, Shugaban Hukumar Talifi da Mista. L. C. Giles, Editan farko Bature na jaridar Gaskiya Ta Fi Kwabo da sauransu, su ne suka fitar da yadda za a yi rubutun Hausa. Kasancewar su ba Hausawa ba, bugu da kari ba su san furucin Hausa da kuma kalmomin sosai ba, sai rubutun Hausa ya taso cikin hajijiya da kuma rudani, wanda ya janyo har zuwa yanzu ake ta tafka kura-kurai, rubutun kuma ya ke ta tafiya da dingishi, face wadanda suka tashi tsaye, don fahimtar yaya ka’idojin rubutun Hausa suke kafin su yi rubutun Hausar.
            Sakamakon matsalolin da suka cunkushe rubutun Hausa, sai aka yi manyan taruka guda uku, domin daidaita ka’idoji da kuma kalmomin Hausa. Taron farko an yi shi ne, a Birnin Bamako da ke kasar Mali, daga 28, ga watan Fabrairu, zuwa 5, ga watan Maris a shekara ta 1966. Taro na biyu an yi shi ne, a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, a ranar 21, ga watan Yuni a shekarar 1970, sai kuma na ukun da aka yi a Cibiyar Nazarin Harsunan Najeriya, a cikin Jami’ar Bayero da ke Kano, a watan Satumbar shekarar 1972. A cikin wadannan tarurrukan an yi gyare-gyare wa ka’idojin rubutun Hausa na cikin littafin ‘Hausa Spellings’, littafin da turawa suka dora Hausawa kansa a hanyar rubutu, wanda kuma shi ke dauke da Manhaja da Jadawalin rubutun Hausa.
            Sai dai duk da gyare-gyaren da aka yi wa ka’idojin rubutun da kuma kalmomin Hausa, sai ya zamanto tsugune ba ta kare ba, wato ba rabu da Bukar ba, an haifi Habu, inda al’amarin ya koma ana kukan targade sai ga karaya, domin an dada rikita mutane ne, wanda ya sa a rubutu guda sai ka ga ana amfani da tsohuwar ka’ida da kuma sabuwar ka’ida. Haka abubuwa suka yi ta tafiya a kudundune, ba tare da kuma an samu mafita ba, wannan matsalar ta ci gaba da ci wa masana ilmin harshen Hausa tuwo a kwarya. Da tura ta kai bango ne, ganin ruwa yana neman karewa dan kada bai gama wanka ba, ma’ana ganin rubutu cikin harshen Hausa na neman ya ci tura, sai masana ilmin harshe na kasar Jamhuriyar  Nijar suka gayyaci takwarorinsu na Najeriya, inda a nan suka shirya wani gagarumin taro a birnin Yamai, a Cibiyar Harshe da Tarihi ta Sarrafa Adabin Baka a Turance (Centre for Linguistic and Historical Studies by Oral Traditions ), a karkashin jagorancin Majalisar Hadin Kan Afirka (OAU), wanda yanzu ta
dawo Tarayyar Afrika (AU), an yi taron ne tun daga ranar 7 zuwa 12 ga watan Janairu, a shekarar 1980.
Daga farko sun daidaita kawunansu a Bakake da Wasulla da Auren Wasulla da kuma Tagwan Bakake, kana daga bisani suka daidaita ka’idojin rubuta kalmomi.
            Ga abubuwan da suka zayyana kamar haka:
 
BAKAKE
Bakaken da aka yarda da su, su ne:
 
KANANA: b, b’(mai lankwasa), c, d, d’ (mai lankwasa), f, g, h, j, k, k’(mai lankwasa), l, m, n, r, s, t, w, y, ’y, z 
MANYA:   B, B’ (mai lankwasa), C, D, ‘D (mai lankwasa), F, G, H, J, K, K’ (mai lankwasa), L, M, N, R, S, T, W, Y, ’Y, Z
 
WASULLA
 
KANANA: a, e, i, o, u
MANYA:  A, E, I, O, U
 
AUREN WASULLA
 
KANANA: ai        au         maimakon      ay      aw
MANYA:   AI      AU       maimakon       AY    AW
 
TAGWAN BAKAKE
 
KANANA:  fy, gw, gy, kw, ky, kw(mai lankwasa), ky (mai lankwasa), sh, ts
MANYA:    FY, GW, GY, KW, KY, KW (mai lankwasa), KY (mai lankwasa), SH, TS
 
KA’IDOJIN RUBUTA KALMOMI
Da suka dawo ka’idojin rubuta kalmomi kuma, sun fito da dokoki goma sha uku (13).  Ga ka’idojin rubuta kalmomin da aka fitar a taron da aka yi a kasar Nijar kamar haka:-
 
 (1). MANYA  BAKAKE
 
Wannan ya kasu kashi biyu ne:
(1a). Duk jimloli suna farawa da manya baki.
Misali: Gobe zan je kasuwa.
            Jiya na ci tuwo.
(1b). A rubuta manya bakake a farkon zanannun sunayen mutane da kuma wurare.
Sunayen mutane:  Adamu, Shamsiyya, Haruna, Mahmud.
Sunayen wurare: Jami’ar Maiduguri, Asibitin Murtala, Bauchi, Kano.
 
(2). Ba a yarda a yi amfani da bakin P a rubutun Hausa ba , sai dai F. Amma  za a iya amfani da P a cikin zanannun sunaye kamar haka:
 Palasdinu       ba        Falasdinu      ba.
 Paris               ba       Faris              ba.
 Sipikin           ba        Sifikin           ba.
 Mustapha      ba        Mustafa      ba.
Amma za a iya rubuta harafin P idan ta zo cikin Kalmar amsa-kama, kana sun amince a rubata Fensiri  da Panko, maimakon Pensiri da Panko
 
(3). Ana amfani da wadannan ka’idojin wajen rubuta bakaken M ko na N.
(3i). A yi amfani da M a tsakiyar kalma, idan bakin B, B (mai lankwasa), F, ko da harafin M ne yake gaban M din, a rubuta M, misali:
 
(a). Tambaya        ba             Tanbaya             ba.
      Jimbiri           ba                 Jinbiri               ba.
      Gammo           ba              Ganmo               ba.
      
(b). Amma a rubuta N a sauran muhallai, misali:
     Gansheka         ba           Gamsheka            ba.
     Gungume        ba           Gumgume            ba.
     Ganzaki           ba           Gamzaki              ba.
     Tuntube          ba          Tumtube               ba.
     Kanwa            ba          Kamwa                 ba.
(c). Ana rubuta N a karshen kalmomi, ko da kalmomin da ke gaba sun fara ne da bakaken                 B, B (mai lankwasa), F, ko M, misali:
   Gidan Bala                 ba                    Gidam Bala                   ba.
   Ramin  bera                ba                    Ramim bera                   ba.
   An fasa                       ba                    Am fasa             ba.
   Sabon maho               ba                    Sabom  maho                ba.
(d). Idan kalma tana karewa da M ne a karshen ta sai a rubuta M din: 
       Malam Ali  ba        Malan Ali                      ba.
       Kullum                   ba        kullun               ba.
      Mutum daya            ba        Mutun daya       ba.
(e). Kalmomin amsa-kama masu karewa da M, sai a rubuta M din:
     Jimgim         ba        Jingin                ba.
     Sukutum      ba        Sukutun ba.
     Kundum      ba        Kundun             ba.
(4). Bakaken nasaba da  na mallaka.
     (1).Bakaken nasaba, watau da N da R, ba sa sajewa da bakaken da ke gabansu:
       (a)   Sarkin makafi  ba        Sarkim makafi               ba.
              Akwatin fata                ba       akwatim fata                 ba.
              Sarkin fada                  ba       Sarkim fada                   ba.
              Sarkin baka                 ba       Sarkin baka                   ba.
       (b)  Ranar dariya                 ba        Ranad dariya                 ba.
             Ranar kuka                   ba        Ranak kuka                   ba.
             Ranar tashi                    ba        Ranat tashi                     ba.
   (2). Bakaken mallaka, watau N da R ba sa sajewa da bakaken da ke gaba da su.
        (a). Gonakinmu                  ba        Gonakimmu                   ba.
              Rigunanmu                   ba        Rigunammu                    ba.
              Matanmu                     ba        Matammu                      ba.
      
       (b). Gonarmu                      ba        Gonammu                      ba.
             Rigarmu                        ba        Rigammu                       ba.
            Motarmu                       ba        Motammu                     ba.
(5). Bakin R mai zuwa karshen fi’ilan haddasau ba ya sajewa da bakin da ke biye da shi, misali:
  (a). Mayar da shi.                    ba        Mayad da shi                ba.
        Sayar masa da shi.             ba        Sayam masa da shi        ba
        Mayar wa Ali shi.  ba        Mayaw wa Ali shi          ba.
 
(b). Motar da ka shiga.            ba        Motad da ka shiga         ba
        Sakar da ta yanke             ba        Sakad da ta yanke         ba.
        Hular da ya karba              ba        Hulad da ya karba         ba.

(6). Ana rubuta karan-dori wajen rubuta tagwan kalma:
       Fadi-tashi               ba        Fadi tashi                       ba.
       Kwan-gaba            ba        Kwan gaba                    ba.
       Bar-ni-da-mugu     ba        Bar ni da mugu  ba.
(7). Ana rubuta kalmomin jam’u a hade kamar haka:
       Komai                    ba                    Ko mai              ba.
      Kowa                      ba                    Ko wa               ba.
      Ko’ina                     ba                    Ko ina               ba.
      Koyaushe                ba                    Ko yaushe         ba.
      Kowanne                ba                    ko wane           ba.
      Kowane                  ba                    Ko  wane          ba.
      Kowadanne ba                    Ko wadanne      ba.
(8). Ana rubuta wadannan zagagen fi’ilan a hade:
    (a). Yakan     rubuta               ba       Ya kan              rubuta               ba.
          Takan          “                   ba        Ta kan                   “                   ba.
          Nakan         “                   ba        Na kan                   “                  ba.
          Mukan        “                   ba        Mu kan                  “                  ba
          Kukan          “                  ba        Ku kan                   “                  ba.
          Sukan          “                  ba        Ku kan                   “                  ba.
          Kikan           “                  ba        Ki kan                    “                  ba.
          Kakan          “                  ba        Ka kan                  “                   ba.
          Akan            “                  ba        A kan                    “                   ba.
   
(b). Yana       rubutawa          ba        Ya na                rubutawa          ba
          Tana              “                 ba        Ta na                       “                 ba.
          Ina                “                 ba        I na                        “                 ba.
         Muna             “                 ba        Mu na                     “                 ba.
         Kuna              “                 ba        Ku na                      “                 ba.
         Suna              “                 ba        Su na                      “                 ba.
         Kina               “                 ba        Ki na                       “                 ba.
         Kana              “                 ba        Ka na                      “                 ba.
         Ana                “                 ba        A na                        “                 ba 
 


(c).  Yake        rubutawa          ba        Ya ke                rubutawa          ba
         Take               “                 ba        Ta ke                        “                ba.
          Nake             “                 ba        Na ke                       “                ba.
          Muke            “                 ba        Mu ke                      “                ba.
          Kuke             “                 ba        Ku ke                       “                ba.
          Suke             “                 ba        Su ke                       “                ba.
          Kike              “                 ba        Ki ke                        “                ba.
         Kake             “                  ba        Ka ke                       “                ba
         Ake               ”                  ba        A ke                        “                ba.
  
(d). Ana so kuma a rubuta kamar haka:-
      Ta       rubuta.
        Mun        “  
        Kun         “    
        Kin          “    
        Ka          “    
        Sun         “    
        Ya           “    
        An           “
                                    da sauransu
(9).  Zagagen fi’ili masu nuna lokaci mai zuwa ana rubuta su ne:
       Zai           tafi.
      Zan          tafi .
       Za mu      tafi        ba        Zamu    tafi        ba.
       Za ku        tafi        ba        Zaku     tafi        ba.
       Za su         tafi        ba        Zasu      tafi        ba.
       Za ki         tafi        ba        Zaki      tafi        ba.
       Za ka        tafi        ba        Zaka     tafi        ba.
       Za a          tafi        ba        Za’a      tafi        ba.

(10). Ana rubuta kalmomi masu ma’ana a wawware cikin jimla:
        Ya sa ni in ba ka kudi.
         Abin da ya sa ya fi shi cancanta shi ne…..
        Na tsai da kai don mu yi kallon tare.
(11)(a) Ana rubuta abin malllaka hade da gajeriyar kalmar mallaka:
           Dokina               ba        Doki     na         ba.
           Rigarsa               ba        Rigar     sa         ba.
          Zanenta               ba        Zanen    ta         ba.
     (b) Amma rubuta abin mallaka daban, kuma doguwar kalmar mallaka daban:
      Wani  doki  nawa                ba        Wani dokinawa ba.
      Wata riga tawa                    ba        Wata rigatawa               ba.
       Wani zane nata                   ba        Wani zanenata               ba.
(12) Ba a hade wakilin-suna mafa’uli da kowace kalma:
       Ya ba ni                ba        Ya bani                         ba.
       Mun sa shi ba        Mun sashi                      ba.
       Ana kiran ka          ba        Ana       kiranka             ba.
(13) sannan ana rubuta 
        Saboda                ba        Sabo     da                    ba.
        Watakila               ba        Wata kila                       ba.
Bayan sun fitar da wadannan ka’idojin rubutun kalmomi ne, suka sake fito da wasu ka’idoji da ya kamata abi wajen rubuta wadannan:
 
Shi ne                ba        shine                ba.
Ita ce                ba        Itace                 ba.
Mu ne               ba        Mune                ba.
Kai ne               ba        Kaine                ba.
Ke ce                ba        Kece                 ba.
Su ne                ba        Sune                 ba.
Ku ne                ba        Kune                 ba.
Ni ne                 ba        Nine                  ba.
 
(2) haka a rubuta:

Ya yi            ba        Yayi                  ba.
Ya ci             ba       Yaci                  ba.
Ya tafi           ba           Ya tafi               ba.
 Ya je             ba       Yaje                  ba.
 Ya fi              ba       Yafi                   ba.
  Ya ki             ba       Yaki                  ba.
   Ta ki              ba       Taki                   ba.
   Ta yi             ba       Tayi                   ba.
 
Idan muka dawo ga ka’idojin rubutu (orthography), nan ma kura-kurai suna nan bila adadin. Lura da hakan ne ya sanya na yi dan takaitaccen fashin baki kan yadda ake amfani da ka’idojin rubutu, wajen rubutu cikin harshen Hausa.
 
(1). AYA (Full Stop) (.)
            Ana amfani da aya a rubutu wajen da ake bukatar cikakkiyar tsayawa, ko saukar da  numfashi gaba daya. Idan har an yi aya a rubutu, to wata jimla ko zance ko magana mai zaman kanta za a shiga, ko kuma rubutu ya kare. Bayan Aya in har za a ci gaba da rubutu, to da babban baki ake fara rubutu, misali:
     (1). Idris ya ci abinci ya koshi. Da yammaci kuma sai ya tafi rafi debo ruwa.
    (2). Shamsiyya ta tafi kasuwa.
A jimla ta biyu an nuna jimla ta riga ta kare, wanda hakan ne ya sanya aka yi Aya a rubutun. Ana amfani da Aya wajen takaita batu, misali, Mal. A. Shehu maimakon Malam Adamu Shehu.
 
(2). WAKAFI (COMMA) (,).
            Ana amfani da wakafi a rubutu wajen da ake bukatar ‘yar karamar dakatawa ko saukar da numfashi kadan. Bayan an yi wakafi a rubutu karamin baki ne yake biyo baya, kasancewar an dan hutasar da mai karatu ne, don ya samu ya daidaita numfashinsa; don kuma karutan ya yi masa ma’ana da kuma dadi. Misali:
(a)    Musa ya tafi kasuwa dazu-dazu, don ya sayo yadin sallarsa. Ka ga an bayyana Musa ya tafi kasuwa, sannan sai aka yi wakafi, don a hutasar da mai karatu, daga bisani kuma aka karasa rubutun  da cewa ‘don ya sayo yadin sallarsa.’
 
(3). ALAMAR TAMBAYA (QUESTION MARK) (?).
            Wannan tana daga cikin ka’idojin rubutu, masu matukar amfani a rubutu, domin tana bambance ma’anar jimla, zance ko magana, inda take nuni da tambaya aka  yi, ba wai zance haka ba (statement). Ma’ana, ana kore wa mai saurare ko mai karatu jahilci. Kana duk inda aka yi alamar tambaya, to ana ja yayin karantawa. Haka shi ma mai karantawa ana so ya ja yayin karantawar.
            (1) Maryam ta je asibiti jiya.    Zance (Statement).
            (2) Maryam ta je asibiti jiya ?  Tambaya (Interrogation).
Jimla ta farko ta nuna Maryam ta riga ta je asibiti jiya. Amma sakamakon alamar tambaya da aka yi a jimla ta biyu, sai  ma’anar ta canza, inda ake tambayar ko Maryam ta je asibiti jiya.
            Babban baki ne yake zuwa bayan an yi alamar tambaya a rubutu. Misali:
(a). Yaushe rabon duniyar siyasar kasar nan da ayyeyare ? Ina jin tun lokacin jamhuriya ta farko, hana rantsuwa zuwa farkon jamhuriya ta biyu.
 
(4). ALAMAR MOTSIN  RAI (EXCLAMATION MARK) (!).
            Ana amfani da alamar motsin rai, wajen sanar da mai karatu wani abu na takaici, tsoro, kaduwa, mamaki da sauransu. Misali:
            (a). Wayyo Allahna !
            (b). Ah ! Ya kashe ni.
            (c). Oh ! Abin da mamaki, dan akuya da wanke-wanke.
            (d). Ya cire min ido !
            Bayan an yi alamar motsin rai a rubutu, babban baki ne, yake biyo baya in har za a ci gaba da rubutu. Misali:
            Ah ! Na shiga uku, na lalace.
            Das ! Gabansa ya buga.
            Zambur ! Ta mike kamar wacce aka tsikara da tsinin mashi.
            Sun yi masa caa ! Kasuwar kuda.
(5). BAKA BIYU (BRACKET OR PARENTHESIS) ( ).
            Ana amfani da baka biyu a rubutu wajen karin bayani ga mai karatu, wato kara fito da ma’anar me ake nufi a zance, jimla ko maganar da aka yi.
            (a). Da sanyi safiya Abubakar ya bar jiharsa (Bauci).  Ka ga an ji Abubakar ya bar jiharsa, to amma wani zai so ya ji ina ne jihar Abubakar, amma da aka sa a cikin baka biyu, sai ya gamsar da mai karatu.
            (b). Sai a watan Satumbar  shekara ta 1927, aka samu wani mutum (dan kasar Sudan) da ya fitar da mutane daga duhun jahilci..
            Ana amfani da baka biyu, wajen sakaye wani batu da bai danganci rubutun da ake yi ba. Misali, ana rubutu cikin harshen Hausa, sai wata kalma ta shigo, ba ta Hausa ba, ko kuma an fadi ma’anarta da Hausa, amma kuma an fi saninta da Turanci, ko kuma dai ana so a santa cikin harshen Turanci, to sai a sanya ta cikin baka biyu. Misali,
            Amina ta dafa miyar tumatir (stew) da safe. Ka ga wani idan ya ji an ce, an yi miyar tumatir, abin zai ba shi mamaki, amma kasancewar an sa Kalmar stew, cikin baka biyu, kuma da ma an fi sanin miyar tumatir din da sunan  stew, sai ya zamanto an fi fahimtar jimlar.
            Ana amfani da baka biyu wajen sakaye takaitattun harrufa. Misali,  Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), Babban Bankin Najeriya (CBN).
            Yayin da ake amfani da baka biyu, wakafi, alamar tambaya ko aya duka suna iya biyo baya, ya danganci yaya jimlar, zancen ko maganar ta ginu. Misali:
            (1). Amina ta dafa miyar tumatir (stew), da sanyin safiya.      (wakafi)
            (2). Bafarawa ya bar biliyoyin Nairori a baitul-malin jiharsa (Sakkwato).     (aya)
            (3). Kana ganin zai iya rabuwa da ita (motarsa) ?         (alamar tambaya).
       Bakin da ke biyo baya, bayan an yi baka biyu a rubutu ya dangancin da wane daga cikin ka’idojin rubutu aka yi amfani. Idan wakafi aka yi a rubutu, karamin baki ne zai biyo baya. Idan kuma aya ko alamar tambaya ce, sai babban baki ya biyo bayan baka biyu.
 
(6) KARAN-DORI (DASH) (-).
            Ana amfani da karan-dori a rubutu, wajen rubuta tagwan kalmomi, misali, 
            (1). Ahmad yana ta safa-da-marwa a dakinsa.
            (2). Shamsiyya ta tsaya kai-da-fata, don ganin ta samu nasarar cin jarrabawarta.
            (3). Hassan yana ta fadi-tashi don ganin ya ci zabe.
            Ana amfani da karan-dori wajen hada kalma da kalma, misali, kaka-tsara-kaka, tana-kasa-tana-dabo, sa-toka-sa-katsi. Idan bayan an yi amfani da karan-dori a karshen rubutu , aya ce take ke zuwa, idan kuma ba a karshen rubutu ya zo ba , wakafi ne ke zuwa. Misali:
           (1). Siyasar kasar nan, tana-kasa-tana-dabo.
           (2). Tana-kasa-tana-dabo, damben Shago da Namadi.
            Wani lokaci ko da an yi amfani da karan-dori, babban baki na iya biyo baya, misali, wajen rubuta suna mai dauke da  Al:  Al-Mustapha, Al-Amin da sauransu. Haka zalika, ana amfani da karan-dori wajen nuna zancen wani musamman ma wajen aikin jarida, misali: Kungiyarmu ta dukufa wajen kare hakkin dan Adam - Alhaji Umaru Ahmed. Wannan karan-dorin da ya zo shi ya nuna cewa zancen wani ne. Har ila yau, ana amfani da karan-dori wajen danganta wasu batutuwa, misali: shekara 50-60, ko daga 1990-1999, awa 20-30, tarihin dandalin a daidaita sahu 2004-2009, da sauransu.
 
(7). RUWA BIYU (COLON) (:).
            Ana amfani da ruwa biyu idan za a lissafa ko zayyano wasu batutuwa yayin rubutu, kuma akasari idan an yi aya mai ruwa a rabutu, an fi yin sakin layin, misali: 
            Bashir Yahuza Malumfashi ya yi rubuce-rubuce da yawa, wanda suka kunshi littattafan hikayoyi da wakoki. A cikin littattafansa akwai:
(1)   Kudin Jini.
(2)   Zinatu Matar Gwamna.
(3)   Sinadarin Rayuwa
(4)   Bikin Kishi.
Ba wai ya zama dole duk lokacin da aka samu ruwa biyu a rubutu, ya zama sai an yi sakin layi ba, misali, Kadan daga cikin wakokin Aminuddeen Ladan Abubakar (ALA) su ne: ‘Bara A Kufa’ da ‘Sakarkari’ da Bubukuwa. Abin da nake so a fahimta shi ne, duk lokacin da aka yi ruwa biyu a rubutu, to harafin da zai  biyo baya bai zama lalle sai babban baki ba, misali, 
Ga yadda ake hada maganin: da farko a samu nono marar tsami, sai a zuba garin magani, sannan a kada, sai kuma a sha. 
Amma  wasu masana ka’idojin rubutu sun ce, dole bayan an yi ruwa biyu a rubutu, sai babban baki ya biyo baya.
 
(8). WAKAFI MAI RUWA (SEMI-COLON) (;).
           Ana amfani da wakafi mai ruwa wajen daidaita jimloli, zantuka ko maganganun da suka zo bi-da-bi, misali:
            (1). Lokacin da aka shelanta ganin watan azumin Ramadana, wasu sun yarda; wasu shakulatin-bangaro suka yi da batun; wasu kuma sun tsaya a rigar-tsakani.
            (2). Hotuna ne guda uku, na farko Bello ne; na biyu Kabiru; na uku kuma  Fahad ne. Wani abu da ake so mutane su sani, shi ne, a wannan rukunin yayin da aka yi wakafi mai ruwa a rubutu, karamin baki ne yake biyo baya, ba kamar idan an yi aya ruwa biyu ba.
  
(9) ZARCE (DOTS OR ELLIPSIS) (...).
            Ana amfani da zarce a rubutu wajen sanar da mai karatu cewa akwai sauran wani abu da ba a karasa ba, wani lokaci ana yin zarce a rubutu don abin da ake so a sanar da mai karatu ya shige shi sosai, kasancewar shi zai karasa zancen da kansa. Zarce yana farawa daga ayoyi (digo) uku zuwa sama. Misali:
(1)   Rayuwar ‘yan Afirka a Turai, ba girin-girin ba………
(2)   Idan kunne ya ji, gangar jiki………..
Sai dai idan har rubutu bai kare ba, bayan an yi  amfani da zarce a rubutu, to babban baki ne zai biyo baya, misali:
(1). Rayuwar ‘yan Afirka a Turai ba girin-girin ba…… Amma idan ka je za ka gane irin kudar da ake dandanawa.
 
(10)ALAMOMIN ZANCEN WANI (QUOTATION MARK) (“  ” ko ‘ ’)
Ana amfani da alamomin zance don kebe ko nuna zance ko magana ta wani ne. Masana ka’idojin rubutu, sun amince a yi amfani da (“ ”) ko (‘ ’) yayin kebence ko nuna zancen wani. Ana kiran wannan alama ta farko  (“ ko ‘ ) da sunan BUDE ZANCE,  ta biyu kuma (” ko ’)  ana kiran ta da sunan RUFE ZANCE. Misali: 
            Mamuda ya ce “Bello ya sayi na’urar kwamfyuta jiya.”  ko
            Mamuda ya ce ‘Bello ya sayi na’urar kwamfyuta jiya.’
Sai dai  takaddama ta kaure tsakanin masana ka’idojin rubutu, wasu su sun ce, lallai ne a saka Aya a karshen magana, zance ko jimla, misali: 
            Hassan ya ce “Ibrahim ba shi da lafiya”.
   Dalilinsu na fadin hakan shi ne, idan dai an yi aya a rubutu  to komai ya kare, idan kuwa haka ne alamar zance za ta kasance kafin aya. Wasunsu sun ce, a’a, idan har ba a sa Aya a rubutu yaushe za a gane zance, jimla ko magana ta zo karshe, bare har a sa alamar zancen wani.
  Ittifakin da aka yi shi ne, duk ka’idar da ka dauka ka yi amfani da ita an amince. Ana nufin idan ka dauki amfani da Aya bayan alamar zancen wani shi ke nan, imma kuma ka zabi ka yi amfani da sai ka sa Aya kafin alamar zancen wani duka daya ne.
 
(12). KARAN TSAYE KO SANDA JIRGE (OBLIQUE OR SLASH) (/).
      Amfanin karan tsaye ko sanda jirge a rubutu shi ne, don a nuna kalmomi biyu ko fiye da haka, wadanda suke da ma’ana daya, kuma duk wacce aka yi amfani da ita  ta wadatar. Misali:
           Ba da/bayar da 
           Domin/don 
           Sa da/sadar da.
            Kana za a iya amfani da karan tsaye ko sanda jirge a jimla, zance ko magana irin misalan da za su biyo baya:
(1)   Ka/ki amsa tambayoyi biyar kawai a wannan sashin.
(2)   Ware jinsin ka/ki daga nan: Namiji/Mace.
(3)   Wannan sashi an yi shi ne, don Yaro/Yarinya.
 
(13) DAFI (‘).
            Ana amfani da wannan alama a rubutu wajen banbamce wa mai karatu bakake da kuma wasulla da kuma yadda za a karanta a rubutu. Misali: 
            Ko’ina     maimakon      koina
            Ka’idoji   maimakon      kaidoji
            Ummul’abai’sin maimakon Ummulabaisin.
            Ka ga yin amfani da wannan alama ce ya sa aka iya gane yadda za a furta wadannan kalmomi yayin karatu. 
            Allah Ya sa wannan mukalar da zam mai amfanarwa, amin.


                                            BASHIR MUSA LIMAN.
                                    O7036925654
                                                I-MEL: diddigi@yahoo.com