Wednesday, April 17, 2013


Rayuwar Duniya A Yau

 

Godiya ga Jallah Sarki Daya,
Ya halicci talaka da mai dukiya,
Da shugabanni har da mabiya,
Don su yi masa bauta a duniya.

Salati dubu ga Annabin gaskiya,
Wanda ya zo da addinin shiriya,
Ga hakuri, hangen nesa da juriya,
Wanda ya yi kira a guje wa karya.

Idan na kalli wannan duniya,
Cike da kayan kawa da kwalliya,
Lu'u-lu'u murjani har da zinariya,
Sai hawaye ya kwarara a idaniya.

Tana dauke da jaba da macijiya,
Mutum, kaska, zomo da hasbiya,
Ruwa, kasa, iska da samaniya,
Ana mata ruwa har da walkiya.

Ku kalli cikin rayuwar duniya,
Cike da kazanta da wankiya,
Ga yaudara da makarkashiya,
Ana ta tafiya an take gaskiya.

Yau ido rufe ake neman duniya,
Ga lahira kuwa an juya baya,
Wasu sun ce da kunyar duniya,
Gara ta lahira, jama'a kun jiya?

Cin amana da rashin gaskiya,
Zalunci, zamba babu tankiya,
Karya alkawari da kuma karya,
Ana ci gaba da aikatasu bai daya.
 
Ga yara kara zube babu tarbiyya,
Idan ka aike su, gunani ko su kiya,
Amma kuma suna so su sha miya,
Su rika tauna nama suna dariya.

Wasu wajen neman tara dukiya,
Sun sadaukar da jiki ko jaririya,
Saboda tsabar bin son zuciya,
Su da shaidan na hira waje daya.

Malamai ana ta neman mabiya,
Sun himmatu ga larabcin karya,
Ko yin fassarar karya ga mabiya,
Su tuna a kabari za su yi kwanciya.

Tubali na toka ba ya gina gaskiya,
Ruwa da wuta babu a waje daya,
Za a ji zafi fa idan an taka kaya,
Ga yara har su yi kuka da idaniya.

Mata na neman mallake zuciya,
Ta mijinsu, sun sake gaskiya,
Sun kuma kama boka shi daya,
A ganinsu bukatarsu tuni ta biya.

Yawan kudinka, yawan sharholiya,
Wai a kashe ahu a nan duniya,
A sha taba, wiwi, koken da giya,
Ga kuma karuwanci don dukiya.

Tabbas masa ta fi kashin saniya,
Ko da girgiza kurna ta fi magarya,
Duba ka ga wannan kukan kurciya,
Amma mai hankali zai ga gaskiya.

Jama'a sun raba goron kiyayya,
Ga juna babu ko ga macijiya,
Sai yawan sara da cin dunduniya,
Da haka an ya za a gama lafiya?

An jefar da jarirai a kan hanya,
Ko tsoron Allah babu cikin zuciya,
An zubar da cikin jariri da jaririya,
An manta da ranar da ake sakayya.

Da mota ake wa shugabanni jiniya,
Talauci ya yi wa jama'arsu mamaya,
Yawon bude ido a Jamus da Bulgeriya,
Amurka, Suwazilan da kuma Saudiyya.

Arkomai mudu sun tauyaya,
Suna algus a cikin cinikayya,
Burinsu a ce sun tara dukiya,
Ranar Sakayya sun yi mantayya.

Maigida yana ta fifita amarya,
Ya bar uwargida a karshen baya,
Ga amarya atamfa dandasheshiya,
Ga uwargida fa atamfa alawayya.

'Yan mata sun ce sai mai dukiya,
Samari kuwa sai tarin karya,
Sai a yi aure, babu zaman lafiya,
A karshe auren sai dai a karya.

Mata ba so a yi musu kishiya,
Idan an yi musu sai kiyayya,
Sun ce da ita babbar makiyiya,
Ba ruwansu da taimakekeniya.

Kyal-kyal banza ce fa duniya
A tsakiyar ka take da ido daya,
Ba ta da goshi ko kuma keya
Amma fa gwana ce kan tsiya.

Gubarta tabbas ta fi ta macijiya,
Zakinta ya fi na 'ya'yan itaciya,
Na da launika kamar hawainiya,
Ta kasance babbar shaidaniya.

Ana ta rayuwa irin ta jahiliyya,
Mata tsirara babu wata kariya,
Suna yawon abinsu bisa hanya,
Ki yi haka kin zama wayayyiya.

Mu dawo da hankali wuri daya,
Mu san fa ita rayuwar duniya,
Tana da farko da karsheniya,
Mu dage mu mutu cikin shiriya.

An halicce mu bauta wa sarki daya,
Don haka mu guji rudin shaidaniya,
Wanda dacinta ya fi iccen madaciya,
A karshe za ta rika yi mana dariya.
 
Kowa zai tafi lahira shi daya,
Ya yi zaman kabari shi daya,
Ya amsa tambayoyi shi daya,
Idan ya tsallake sai ya yi dariya.

Azabar cikin kabari da wuya,
Mu dage mu yi aiki da gaskiya,
Bashiru ne ke fada mana gaskiya,
Don kauce wa yin da-na-saniyya.

Ubangiji dora mu a hanyar gaskiya,
Ka ba mu damar kauce wa karya,
Wacce ke sa a sha matukar wuya,
Har a rika kuka mai cike da magiya.

Mu bauta wa Allah Shi daya,
Da koyarwar Annabin gaskiya,
Lahira za ta yi zaki kamar miya,
Mu kuma rika wasa har da dariya.
 
Tammat Bashiru nan zai diga aya,
Kan wakar mamugunciya duniya,
Mai tafiya tare da son zuciya
A bi duniya a samu bacin zuciya.