Wednesday, June 12, 2013


Abubuwa 5 da ke samar da mai

Mutane da yawa na amfani da mai a babura da injina da motoci da sauransu, wanda a yanzu komai zai iya tsayawa cik idan har aka ce babu mai, hakan ne ma ya sanya a shekarar bara da Shugaba Jonathan Goodluck ya kara kudin mai al’ummar Najeriya suka rikice, komai ya balgace, inda kuma kasashen Yamma ke fafutikar mamaye kasashen da suke da arzikin mai. Shi mene ne mai? Da yaya ake samunsa kasancewar mutane da yawa suna amfanin da shi ba tare da sanin ko ta yaya aka same shi har aka hake shi ba? Me ya sa ake samun mai a wani wuri ko kasa amma kuma ba a samu wani wuri ko kasa?
A wannan mukalar zan yi gamsasshen bayanin da zai amsa wadannan tambayoyin da na zayyano a sama ga masu karatu har su fahimci yadda abubuwa biyar ke haduwa su samar da mai. Idan aka samu hudu daga cikin biyar din to ba za a kai ga hakar mai ba.
Da farko ina so masu karatu su sani, ana samun mai daga dutse ne, kuma duwatsu a duniya sun kasu kashi uku ne, akwai dutsen igneous (igniyos) da dutsen sedimentary (sedimentari) da kuma dutsen metamorphic (metamofik), ba za a samu mai ba sai a dutsen sedimentary. Ba wai daga an samu dutsen sedimentary za a samu mai ba, a’a sai idan muhallin ya zama sedimentary basin (sedimentari bazin), wato an samu kwayoyin duwatsu da suka zama shimfidu daga dutsen mafari (misali, shale) zuwa dutsen tafki (reservoir rock, misali sandstone) da sauran shimfidun duwatsu. 
Ba lallai ne daga muhalli ya zama sedimentary basin kuma ya samar da mai ba, a’a sai an samu abubuwa biyar a muhallin, wadannan abubuwa biyar sun hada da: (1) Dutsen mafari (Source Rock) misali, ‘shale’ (shel), sai (2) Dutsen Tafki (Reservoir Rock), misali sandstone (sandsiton), sai (3) Zafi (Geothermal heating) yadda za a furta- (Jotamal hitin) da (4) Kaura (Migration) yadda ake furtawa- (Maigireshin), sai kuma (5) Tarko (Trap).

(1) Dutsen mafari (Source rock)
Shi ne dutse na farko da yake zama matakin samuwar mai. Misalin wannan dutse shi ne shale. Idan dutsen shale na kunshe da sinadaran Hydrocarbons (sinadaran da ke kunshe da carbon) ya zama mafarin dutse. Wasu kan tambaya da yaya ake samun shale? Akan samu shale a lokacin da kwayoyin duwatsu da ake kira sediments suka hadu a wuri daya daga karshe kuma sai su dunkule su zama dutsen shale. An fi samun wannan dutsen a muhallin da ake kira Lacustrine (lakostarain) ko Deltaic (deltaik), wato muhallin da ya hada da tafki da korama da kududdufi da teku da sahara da sauransu.
Wannan dutse ya karkasu zuwa kashi uku bisa ga bambancin sinadaran hydrocarbons da suke kunshe a cikinsa. An kuma yi rabe-raben ne bisa ga sinadarin kerogen da sauransu.

1 Dutsen shale kan zama dutsen mafari (source rock) ne a lokacin da kwari ko dabbobi da ke rukunin algal suka makale a wurin da babu iska sosai (anodic), an kuma fi samun irin wadannan duwatsu a karkashin tafki.
2 Na biyu, dutsen shale kan zama mafarin dutse (source rock) idan kwayoyin bakteriya suka ruvar da halittun cikin teku da ake kira planktonic a kuma wurin da babu iska, sukan bayar da iskar gas da kuma mai idan akwai zafi, idan kuma suka shige cikin karkashin kasa.
3       Dutsen shale kan zama mafarin dutse idan kwayoyin bakteriya da na fungi (fungai) suka ruvar da dabbobin tudu kamar su kakan kadangaru (dinosaur) da tsire-tsire a cikin kasa, kuma idan ba su rika samun iska ba. Irin wadanan duwatsu kan samar da kwal da sauransu.

Kafin dutsen shale ya zama dutsen mafari sai idan yana dauke da sinadarin kerogen kashi 0.5 a cikinsa, amma kuma yakan zama dutsen mafari mafi kyau idan yana kunshe da kashi 12 zuwa sama a cikinsa. Misalin dutsen shale a Najeriya shi ne, Fika Shale.

(2) Dutsen tafki (Reservoir rock)
Shi ne dutse na gaba wanda yake zama ma’ajiyar mai bayan ya yi kaura daga dutsen mafari (source rock). Yana kunshe da kofofi da tarko masu yawa da ke hana man yin kaura bayan ya shiga cikinsa. Misalin wannan dutse shi ne, sandstone, a Najeriya akwai Gombe Sandstone.

Wannan hoton na nuna yadda mai yake kaura daga dutse mafari zuwa dutsen tafkin mai.
(3) Zafi (Geothermal Heating)
Akwai wani zafi da ke taimakawa wurin samuwar mai, shi wannan zafin ake kira geothermal heating. Zafin da ke samar da mai ya fara daga 60 zuwa 150 a ma’aunin degree centigrade (digiri sentigiret), ana auna ma’aunin degree centigrade ne bisa ga nisan dutsen a cikin kasa.

Masana binciken kasa sun ce wannan zafin na samuwa ne a karkashin kasa tun lokacin da aka samar da duniya, wanda a yanzu kuma zafin rana da ake kira solar (sola) da kuma ruvewar sinadarai a cikin kasa ke samar da shi. Zafin da aka samu wurin dutse mai aman wuta da girgizar kasa na taimaka wa zafin da ke samar da mai. Masana sun ce zafi a cikin kasa daga kafa 10 zuwa mita 3 yakan kai 12.8 a ma’aunin degree centigrade.

(4) Kaura (Migration)
Kaurar mai na taka muhimmiyar rawa wurin samuwar mai har a kai ga hakarsa. Akwai hanyoyi da yanayi da suke sanya mai ya yi kaura. Akwai kaura ta farko da kuma ta biyu. Ta farko ita ake kira primary (firamari maigireshin) migration, ta biyu kuma ita ce secondary migration (sakandare maigireshin). Kaura ta farko takan faru daga dutsen mafari zuwa wani dutsen mafari, kaurar mai ta biyu kuma takan faru daga dutsen mafari zuwa dutsen tafkin mai. Masana sun ce samuwar kwayoyin da suke ba da shimfidu (layers) ta hanyar  bisnewa na haifar da kaurar mai, samuwar bisnewar ake kira burial (buriyal).

Misalin tarko, a tsakiya mai ne a taskance
Zayyanar shimfidun duwatsu da ke samar da mai. A kasa dutsen mafari ne, sai ruwa da mai a cikin dutsen tafki, a saman dutsen tafki kuma tarko ne (dutsen Rock seal) 
Ga yadda kaurar mai ke faruwa daga mashimfidar dutsen mafari (source rock) zuwa dutsen mafari ko zuwan dutsen tafki (Reservoir rock):
Idan zafi ya rika karuwa zai sanya sinadaran hydrocarbons su rika motsawa. Kamar yadda ruwa yake motsawa idan aka dora shi a wuta sakamakon zafi. Inda kuma masana suka ce hakan na faruwa a sakamakon bisnewa da ake yi kwayoyin da suka samar da shimfidun duwatsu walau na mafari ko na tafki.
Idan zafi ya karu sai sinadaran hydrocarbons su narke, inda wasu kuma sukan zama kamar gas. Hakan sai ya sanya su mamaye dutsen. Misali, za a tuna yadda idan aka dora tukunya a wuta aka kuma sanya danwake a ciki lokacin da ya tafasa yakan cika har ya fi karfin tukunyar har sai an rika fifitawa. To kamar haka ne yake faruwa ga sinadaran hydrocarbons.
Idan za a iya tunawa mun ce dutsen mafari (source rock) na dauke da kofofi (Pores), to ta cikin wadannan kofofin ne sinadaran hydrocarbons wadanda suka narke suke yin kaura zuwa ko dutsen mafari ko kuma dutsen tafkin mai. Yawan samuwar kofofi ake kira High Porosity (hai forositi) hakan kan kawo mai mai yawa ya yi kaura cikin kankanen lokaci. 
Baker (1980) wani masani kan mai, ya ce ruwa na taimakawa wurin samar da kaurar mai, kasancewar a kowane lokaci idan aka hada ruwa da mai; mai na kasancewa a saman ruwa, kuma idan ruwa ya rika motsawa mai ma zai rika motsawa. Ya bayar da hujjar cewa kowa yana tabbacin akwai ruwa a cikin kasa wanda ake kira (underground water), wanda kuma shi ya sa ake samun ruwa idan an tona rijiya. To ruwan da yake cikin kasa ne a lokacin da yake motsawa sai ya rika motsa mai har ya sanya ya yi kaura.
Wasu masana sun ce ruwa ba ya taka rawa wurin samar da kaurar mai, suka ce a lokacin da zafi ya narkar da sinadaran hydrocarbons, akwai sinadaran da suke fara narkewa inda kuma kasancewar sinadarin kerogen ne ke samar da mai, to sai wadannan sinadaran da suka narke su rika tafiya da sinadarin kerogen, wadannan sinadarai kuwa kan yi kaura ta kofofin da ke jikin dutsen mafari. Masanan da suke yarda da hakan akwai Tissot da Welte, 1978 da Hunt, 1979 da kuma McAuliffe 1979.
Wadansu masana kuma sun ce idan zafi ya turara sinadaran hydrocarbons sai su fara karo da juna hakan ne kuma zai sanya su rika yin kaura ta kofofin da ke jikin dutsen mafari, masana da dama sun amince da wannan hanyar sai dai Dickey 1975 da Magara 1980 ba su yarda da wannan hanyar ba.
Amma dai koma wace hanya ce duka masanan sun yarda idan har babu kaura to kuwa ba za iya hakar mai ba, sun kuma yarda zafin ne yake sanya mai ya yi kaura.

(5) Tarko

Jama’a da dama kan yi mamaki shin me ya sa ba a samun man fetur a kowane wuri, ba ya ga haka kuma tun da mai kamar ruwa ne me ya sa ba ya tafiya daga wannan gari zuwa wancan? Ko kuma me ya sa ya tsaya a wurin daya kawai? Amsar dukkan wadannan tambayoyi ya ta’allaka a kan abu daya wato samuwar tarko. Tarko ne ke taimakawa wurin taskance mai a wuri daya ba tare da ya motsa zuwa wani wuri ba. Akan samun tarko ne ta hanyar girgizar kasa da tsunami, an samu tarko lokacin samuwar duwatsu da ake kira orogeny, sannan an samu tarko lokacin da aka samar da duniya kamar yadda masana suka ce. Su wadannan tarko su ake kira faults da folds da kuma dutsen cap rock (kaf rok). Sakamakon abubuwan da na lissafo a sama sai a samu mafarin dutse ko tabkin dutse ya lankwashe wato ya rika hawa da sauka har ya bayar da surar folds, ko ya karye ko kuma ya rubza. Karyewar ko rubzawar dutse ko shimfidar dutse ake kira faults, lankwashewar dutse kuma ake kira folds. Wani lokaci a kan samu tarko idan dutsen cap rock ya kasance a saman shimfidar ko dutsen tafki. Dutsen cap rock kan hana fitar mai bayan ya shiga shimfidar ko dutsen tafkin mai. Wannan dutse baki ne, suwal-wal kuma ba shi kofofi a jikinsa.

Samuwar mai
A nan zan yi bayanin yadda wadannan abubuwa biyar da na lissafa suke haduwa su samar da mai. A lokacin da dutsen mafari ke shigewa cikin kasa sakamakon samuwar sabbabin kwayoyin duwatsu (sediments) a samansu, yanayi kan canza, wanda a lokacin da suke waje akwai iska, amma a lokacin da suke kara shiga ciki babu iska, sannan yanayin yakan kara zafi, wannan zafin da kuma rashin iska sai ya sanya sinadarin Kerogen da ke cikin dutsen mafari ya fara dagwargwajewa. Wannan dagwargwajewar ake kira cracking (kirakin). 
Masu magana sukan ce idan gyada ta sha matsa sai ta yi mai, don haka a lokacin da aka kara samu wadansu duwatsu a saman dutsen mafari (source rock) sai nauyi ya sanya sinadarin Kerogin ya fara fitar da mai, musamman ma idan akwai isasshen zafi.

Wani abu da nake so mai karatu ya fahimta shi ne, akwai kofofi a jikin dutsen mafari, inda kuma sai mai ya rika ya rika naso walau zuwa wani dutsen mafari ko kuma dutsen tafki. Wannan nason da yake yi shi ake kira kaura (migration). Bayan ya yi kaura ne sai ya shiga dutsen tabki, wanda kuma da ma yana dauke da tarko, wannan tarkon ne zai taskance man. Daga nan sai a gudanar da bincike bayan an tabbatar da samuwar mai sai a hako shi.
A shekarun baya an yi ta samun jan-kafa wurin aikin hakar mai da ke yankin Tafkin Chadi, inda wadansu suka yi hasashen babu mai a yankin. Hakan ya sanya zan yi bayani kan samuwar mai ko akasin hakan a yanki Tafkin Chadi (Chad Basin) da ke Jihar Barno, zan yi bayanin ne bisa ga abubuwa biyar da na lissafo a sama. 

Dutsen mafari
Tafkin Chadi na kunshe da dutsen mafari da ake Gongila ko Fika Shale. Shimfida ko dutsen Gongila na dauke da sinadarin hydrocarbons kashi 1.5 a cikinsa, inda kuma  dutsen ko shimfidar Fika Shale ke dauke da sinadaran hydrocarbons da ya kai kashi 0.9 a cikinsa.  Masana sun ce idan har shimfida ko dutse mafari ya samu kashi 0.5 na sanadarin Hydrocarbon to zai iya zama dutsen mafari.

Dutsen Tafki
A bisa ga bayanin da masana suka yi sun bayyana dutse ko shimfidar dutsen Gombe Sandstone da Keri-Keri na da inganci ko nagartar da za su zama dutsen tafki.  Wadannan shimfidun duwatsu suna dauke da kofofi da kuma tarko da za su iya taskance mai.

Zafi
Sakamakon bincike da aka gudanar an gano dutsen mafari yana da nisan mita 300 a karkashin kasa, sannan akwai zafin da ya kama daga 60 zuwa 120 a ma’aunin digiri centigrade (Degree Centigrade), idan ba za manta ba na ce zafi daga 60 zuwa 150 ne ke iya sanya sinadaran hydrocarbons su fara narkewa. Idan kuwa haka ne tafkin Chadi ya cika sharadin zafin da zai iya narkar da wadannan sinadarai.

Kaura
Bincike ya bayyana akwai kofofi (pore spaces) a jikin dutsen mafari na Fika Shale, don haka bisa ga tabbatacin akwai isasshen zafin da zai iya narkar da sinadaran hydrocarbon, to kuwa akwai kofofin da wadannan sinadarai za su iya kaura. Baya ga haka a jikin dutsen tafkin mai Gombe Sandstone da kuma Kerri-Kerri akwai hanyoyin da man zai iya shiga.

Tarko
Alkaluman bayanai kan samuwar duniya sun bayyana an samu tarko a Tafkin Chadi cikin shekarar Jurassic da kuma Santonian. Santonian da Jurassic wadansu shekaru ne da suka taka rawa wurin samuwar nahiyoyin duniya. Wadannan shekaru suna cike da ayyukan samuwar duwatsu da zaizaiya da lankwashewa da kuma karyewar shimfidar duwatsu, wannan ayyukan ake kira tectonic activities (tektonik aktibitis). Wadannan ayyukan ne suka samar da tarko a tafkin Chadi.
Wannan ita ta kawo karshen takaddamar walau akwai mai a Tafkin Chadi ko babu. Ina ba mai karatu tabbacin akwai mai a Tafkin Chadi sai dai kawai a hako shi.

Bashir Musa Liman


07036925654