Tuesday, November 13, 2012

Goyon ciki: Hanyoyin da ya kamata mata su bi
Sau da dama mata sukan shiga tsomomuwa a lokacin da suka samu juna biyu, inda za ka samu wahalar yau daban, ta gobe ma daban, saboda da hakan ne zan yi wannan mukalar don na fito da hanyoyin da ya kamata mata su bi a lokacin da suke goyon ciki.  Allah Ya sa bayanin ya zamo mai amfani, amin.
Babbar matsalar da mata masu juna biyu suke fuskanta ita ce, gudanar da aikace-aikacen gida da sauran ayyuka, walau na ofis ko kasuwanci da sauran sana’o’i. Wani lokaci kuma masu juna biyu suna da saurin gajiya.
A lokacin da mace take da juna biyu, abin da yake sanya ta cikin tsomomuwa shi ne, yawaita yin amai, wanda yake faruwa a dalilin tashin zuciya ko hawa da saukar wadansu sinadaran jiki.

Yadda mai juna biyu za ta magance yin amai
Kamshin abinci da duk wani abu mai sanya kyankyami yakan sanya a yi amai.
Hanyar da mai juna biyu za ta magance yin amai ita ce, kaurace wa duk wani abincin da yake tayar da zuciya. Cin kayan marmari da kuma biskit, misali biskit din ‘Crackers’ na hana tashin zuciyar da kan sanya a yi amai. Shan shayi da aka yi da citta ko da lemon tsami na magance yin amai. Ya kamata mai juna biyu ta rika yawaita shan ruwa mai tsafta, hakan na kwantar da zuciya har a magance yin amai.

Yadda mai juna biyu za ta magance yawan gajiya
Wani abu kuma da yake ci wa mai juna biyu tuwo-a-kwarya shi ne, yawan jin gajiya, walau ta yi aiki, ko kuma ba ta yi ba. Yadda mai juna biyu za ta magance yawan gajiya sun hada da:

Yawaita cin abinci mai dauke da sinadarin ‘Iron’ da kuma mai nau’in sinadarin ‘Protein’ na magance. Yawaitar gajiya ga mai juna biyu na nuna alamar karancin sinadarin ‘Iron’, amma idan mai juna biyu tana cin abincin da ke dauke da sinadarin ‘Iron’ zai taimaka mata kwarai da gaske. Ya kamata mai juna biyu ta rika cin jan nama da kaji da ganyayyaki da suka hada da alayyahu da zogale da salak da kabeji da sauransu. Haka ya kamata mai juna biyu ta rika cin wake.
Wata hanya da mai juna biyu ta rika samun karfi da kuzari ita ce, ya kamata mai juna biyu ta rika hutawa. Ma’ana idan ta yi aiki sai ta shiga daki, sannan ta kashe fitila, ta rufe idanunta, ta kuma mike kafafunta har zuwa wadansu mintuna, hakan zai sanya ta samu karfi da kuma kuzari a jikinta.
Ana so mai juna biyu ta guji aikata ayyukan da suke bukatar karfi mai yawa. Idan so samu ne mai juna biyu ta samu wanda zai rika taya ta aiki.
Ana so mai juna biyu ta rika motsa jiki, hakan zai kara mata lafiya da kuma kuzari.
Ya kamata mai juna biyu ta rika kwanciya da wuri, kuma an fi so ta kwanta a rigingine, yin hakan zai sanya jini ya rika zaga jikin jaririn da mai juna biyu take dauke da shi. Idan mai juna biyu tana son samun natsuwa da jin dadi a lokacin da take kwance, to ta sanya karamin matashi a tsakanin kafafunta da kuma karkashin cikinta.

Yadda mai juna biyu za ta rika zama da tashi:
Sanin kowa ne daga lokacin da ciki ya fara girma zama da tashi da kuma tafiya har da kwanciya kan zama wane kayan Gabas da ke bai wa mai juna biyu wahala, hakan yakan sanya rashin natsuwa da kwanciyar hankali ga mai juna biyu.

Zaman mai juna biyu
A lokacin da mai juna biyu za ta zauna, ya kamata ta zauna a kan duwawunta biyu, ma’ana ba a so ta rika bada karfi ko kuma zama a kan duwawu daya. Sannan ya kamata ta zauna a wajen zama da zai ba ta damar jingina ko kishingida, a lokaci guda bai kamata mai juna biyu ta zauna a wajen da yake da tauri ba, ma’ana wajen zaman da ba shi da laushi ko kadan. Idan kuma kujerar da mai juna biyu take zaune ba ta da laushi, to za ta iya sanya karamin matashin kai, sannan ta jingina a kai.

Tsayuwar mai juna biyu
Ba a so mai juna biyu ta dauki lokaci a tsaye. Yin hakan na sanya taruwar jini a kafafunta, wanda zai iya haifar da radadi a kafafun mai juna biyu, ko kuma ya sanya jiri ko hajijiya. Sannan dadewa a tsaye yana sanya wani nauyi a bayan mai juna biyu, ko ya haifar da ciwon baya. Idan har ya zama dole mai juna biyu ta dade a tsaye, to ya kamata ta rika dora daya daga cikin kafafunta a kan karamar kujera, ko wani abu mai dan tsawo. Haka ya kamata mai juna biyu ta rika canza kafafunta a kan karamar kujerar, sannan kuma ya kamata ta rika hutawa lokaci zuwa lokaci. Kuma a duk lokacin da mai juna biyu za ta tsaya, to ta rika sanya takalma masu kyau, wadanda ba sa haifar da tara jini a kafafu. Ko ta sanya wadansu takalma da ke yin tausa a kafafu wato ‘massaging shoe’, ko kuma ta rika daura ko sanya wani tufafi da ake kira ‘supporting hose’.
Sannan idan mai juna biyu za ta daga wani abu, to abin ya zama kusa da jikinta, ma’ana kada ta bayar da tazara sosai tsakaninta da abin da za ta daga, domin yin hakan zai iya sanya nauyi ya rinjaye ta, wanda idan haka ta faru, zai iya haifar da wata matsala. Ya kamata kuma mai juna biyu ta guji jujjuya jikinta a lokacin da za ta daga kayan.

Wadansu abubuwa da mai juna biyu za ta kauracewa:
Ya kamata mai juna biyu ta guji aikata duk wani abu da zai rika sanya mata gajiya. Ana so mai juna biyu ta rika aikata aikin da ba zai bukaci karfi da yawa ba.
Ya kamata mai juna biyu ta rika hira da mutane domin cire mata gajiyar kwakwalwa, wanda gajiyar kwakwalwa na haifar da gajiyar jiki, yakan kuma sanya mai juna biyu ta rika jin kamar ba ta da lafiya (queasy ko nausea). Ya kamata mai juna biyu ta rika hutawa, sannan ta rika motsa jiki a hankali.
A lokacin da ciki ya fara girma kamar daga wata biyar ko shida. Ya kamata mai juna biyu ta guji:

-      Kusantar sinadarai masu cutarwa.
-      Daukar lokaci wajen aiki.
-      Dadewa a tsaye.
-      Daga abu mai nauyi.
-      Zama a wajen da ake yawaita hayaniya ko surutu mai karfi.
-      Zama a wurin da akwai injina masu kara.
-      Zama a muhallin da ke da sanyi da yawa. Ya kamata mai juna biyu ta guji shan ruwa mai sanyi, ko yawaita zama a karkashin na’urar AC na tsawon lokaci.

Hanyoyi 6 da mai juna biyu za ta magance ciwon baya:
Da yawa masu juna biyu kan yi fama da ciwon baya, domin na tava satar zancen wadansu mata suna hira, inda daya daga cikinsu take cewa, ba yin ciki ba ne matsalar, ciwon baya ne yake takura mata, inda dayar ta ce, daga ta samu juna biyu za ta fara jin fargabar yadda za ta kaya da ciwon baya mai tsanani.
Ciwon baya ga mai juna biyu yana faruwa ne, sakamakon, tafiyarta da zamanta da yadda take gudanar ayyukanta sukan canza, wato ba kamar a lokacin da ba ta da juna biyu ba, wadannan canje-canje wajen tafiya da zama da tashin mai juna biyu ne ke haifar da ciwon baya.
A dalilin haka ne zan yi wa mai juna biyu bayanan wadansu hanyoyin shida zuwa bakwai da za su rage zafi da radadin ciwon baya.

Hanya ta farko
Daga lokacin da jariri ya fara girma, wurin zaman jaririn mai juna biyu (Center of gravity) na canzawa.  Hanyar da mai juna biyu za ta guje wa hakan ita ce, ta rika yin goho ko doro kadan yayin da take tsaye ko tafiya. Yin hakan zai saukaka wa jijiyoyin baya damawe ko takurewa, wanda hakan na daya daga cikin matsalolin da ke haifar da ciwon baya ga mai juna biyu. Domin guje wa ciwon baya ga mai juna biyu, idan za ta tsaya sai ta tsaya a kan kafafunta, sannan ta daga kirjinta sama, ta kuma mayar da kafadunta baya, sannan kada ta hade gwiwowinta wuri daya. Idan kuma tsayuwa ta kama mai juna biyu zuwa tsawon lokaci, to ta samu karamar kujera ta dora kafarta daya kai, sannan lokaci zuwa lokaci ta rika caccanza kafafunta. Haka ana so idan mai juna biyu za ta tsaya, to ta jingina da wani abu, hakan ma zai magance ciwon baya.
Zama kan abin zama mai kyau zai magance ciwon baya. A lokacin da mai juna biyu za ta zauna ya kamata ta kwantar da bangaren bayanta na sama,  a lokaci guda ta mike wuyanta, sannan ta bude kafafunta.

Hanya ta biyu
Hanya ta biyu ta magance ciwon baya ita ce, mai juna biyu ta guji sanya takalmi mai tsawo, wanda ake kira ‘high-heel’. Sannan sanya wani dan kamfe da ake kira ‘maternity pants’ yana magance ciwon baya. Haka idan mai juna biyu tana sanya tufafin kwankwaso ‘Waistband’ zai magance mata ciwon baya.

Hanya ta uku
Yayin daga wani abu mai nauyi ko marar nauyi, ko kuma yayin tashi daga zaune ko kwanciya, kada mai juna biyu ta yi amfani da kwankwansonta, domin magance ciwon baya sai ta yi amfani da gwiwowinta. Ya kamata mai juna biyu ta guji daga abu mai nauyi.

Hanya ta hudu
Idan mai juna biyu za ta kwanta ya kamata ta kwanta a rigingine, ba wai ta kwanta a kan bayanta ba. Sannan mai juna biyu ta tankwasa kafarta ko kafafunta. Yana da kyau mai juna biyu ta sanya karamin matashin kai a tsakanin kafafunta. Idan kuma mai juna biyu za ta kwanta a bayanta, to ta sanya karamin matashin kai a daidai karkashin cikinta. Ko kuma ta kwanta a kan dogon matashin kai.

Hanya ta biyar
Yana da kyau a rika yi wa mai juna biyu tausa a dukkan gavvanta, musamman jijiyoyin bayanta da kwankwasonta da kuma cinyoyinta.

Hanya ta shida
Idan mai juna biyu tana yin kananan aikace-aikace zai magance mata ciwon baya. Yana da kyau mai juna biyu ta rika tafiya mai ‘yar tazara ko kuma iyo a ruwa, idan ta mallaki kududdufin iyo na zamani a gidanta.
Yana da kyau mai juna biyu ta mikar da bayanta, sannan ta dora nauyinta a kan tafin hannuwanta da gwiwowinta, sannan ta tafiyar da kanta zuwa kallon kasa, a lokaci guda ta motsar da cikinta na dakiku, sannan ta sake cikin. Za ki yi hakan kamar sau goma kowace rana. Yin hakan na magance ciwon baya.
Idan bayan mai juna ta bi wadannan hanyoyi 6 da na lissafo sama, sannan kuma ciwon bayan na damunta, sai ta tuntuvi likita.
Mai juna biyu za ta iya shan magani don magance ciwon baya, misali, ta rika shan maganin ‘acetaminophen’ (Tylenol) lokaci zuwa lokaci, sai dai wadansu masana kiwon lafiya sun ce hakan bai cika maganin matsalar ciwon baya ba.
Ya kamata mai juna biyu ta fahimci idan ta rika yawan jin ciwon baya, musamman ma idan juna biyun ya girma sosai, to alama ce ta zuwan nakuda. Amma idan ciwon bayan yana hade da zubar ruwa daga gaban mai juna biyu ko jini, to hakan na bukatar a gaggauta ganin likita.

Ko yin jima’i na haifar da matsala ga mai juna biyu?
Idan har yin jima’i ba ya haifar wa mai juna biyu matsala, to za ta iya jima’in. Sai dai duk da haka akwai bukatar mai juna biyu ta rika hutun jima’i.
Daga farkon girman ciki, akwai gajiya da caccanzawar sinadaran sha’awa da rashin lafiya da sauransu, inda suke kawar da sha’awar yin jima’i ga mai juna biyu, har ila yau idan juna biyu ya girma sosai, ciwon baya da kara girman jiki ko nauyi yakan dakusar da sha’awar jima’i ga mai juna biyu, to abin ya kamata shi ne, mijin mai juna biyu ya yi mata uzuri.

Ko yin jima’i na haifar da zubewar ciki?
Da yawa daga cikin masu juna biyu sukan kaurace wa yin jima’i a lokacin da suka samu juna biyu, ko kuma juna biyun ya fara girma, don suna tsammanin yin jima’in na haifar da zubewar juna biyu. Ina so su gane juna biyu na zubewa ne, sakamakon matsalar sinadaran da ake kira ‘chromosome’ da dai sauran matsaloli.

Ko yin jima’i na haifar da matsala ga jaririn da ke ciki?
Yin jima’i ba ya haifar da matsala ga jaririn da ke ciki, domin akwai wani ruwa da ake ‘amniotic fluid’ a kokon da ke rike da jariri har zuwa mahaifa, wannan ruwa na kare jariri daga dukkan wani abu da zai kawo masa matsala.

Ko yaya za a yi jima’i lokacin da juna biyu ya fara girma?
A lokacin da juna biyu yake girma, bai kamata mijin mai juna ya zama a samanta a lokacin yin jima’i ba. Haka bai kamata mai juna biyu ta kwanta a bayanta ba. Idan har yin jima’in ya zama dole, to mai juna za ta karkace don kare nauyi a kan juna biyunta.

Ko yin jima’i na haifar da haihuwa kafin lokaci?
Sau da dama masu juna biyu suna tunanin yin jima’i na haifar da haihuwa tun kafin lokacin haihuwa ya yi, ma’ana tun kafin wata takwas ko tara. To, ina so masu juna biyu su fahimta yin jima’i ba ya kawo hakan.

Ko wane lokaci ya kamata a kaurace wa yin jima’i?
Babu wane takaimaiman lokaci da mai juna za ta kaure wa yin jima’i, sai idan har ta tava fuskantar matsalar haihuwa tun kafin lokacin haihuwa ya yi, kuma haihuwar ta zo da matsala. Mai juna biyu za ta kaurace wa jima’i idan har jini yana fitowa daga gabanta. Haka ya kamata mai juna biyu ta kaurace wa yin jima’i idan akwai matsalar yoyon ruwan da ke ba da kariya ga jariri (amniotic fluid). Ko kuma idan kwaroron cervid yana yawan budewa a-kai-a-kai.

Bayan haihuwa ko zuwa wane lokaci ya kamata a fara jima’i?
Ko mai juna biyu ta haihu da kanta ko kuma a asibiti, ko kuma ta hanyar fidar C-section, mahaifa da gaban matar da ta haihu yana daukar lokaci kafin su warke. Sai dai yawancin masana kiwon lafiya sun yi ittifakin matar da haihu ya kamata ta kaurace wa yin jima’i har na tsawon mako shida ko bakwai. Wannan yana sanya mahaifa ta rufe sosai, haka duk wani ciwon da aka ji yayin haihuwa ya warke sosai.

Ko ya kamata mai juna biyu ta rika shan magungunan da ke dauke da sinadarin Vitamin?
A zahirin gaskiya cin ganyayyaki da ‘ya’yan itatuwa da sauran abincin masu gina jiki da kuma ba da kuzari sun fi bayar da sinadaran Vitamins, maimakon shan magunguna da suke ba da sinadaran Vitamins, wadanda a Turance ake kira prenatal Vitamins. Sai dai wasu masana kiwon lafiyar sun ce, ko kana da kyau to ka kara da wanka, ma’anar hakan shi ne, ko da mace tana cin abincin da ya kamata, to ya kamata a rika shan magungunan prenatal Vitamins, musamman ma idan mace tana da matsalar daukar ciki ko tsoron zubewar ciki.

Me ya sa sinadaran Vitamins na prenatal suke da muhimmanci?
Sinadaran Vitamins na prenatal suna dauke da sinadarin ‘Folic Acid’ da kuma ‘Iron’. Sinadarin ‘Folic Acid’ yana kara karfin kwaroron kashin baya. Matsalar sinadarin ‘Folic acid’ yana haifar da matsala a kwakwalwa da kuma kashin baya.
Sinadarin ‘Iron’ yana hana kamuwa da cutar karancin jini (anemia). Kuma kowa ya san mai juna biyu idan ta zo haihuwa akwai fargabar zubar jini daga gare ta.
Haka ya kamata mai juna biyu ta rika shan magungunan masu dauke da sinadaran ‘Calcium’, da kuma ‘Vitamin D’.  Ya kamata ta rika shan wadannan magungunan ne a lokacin da take aji na uku na girman ciki, wato a lokacin da kasusuwan jarirai suke haduwa sosai. Wadannan sinadaran suna taimakawa wajen ba da kwarin kashin jariri. Haka ya kamata mai juna biyu a wannan lokacin ta rika shan madara da duk wani abinci da yake kunshe da sinadaran ‘Calcium’ da ‘Vitamin D’.
Idan mai juna biyu za ta sha magungunan da suke dauke da sinadaran da ke taimaka wa juna biyunta to ta sha:
Mai Sinadarin ‘Folic Acid’ da ke da nauyin miligiram 400-800, ko na sinadarin ‘Calcium’ mai nauyin miligiram 250, ko mai sinadarin ‘Iron’ mai nauyin miligiram 30, ko mai sinadarin ‘Vitamin C’ mai nauyin miligiram 50. Ko ta sha mai sinadarin ‘Vitamin B-6’ mai nauyin Miligiram 2, ko ‘Vitamin D’ mai nauyin 400.
Sai dai ina son na ja hankalin mai juna biyu ta sani cewa, za ta ji dadin amfani da wadannan magungunan ne idan tana cin ganyayyaki da ‘ya’yan itatuwa da kuma abinci mai ba da kuzari da gina jiki.

Ko yaushe ya kamata a rika shan magungunan firinatal (prenatal)?
An fi son mace ta rika shan magungunan tun kafin ta samu juna biyu. Haka ana so mace ta rika shan magunguna a lokacin da juna biyu yake da wata daya, wanda  a lokacin ne ake halittar kwakwalwar jariri da kuma wani kwaroro, inda daga karshe yake zama kwaroron kashin bayan jariri.
Wani lokaci mata sukan fuskanci matsalar hadiyar magunguna, idan wannan matsalar ta afku sai a gwada wadanda ake taunawa. Ko kuma a tuntuvi likita domin karin bayani.

Ko har zuwa wane lokaci ya kamata a rika shan magungunan?
Ya kamata a rika shan magunguna tun kafin daukar ciki har zuwa lokacin haihuwa. Amma kafin a rika sha ana tuntuvar likita, don kauce wa faruwar wata matsala. Haka za a rika shan wadannan magunguna lokacin da ake shayarwa.

Ko akwai matsalolin da magungunan ke haifarwa?
Wadansu matan sukan yi rashin lafiya idan sun sha magungunan, wadansu kuma sukan ji kamar ba su da lafiya. Idan ana jin kamar za a yi rashin lafiya, to kafin ko bayan an sha magungunan a rika cin ‘ya’yan itatuwa.
Sai dai wani lokacin magungunan da suke dauke da sinadaran ‘Iron’, kan haifar da kumburin ciki. Don magance kumburin ciki sai a rika shan jus mai tsami-tsami ko a rika shan ruwa da yawa. Sannan ya kamata a rika cin ganyayyaki.
A karshe ina fata wannana mukalar za ta zamo wata fitila da za ta haska matsalar da ta dabaibaye masu juna biyu har suke afka wa wadansu matsalolin da ke yin lahani ga lafiyarsu ko ta jariri, inda wani lokaci akan yi asarar jariri ko mai juna biyu ko kuma duka. Allah Ya taimake mu, amin.

No comments:

Post a Comment