Goyon ciki: Hanyoyin
da ya kamata mata su bi
Sau da dama
mata sukan shiga tsomomuwa a lokacin da suka samu juna biyu, inda za ka samu
wahalar yau daban, ta gobe ma daban, saboda da hakan ne zan yi wannan mukalar
don na fito da hanyoyin da ya kamata mata su bi a lokacin da suke goyon ciki. Allah Ya sa bayanin ya zamo mai amfani, amin.
Babbar
matsalar da mata masu juna biyu suke fuskanta ita ce, gudanar da aikace-aikacen
gida da sauran ayyuka, walau na ofis ko kasuwanci da sauran sana’o’i. Wani
lokaci kuma masu juna biyu suna da saurin gajiya.
A lokacin da
mace take da juna biyu, abin da yake sanya ta cikin tsomomuwa shi ne, yawaita yin
amai, wanda yake faruwa a dalilin tashin zuciya ko hawa da saukar wadansu
sinadaran jiki.
Yadda mai juna biyu za
ta magance yin amai
Kamshin abinci
da duk wani abu mai sanya kyankyami yakan sanya a yi amai.
Hanyar da mai
juna biyu za ta magance yin amai ita ce, kaurace wa duk wani abincin da yake
tayar da zuciya. Cin kayan marmari da kuma biskit, misali biskit din ‘Crackers’
na hana tashin zuciyar da kan sanya a yi amai. Shan shayi da aka yi da citta ko
da lemon tsami na magance yin amai. Ya kamata mai juna biyu ta rika yawaita
shan ruwa mai tsafta, hakan na kwantar da zuciya har a magance yin amai.
Yadda mai juna biyu za
ta magance yawan gajiya
Wani abu kuma
da yake ci wa mai juna biyu tuwo-a-kwarya shi ne, yawan jin gajiya, walau ta yi
aiki, ko kuma ba ta yi ba. Yadda mai juna biyu za ta magance yawan gajiya sun
hada da:
Yawaita cin
abinci mai dauke da sinadarin ‘Iron’ da kuma mai nau’in sinadarin ‘Protein’ na
magance. Yawaitar gajiya ga mai juna biyu na nuna alamar karancin sinadarin
‘Iron’, amma idan mai juna biyu tana cin abincin da ke dauke da sinadarin ‘Iron’
zai taimaka mata kwarai da gaske. Ya kamata mai juna biyu ta rika cin jan nama
da kaji da ganyayyaki da suka hada da alayyahu da zogale da salak da kabeji da
sauransu. Haka ya kamata mai juna biyu ta rika cin wake.
Wata hanya da
mai juna biyu ta rika samun karfi da kuzari ita ce, ya kamata mai juna biyu ta
rika hutawa. Ma’ana idan ta yi aiki sai ta shiga daki, sannan ta kashe fitila,
ta rufe idanunta, ta kuma mike kafafunta har zuwa wadansu mintuna, hakan zai
sanya ta samu karfi da kuma kuzari a jikinta.
Ana so mai
juna biyu ta guji aikata ayyukan da suke bukatar karfi mai yawa. Idan so samu
ne mai juna biyu ta samu wanda zai rika taya ta aiki.
Ana so mai
juna biyu ta rika motsa jiki, hakan zai kara mata lafiya da kuma kuzari.
Ya kamata mai
juna biyu ta rika kwanciya da wuri, kuma an fi so ta kwanta a rigingine, yin
hakan zai sanya jini ya rika zaga jikin jaririn da mai juna biyu take dauke da
shi. Idan mai juna biyu tana son samun natsuwa da jin dadi a lokacin da take
kwance, to ta sanya karamin matashi a tsakanin kafafunta da kuma karkashin
cikinta.
Yadda mai juna biyu za ta rika zama da tashi:
Sanin kowa ne daga
lokacin da ciki ya fara girma zama da tashi da kuma tafiya har da kwanciya kan
zama wane kayan Gabas da ke bai wa mai juna biyu wahala, hakan yakan sanya
rashin natsuwa da kwanciyar hankali ga mai juna biyu.
Zaman mai juna biyu
A lokacin da mai juna
biyu za ta zauna, ya kamata ta zauna a kan duwawunta biyu, ma’ana ba a so ta rika
bada karfi ko kuma zama a kan duwawu daya. Sannan ya kamata ta zauna a wajen
zama da zai ba ta damar jingina ko kishingida, a lokaci guda bai kamata mai
juna biyu ta zauna a wajen da yake da tauri ba, ma’ana wajen zaman da ba shi da
laushi ko kadan. Idan kuma kujerar da mai juna biyu take zaune ba ta da laushi,
to za ta iya sanya karamin matashin kai, sannan ta jingina a kai.
Tsayuwar mai juna biyu
Ba a so mai juna biyu
ta dauki lokaci a tsaye. Yin hakan na sanya taruwar jini a kafafunta, wanda zai
iya haifar da radadi a kafafun mai juna biyu, ko kuma ya sanya jiri ko
hajijiya. Sannan dadewa a tsaye yana sanya wani nauyi a bayan mai juna biyu, ko
ya haifar da ciwon baya. Idan har ya zama dole mai juna biyu ta dade a tsaye,
to ya kamata ta rika dora daya daga cikin kafafunta a kan karamar kujera, ko
wani abu mai dan tsawo. Haka ya kamata mai juna biyu ta rika canza kafafunta a
kan karamar kujerar, sannan kuma ya kamata ta rika hutawa lokaci zuwa lokaci.
Kuma a duk lokacin da mai juna biyu za ta tsaya, to ta rika sanya takalma masu
kyau, wadanda ba sa haifar da tara jini a kafafu. Ko ta sanya wadansu takalma
da ke yin tausa a kafafu wato ‘massaging shoe’, ko kuma ta rika daura ko sanya
wani tufafi da ake kira ‘supporting hose’.
Sannan idan mai juna
biyu za ta daga wani abu, to abin ya zama kusa da jikinta, ma’ana kada ta bayar
da tazara sosai tsakaninta da abin da za ta daga, domin yin hakan zai iya sanya
nauyi ya rinjaye ta, wanda idan haka ta faru, zai iya haifar da wata matsala.
Ya kamata kuma mai juna biyu ta guji jujjuya jikinta a lokacin da za ta daga
kayan.
Wadansu abubuwa da mai juna biyu za ta kauracewa:
Ya kamata mai juna
biyu ta guji aikata duk wani abu da zai rika sanya mata gajiya. Ana so mai juna
biyu ta rika aikata aikin da ba zai bukaci karfi da yawa ba.
Ya kamata mai juna biyu
ta rika hira da mutane domin cire mata gajiyar kwakwalwa, wanda gajiyar kwakwalwa
na haifar da gajiyar jiki, yakan kuma sanya mai juna biyu ta rika jin kamar ba
ta da lafiya (queasy ko nausea). Ya kamata mai juna biyu ta rika hutawa, sannan
ta rika motsa jiki a hankali.
A lokacin da ciki ya fara girma kamar daga wata biyar ko shida.
Ya kamata mai juna biyu ta guji:
-
Kusantar sinadarai masu cutarwa.
-
Daukar lokaci wajen aiki.
-
Dadewa a tsaye.
-
Daga abu mai nauyi.
-
Zama a wajen da ake yawaita hayaniya ko surutu mai karfi.
-
Zama a wurin da akwai injina masu kara.
-
Zama a muhallin da ke da sanyi da yawa. Ya kamata mai juna biyu
ta guji shan ruwa mai sanyi, ko yawaita zama a karkashin na’urar AC na tsawon
lokaci.
Hanyoyi 6 da mai juna
biyu za ta magance ciwon baya:
Da yawa masu juna biyu kan yi fama da ciwon baya, domin na tava
satar zancen wadansu mata suna hira, inda daya daga cikinsu take cewa, ba yin
ciki ba ne matsalar, ciwon baya ne yake takura mata, inda dayar ta ce, daga ta
samu juna biyu za ta fara jin fargabar yadda za ta kaya da ciwon baya mai
tsanani.
Ciwon baya ga mai juna biyu yana faruwa ne, sakamakon, tafiyarta
da zamanta da yadda take gudanar ayyukanta sukan canza, wato ba kamar a lokacin
da ba ta da juna biyu ba, wadannan canje-canje wajen tafiya da zama da tashin
mai juna biyu ne ke haifar da ciwon baya.
A dalilin haka ne zan yi wa mai juna biyu bayanan wadansu
hanyoyin shida zuwa bakwai da za su rage zafi da radadin ciwon baya.
Hanya ta farko
Daga lokacin da jariri ya fara girma, wurin zaman jaririn mai
juna biyu (Center of gravity) na canzawa.
Hanyar da mai juna biyu za ta guje wa hakan ita ce, ta rika yin goho ko
doro kadan yayin da take tsaye ko tafiya. Yin hakan zai saukaka wa jijiyoyin
baya damawe ko takurewa, wanda hakan na daya daga cikin matsalolin da ke haifar
da ciwon baya ga mai juna biyu. Domin guje wa ciwon baya ga mai juna biyu, idan
za ta tsaya sai ta tsaya a kan kafafunta, sannan ta daga kirjinta sama, ta kuma
mayar da kafadunta baya, sannan kada ta hade gwiwowinta wuri daya. Idan kuma
tsayuwa ta kama mai juna biyu zuwa tsawon lokaci, to ta samu karamar kujera ta dora
kafarta daya kai, sannan lokaci zuwa lokaci ta rika caccanza kafafunta. Haka
ana so idan mai juna biyu za ta tsaya, to ta jingina da wani abu, hakan ma zai
magance ciwon baya.
Zama kan abin zama mai kyau zai magance ciwon baya. A lokacin da
mai juna biyu za ta zauna ya kamata ta kwantar da bangaren bayanta na
sama, a lokaci guda ta mike wuyanta,
sannan ta bude kafafunta.
Hanya ta biyu
Hanya ta biyu ta magance ciwon baya ita ce, mai juna biyu ta
guji sanya takalmi mai tsawo, wanda ake kira ‘high-heel’. Sannan sanya wani dan
kamfe da ake kira ‘maternity pants’ yana magance ciwon baya. Haka idan mai juna
biyu tana sanya tufafin kwankwaso ‘Waistband’ zai magance mata ciwon baya.
Hanya ta uku
Yayin daga wani abu mai nauyi ko marar nauyi, ko kuma yayin
tashi daga zaune ko kwanciya, kada mai juna biyu ta yi amfani da kwankwansonta,
domin magance ciwon baya sai ta yi amfani da gwiwowinta. Ya kamata mai juna biyu
ta guji daga abu mai nauyi.
Hanya ta hudu
Idan mai juna biyu za ta kwanta ya
kamata ta kwanta a rigingine, ba wai ta kwanta a kan bayanta ba. Sannan mai
juna biyu ta tankwasa kafarta ko kafafunta. Yana da kyau mai juna biyu ta sanya
karamin matashin kai a tsakanin kafafunta. Idan kuma mai juna biyu za ta kwanta
a bayanta, to ta sanya karamin matashin kai a daidai karkashin cikinta. Ko kuma
ta kwanta a kan dogon matashin kai.
Hanya ta biyar
Yana da kyau a rika yi wa mai juna
biyu tausa a dukkan gavvanta, musamman jijiyoyin bayanta da kwankwasonta da
kuma cinyoyinta.
Hanya ta shida
Idan mai juna biyu tana yin kananan
aikace-aikace zai magance mata ciwon baya. Yana da kyau mai juna biyu ta rika
tafiya mai ‘yar tazara ko kuma iyo a ruwa, idan ta mallaki kududdufin iyo na
zamani a gidanta.
Yana da kyau mai juna biyu ta mikar da
bayanta, sannan ta dora nauyinta a kan tafin hannuwanta da gwiwowinta, sannan
ta tafiyar da kanta zuwa kallon kasa, a lokaci guda ta motsar da cikinta na dakiku,
sannan ta sake cikin. Za ki yi hakan kamar sau goma kowace rana. Yin hakan na
magance ciwon baya.
Idan bayan mai juna ta bi wadannan
hanyoyi 6 da na lissafo sama, sannan kuma ciwon bayan na damunta, sai ta tuntuvi
likita.
Mai juna biyu za ta iya shan magani
don magance ciwon baya, misali, ta rika shan maganin ‘acetaminophen’ (Tylenol)
lokaci zuwa lokaci, sai dai wadansu masana kiwon lafiya sun ce hakan bai cika
maganin matsalar ciwon baya ba.
Ya kamata mai juna biyu ta fahimci
idan ta rika yawan jin ciwon baya, musamman ma idan juna biyun ya girma sosai,
to alama ce ta zuwan nakuda. Amma idan ciwon bayan yana hade da zubar ruwa daga
gaban mai juna biyu ko jini, to hakan na bukatar a gaggauta ganin likita.
Ko yin jima’i na haifar da matsala ga mai juna
biyu?
Idan har yin jima’i ba ya haifar wa
mai juna biyu matsala, to za ta iya jima’in. Sai dai duk da haka akwai bukatar
mai juna biyu ta rika hutun jima’i.
Daga farkon girman ciki, akwai gajiya
da caccanzawar sinadaran sha’awa da rashin lafiya da sauransu, inda suke kawar
da sha’awar yin jima’i ga mai juna biyu, har ila yau idan juna biyu ya girma
sosai, ciwon baya da kara girman jiki ko nauyi yakan dakusar da sha’awar jima’i
ga mai juna biyu, to abin ya kamata shi ne, mijin mai juna biyu ya yi mata
uzuri.
Ko yin jima’i na haifar da zubewar ciki?
Da yawa daga cikin masu juna biyu sukan
kaurace wa yin jima’i a lokacin da suka samu juna biyu, ko kuma juna biyun ya
fara girma, don suna tsammanin yin jima’in na haifar da zubewar juna biyu. Ina so
su gane juna biyu na zubewa ne, sakamakon matsalar sinadaran da ake kira ‘chromosome’
da dai sauran matsaloli.
Ko yin jima’i na haifar da matsala ga jaririn
da ke ciki?
Yin jima’i ba ya haifar da matsala ga
jaririn da ke ciki, domin akwai wani ruwa da ake ‘amniotic fluid’ a kokon da ke
rike da jariri har zuwa mahaifa, wannan ruwa na kare jariri daga dukkan wani
abu da zai kawo masa matsala.
Ko yaya za a yi jima’i lokacin da juna biyu ya
fara girma?
A lokacin da juna biyu yake girma, bai
kamata mijin mai juna ya zama a samanta a lokacin yin jima’i ba. Haka bai
kamata mai juna biyu ta kwanta a bayanta ba. Idan har yin jima’in ya zama dole,
to mai juna za ta karkace don kare nauyi a kan juna biyunta.
Ko yin jima’i na haifar da haihuwa kafin
lokaci?
Sau da dama masu juna biyu suna
tunanin yin jima’i na haifar da haihuwa tun kafin lokacin haihuwa ya yi, ma’ana
tun kafin wata takwas ko tara. To, ina so masu juna biyu su fahimta yin jima’i
ba ya kawo hakan.
Ko wane lokaci ya kamata a kaurace wa yin
jima’i?
Babu wane takaimaiman lokaci da mai
juna za ta kaure wa yin jima’i, sai idan har ta tava fuskantar matsalar haihuwa
tun kafin lokacin haihuwa ya yi, kuma haihuwar ta zo da matsala. Mai juna biyu
za ta kaurace wa jima’i idan har jini yana fitowa daga gabanta. Haka ya kamata
mai juna biyu ta kaurace wa yin jima’i idan akwai matsalar yoyon ruwan da ke ba
da kariya ga jariri (amniotic fluid). Ko kuma idan kwaroron cervid yana yawan
budewa a-kai-a-kai.
Bayan haihuwa ko zuwa wane lokaci ya kamata a
fara jima’i?
Ko mai juna biyu ta haihu da kanta ko
kuma a asibiti, ko kuma ta hanyar fidar C-section, mahaifa da gaban matar da ta
haihu yana daukar lokaci kafin su warke. Sai dai yawancin masana kiwon lafiya
sun yi ittifakin matar da haihu ya kamata ta kaurace wa yin jima’i har na
tsawon mako shida ko bakwai. Wannan yana sanya mahaifa ta rufe sosai, haka duk
wani ciwon da aka ji yayin haihuwa ya warke sosai.
Ko ya kamata mai juna biyu ta rika shan
magungunan da ke dauke da sinadarin Vitamin?
A zahirin gaskiya cin ganyayyaki da
‘ya’yan itatuwa da sauran abincin masu gina jiki da kuma ba da kuzari sun fi
bayar da sinadaran Vitamins, maimakon shan magunguna da suke ba da sinadaran Vitamins,
wadanda a Turance ake kira prenatal Vitamins. Sai dai wasu masana kiwon lafiyar
sun ce, ko kana da kyau to ka kara da wanka, ma’anar hakan shi ne, ko da mace
tana cin abincin da ya kamata, to ya kamata a rika shan magungunan prenatal Vitamins,
musamman ma idan mace tana da matsalar daukar ciki ko tsoron zubewar ciki.
Me ya sa sinadaran Vitamins na prenatal suke
da muhimmanci?
Sinadaran Vitamins na prenatal suna dauke
da sinadarin ‘Folic Acid’ da kuma ‘Iron’. Sinadarin ‘Folic Acid’ yana kara karfin
kwaroron kashin baya. Matsalar sinadarin ‘Folic acid’ yana haifar da matsala a kwakwalwa
da kuma kashin baya.
Sinadarin ‘Iron’ yana hana kamuwa da
cutar karancin jini (anemia). Kuma kowa ya san mai juna biyu idan ta zo haihuwa
akwai fargabar zubar jini daga gare ta.
Haka ya kamata mai juna biyu ta rika
shan magungunan masu dauke da sinadaran ‘Calcium’, da kuma ‘Vitamin D’. Ya kamata ta rika shan wadannan magungunan ne
a lokacin da take aji na uku na girman ciki, wato a lokacin da kasusuwan
jarirai suke haduwa sosai. Wadannan sinadaran suna taimakawa wajen ba da kwarin
kashin jariri. Haka ya kamata mai juna biyu a wannan lokacin ta rika shan
madara da duk wani abinci da yake kunshe da sinadaran ‘Calcium’ da ‘Vitamin D’.
Idan mai juna biyu za ta sha
magungunan da suke dauke da sinadaran da ke taimaka wa juna biyunta to ta sha:
Mai Sinadarin ‘Folic Acid’ da ke da
nauyin miligiram 400-800, ko na sinadarin ‘Calcium’ mai nauyin miligiram 250,
ko mai sinadarin ‘Iron’ mai nauyin miligiram 30, ko mai sinadarin ‘Vitamin C’
mai nauyin miligiram 50. Ko ta sha mai sinadarin ‘Vitamin B-6’ mai nauyin
Miligiram 2, ko ‘Vitamin D’ mai nauyin 400.
Sai dai ina son na ja hankalin mai
juna biyu ta sani cewa, za ta ji dadin amfani da wadannan magungunan ne idan
tana cin ganyayyaki da ‘ya’yan itatuwa da kuma abinci mai ba da kuzari da gina
jiki.
Ko yaushe ya kamata a rika shan magungunan
firinatal (prenatal)?
An fi son mace ta rika shan magungunan tun kafin ta samu juna
biyu. Haka ana so mace ta rika shan magunguna a lokacin da juna biyu yake da
wata daya, wanda a lokacin ne ake
halittar kwakwalwar jariri da kuma wani kwaroro, inda daga karshe yake zama
kwaroron kashin bayan jariri.
Wani lokaci mata sukan fuskanci matsalar hadiyar magunguna, idan
wannan matsalar ta afku sai a gwada wadanda ake taunawa. Ko kuma a tuntuvi
likita domin karin bayani.
Ko har zuwa wane
lokaci ya kamata a rika shan magungunan?
Ya kamata a rika shan magunguna tun kafin daukar ciki har zuwa
lokacin haihuwa. Amma kafin a rika sha ana tuntuvar likita, don kauce wa
faruwar wata matsala. Haka za a rika shan wadannan magunguna lokacin da ake
shayarwa.
Ko akwai matsalolin da
magungunan ke haifarwa?
Wadansu matan sukan yi rashin lafiya idan sun sha magungunan, wadansu
kuma sukan ji kamar ba su da lafiya. Idan ana jin kamar za a yi rashin lafiya,
to kafin ko bayan an sha magungunan a rika cin ‘ya’yan itatuwa.
Sai dai wani lokacin magungunan da suke dauke da sinadaran ‘Iron’,
kan haifar da kumburin ciki. Don magance kumburin ciki sai a rika shan jus mai
tsami-tsami ko a rika shan ruwa da yawa. Sannan ya kamata a rika cin
ganyayyaki.
A karshe ina fata wannana mukalar za ta zamo wata fitila da za
ta haska matsalar da ta dabaibaye masu juna biyu har suke afka wa wadansu
matsalolin da ke yin lahani ga lafiyarsu ko ta jariri, inda wani lokaci akan yi
asarar jariri ko mai juna biyu ko kuma duka. Allah Ya taimake mu, amin.