BAMBANCI TSAKANIN TURAWA DA NASARAWA
Kamar yadda tarihihi suka nuna bayan
zuwan Larabawa kasar Hausa, an jaddada musulunci a kasar Hausa ta hanyoyi biyu
ne. Hanya ta farko ita ce, wacce mutanen kasar Turkiyya suka bi, wanda suka
shigo Afirka ta kasashen Magribi (Afrikiyya ta Arewa), wato kasashe kamar su
Moroko da Tunisiya da Masar da Mauritaniya da sauran kasashen Arewacin Afirka,
wanda suka gangaro zuwa kasashen Hausa. Hanya ta biyu ita ce, wacce Wangarawa
(mutanen kasar Mali) suka bi, wanda suka biyo ta kasar Chadi, zuwa kasar Borno,
daga bisani suka karaso kasashen Hausa. Masu tarihi sun amince da wadannan
hanyoyi biyu, amma da yake rubutuna don a fahimci bambamcin da yake tsakanin
Turawa da Nasarawa ne, sai na fi mayar da hankalina, ga bangaren da musulunci
ya shigo kasar Hausa ta hanyar kasashen Magribi, wanda tsatson faruwar hakan
shi ne, a sakamakon zuwan mutanen Turkiyya.
Mutanen Turkiyya wanda tarihi ya nuna
a zamanin baya sun fi Nasarawa (wadanda ake kira Turawan Mulkin Mallaka) karfi
da ilmi da wayewa, sun kuma kasance ma’abota kasuwanci da yawon bude idanu,
kuma uwa-uba masu dabbaka addinin musulunci ne, wanda a ta dalilin hakan ne
suka shigo kasashen Afirka.
Da farko da niyyar cinikayya suka
shigo, sai dai sannu-a-hankali, sakamakon sabawa da aka yi da su, ta kuma
hanyar nuna dabi’u da halaye nagari, sai suka fara yi wa mutane wa’azi, wanda
ba a jima ba suka yi galaba a kan mutanen Afirka, suka kuma karbi musulunci.
Hakan kuwa ya samu nasaba ne, sakamakon yanayinsu, halayyarsu da kuma sanin ya
kamatarsu da zamantakewarsu. Haka dai suka yi a kasashen Hausa ma lokacin da
suka shigo kasar Hausar, wanda hakan ya sanya suka yi nasara ba tare da
kaulin-bala-a-malin ba.
Ya zo tarihince cewa, suit ko coat din da Nasarawa suke sanyawa, asalinta
suturar mutanen kasar Turkiyya ce, wanda wani mutum ne da ake kira Mustafa
Kemal Ataturk yake sanyawa. Wanda da ma na fada a baya cewa mutanen kasar
Turkiyya sun fi Nasarawa wayewa da ilmi da kuma sanin duniya, don haka a
sakamakon yawon bude idanu da mutanen kasar Turkiyya suke yi, ya sanya da suka
je kasashen Nasarawa, sai Nasarawa suka kwaikwayi sanya coat ko suit, wanda yanzu matane da yawa suka
dauka cewa coat ko suit suturar Nasarawa ce. Mai karatu ka
rike wannan zai zo a gaba.
Mustafa Kemal Ataturk da 'yan tawagarsa
Mustafa Kemal Ataturk sanye da kwat
Bayan mutanen Turkiyya sun jaddada
musulunci a kasar Hausa ne, sai kuma Wangarawa suka sake jaddada shi. Sai dai
duk da wannan jan aiki da suka yi, ba su fitar da daudar maguzanci a cikin
kasar Hausa ba, wadanda suka hada da: rawar bori da camfe-camfe da zuwan wajen
boka da kuma sauran ayyukan al’ada. Wadannan ayyukan al’adar sun ci gaba da
faruwa ne, har zuwa lokacin da Mujaddadi Shehu Usman Dan Fodiyo, ya fara Jihadi
cikin shekarar 1804, inda ya fara da Gobir, wanda ya yi ta yi har ya ci
garuruwa irin su Kano da Gwandu da Daura da Zamfara da Katsina da Bauci, wanda
a lokacin jihadin Jihar Bauci ta samu tutocin Shehu guda 5, wadanda suka kunshi
Bauci da Gombe da Katagum da Misau da kuma Jama’are. Haka dai ya ci sauran
garuruwan kasashen Hausa, da yawansu ba tare da an yi yaki ba.
Yanzu zan dawo jihadin da aka yi a
Kano saboda mahimmancin da yake da shi a wannan rubutun. Cikin shekarun
1805-1806 ne, Mujaddadi Shehu ya ci kasar Kano, wanda a nan aka nada Sarki
Suleiman sarautar Kasar Kano, inda cikin shekaru biyu, wato (1807-1808) aka
gina masallaci da kuma makarantar islamiyya. Kuma tarihi ya nuna mutanen kasar
Turkiyya ne suka kafa harsashin masallaci da makarantar.
Daga nan ne, Mujaddadi Shehu ya ci
gaba da jihadi, wanda hakan ya kawo kifewar duk wata dauda ta maguzanci.
Musulunci mai inganci ya samu harsashin kafuwa. Duk da cewa an samu matsaloli
amma abubuwa sun yi ta gudana har zuwa shekarar 1903, wato karni na 19 ke nan,
lokacin da Nasarawa (Turawan Mulkin Mallaka), suka ci kasar Hausa ke nan.
Matsaloli biyu ne suka janyo Nasarawa suka ci kasar Hausa, wato matsalar cikin
gida (Internal Factors) da kuma matsalar waje (External Factors).
Matsalar cikin gida ta faru ne,
sakamakon kara dawowa da sha’anin mulkin masarautu da aka yi, wanda ake yi tun
kafin jihadi. Inda sarakuna suke gabatar da mulki bisa ga abin da ya kwanta
musu a rai, maimakon bin tafarkin shari’a. Wasunsu ma ba su da karatun addini
irin na su Halifa Muhammadu Bello, bugu da kari, an mayar da Halifanci gado,
maimakon karatun addininka da dacewarka ya baka Halifanci. Misali a Sakkwato
bayan mutuwar Aliyu Babba, sai kawunsa Abubakar Atiku ya gaje shi. Haka a Kano,
bayan mutuwar Sarki Ibrahim Dabo (1816-1846), sai ‘ya’yansa uku suka gaje shi,
daya-bayan-daya. Tarihi ya kuma nuna cewa, a dukkan masarautun da aka yi jihadi
an samu wadannan matsalolin, wanda hakan ya janyo ake mulkin kama karya
maimakon mulki bisa tafarkin shari’a.
Hakan ya kawo aka fara fadan
karon-battar-karfe, gami da fito-na-fito don neman sarauta, misali a Kano da
Gombe da Muri da Hadejiya duk hakan ya faru. Ire-iren wadannan matsalolin cikin
gidan da suka dabaibaye kasar Hausa ne, suka sanya Nasarawa yin nasara a kasar
Hausa, tun da sun yi amfani da rarrabuwar kai wajen karya sarakunan kasar
Hausa. Da ma kowa ya sani rashin hadin kai na jawo a farraka al’umma komai
yawanta.
Idan muka koma matsalolin waje (External Factors) kuma, sai mu gane cewa, Nasarawa irin su Mango Park da
William Lander da kuma Letitra Strode Landern waxanda ake kira Landern Brothers
da Clapperton da Barth da Overweg da Vogel, suka tura wa Nasarawa bayanan leken asiri. Haka
akwai rohoto daga mutanen kasar Jamus da Dokta Gerhard Rolfs ya yi a Tafiya
Mabudin Ilmin da ya yi daga Tripoli (kasar Libya) zuwa Legas ta Najeriya. Har
ila yau an samu bayanai a kan kasar Hausa daga Gustav
Nactigal, wanda Sarki William na Prussia ya turo da kyaututtuka zuwa wajen
Shehu Omar a Kukawa, wanda bayanin takardar da aka turo Nactigal tana kunshe da
wani ihsani da aka yi wa Shehu Umar din, wanda hakan ya samu ne, a dalilin tarba
da karramawar da ya yi wa ‘yan hakar ma’adanan kasar Jamus. Bugu da kari an
samu rahotannin daga ‘yan hakar ma’adanan kasar Faransa.
Landern Brothers a lokacin da suka ziyarci Sarkin Badagiri a Legas
Zanen hoton Mungo Park
Rahotannin suna dauke da al’adu da
noma da kiwo da tattalin arziki da muhalli da masarautu da nazarin kasa da
yanayi da kuma sauran hanyoyin rayuwar al’ummar Hausawa. Da wadannan rahotannin
Nasarawa suka yi amfani, wanda daga karshen-karshe suka ci kasar Hausa, wanda
tarihi ya nuna sun shigo kasar Hausa bayan zuwan mutanen kasar Turkiyya ne.
An bar mutanen kasar Ingila sun shigo
kasar Hausa ne cikin ruwan sanyi, ba tare da sa-toka-sa-katsi ko
kai-wa-ruwa-rana ba, kafin daga bisani aka fara yake-yake, dalilin da ya sa aka
bar su suka shiga kasar Hausa cikin ruwan sanyi shi ne, su ma an gan su sanye
da suit ko coat, wanda kuma da ma an ga mutanen kasar
Turkiyya suna sanya irin ta. Mutanen Turkiyya kuwa Bahaushe ya san mutanen
kirki ne, wannnan sai ya sanya Nasarawa suka sakata, suka bararraje, suka kuma
wala, ba tare da wani ya lakuci hancinsu ba! Wanda hakan ya sanya suka nemi
wuce makadi da rawa, ta hanyar fitowa da manufofinsu ta son yada addinin
Kiristanci, da kuma son kwashe dukiyar da take arewa, sai aka yi musu tawaye,
ta hanyar taka musu burki, bayan an nuna su da yatsa, a lokaci guda kuma aka
shirya yakar su, wanda hakan ya kawo aka yi ta gwajin kwanjin yake-yake
tsakanin mutanen Hausa da kuma masu jajayen kunnuwa.
Kada ka gaji, biyo ni kadan zuwa
baya, lokacin da mutanen kasar Turkiyya suka shigo kasar Hausa, sun shaida cewa
daga kasar Turkiyya suke, wanda daga nan ne, Hausawa suka fara kiransu da
Turkawa, ma’ana suka Hausantar da sunan. Wannan al’ada da dabi’a ce ta Malam
Bahaushe wato ya hausantar da duk wani abu da ya ji an ambata, don yarensa ya
zama ya hadiye shi, don kuma ya samu saukin iya furtawa da kuma gane shi.
Misali, ya hausantar da sunan Khadijah zuwa Hadiza karshe da ya ga sunan yana
ba shi wuya sai ya hausantar zuwa Dija ko Dije. Haka ya Hausantar da sunan
Usman zuwa Usmanu karshe zuwa Manu. Wannnan ga fannin sunayen mutane ke nan.
Malam Bahaushe ya hausantar da kalmar
Din zuwa Addini, Ilmu zuwa Ilimi, Al-khair zuwa Alheri da sauran batutuwa da
Bahaushe yake hausantarwa. Wannan dalili ne, ya sanya Bahaushe ya Hausantar da
sunan kasar Turkey zuwa Turkiyya, mutanen kasar Turkiyya
kuma zuwa Turkawa, karshe da ya ga hakan yana yi wa harshensa tsauri, sai ya
sake hausantarwa zuwa Turawa. Namiji Bature maimakon Baturke; ta mace, Baturiya
maimakon Baturkiya.
Wannan ta sa da Bahaushe ya ga
Nasarawa da irin kayan Turkawa, sai ya fara kiran su da Turawa, maimakon ya
tambayi sunansu. Bayan Nasarawa sun ci kasar Hausa da yaki ne (1903-1906), sai
suka bi diddigin dalilin da ya sa Hausawa suke kiran su da Turawa, a nan suka
fahimci tsatson sunan ya samo asali a ta dalilin sunan da ake kiran mutanen
kasar Turkiyya ne, daga nan sai suka nemi a daina kiran su da Turawa, a nan
kilu-ta-ja-bau! Maimakon a daina kiran su da Turawa, sai kuma abin ya zama a
garin gyaran gira aka rasa ido, domin an dawo ana kiran su da kafirai. Wannan
ce ta sanya Nasarawa suka yi ruwa, suka tsaki, suka yi uwa- da–makarbiya, wajen
janyo hankalin Hausawa da cewa, ku musulmi ne, masu bin Kur’ani, idan kuka duba
littafinku za ku ga an kira mu da Nasara ne ba kafirai ba, wannan ce ta sanya
wadanda suka hankalta suka Hausantar da sunan Nasara zuwa Nasarawa, wannan ne
ma kuma ya sanya ake kiran sunan unguwar da Nasara suka zauna a Kano da sunan
Nasarawa.
Sai dai ko a wancan lokacin an samu
wadanda ba ruwansu, in dai mutum farar fata, mai jan kunnuwa da kuma gashi yana
yalki kuma sanye da suit ko coat, to sunansa Bature, jam’insu kuma Turawa.
Wanda har zuwa yanzu da na yi rubutun nan, wasu ba ruwansu don tantance Turawa
da Nasarawa. Kuma wasu ma ba su san ko akwai bambamci tsakanin Turawa da kuma
Nasarawa ba. Ko Bature da Banasare ba.
A karshe ina fata wannan mukala za ta
zama sila da za ta sanya a fahimci bambancin da ke tsakanin Turawa da Nasarawa.
Bashir Musa Liman
Marubuci,
Manazarci da kuma sharhi a kan al’amuran yau da kullum.
07036925654