Thursday, September 13, 2012

Bambanci tsakanin Turawa da Nasarawa


                        BAMBANCI TSAKANIN TURAWA DA NASARAWA

Kamar yadda tarihihi suka nuna bayan zuwan Larabawa kasar Hausa, an jaddada musulunci a kasar Hausa ta hanyoyi biyu ne. Hanya ta farko ita ce, wacce mutanen kasar Turkiyya suka bi, wanda suka shigo Afirka ta kasashen Magribi (Afrikiyya ta Arewa), wato kasashe kamar su Moroko da Tunisiya da Masar da Mauritaniya da sauran kasashen Arewacin Afirka, wanda suka gangaro zuwa kasashen Hausa. Hanya ta biyu ita ce, wacce Wangarawa (mutanen kasar Mali) suka bi, wanda suka biyo ta kasar Chadi, zuwa kasar Borno, daga bisani suka karaso kasashen Hausa. Masu tarihi sun amince da wadannan hanyoyi biyu, amma da yake rubutuna don a fahimci bambamcin da yake tsakanin Turawa da Nasarawa ne, sai na fi mayar da hankalina, ga bangaren da musulunci ya shigo kasar Hausa ta hanyar kasashen Magribi, wanda tsatson faruwar hakan shi ne, a sakamakon zuwan mutanen Turkiyya.
Mutanen Turkiyya wanda tarihi ya nuna a zamanin baya sun fi Nasarawa (wadanda ake kira Turawan Mulkin Mallaka) karfi da ilmi da wayewa, sun kuma kasance ma’abota kasuwanci da yawon bude idanu, kuma uwa-uba masu dabbaka addinin musulunci ne, wanda a ta dalilin hakan ne suka shigo kasashen Afirka.
Da farko da niyyar cinikayya suka shigo, sai dai sannu-a-hankali, sakamakon sabawa da aka yi da su, ta kuma hanyar nuna dabi’u da halaye nagari, sai suka fara yi wa mutane wa’azi, wanda ba a jima ba suka yi galaba a kan mutanen Afirka, suka kuma karbi musulunci. Hakan kuwa ya samu nasaba ne, sakamakon yanayinsu, halayyarsu da kuma sanin ya kamatarsu da zamantakewarsu. Haka dai suka yi a kasashen Hausa ma lokacin da suka shigo kasar Hausar, wanda hakan ya sanya suka yi nasara ba tare da kaulin-bala-a-malin ba.
Ya zo tarihince cewa, suit ko coat din da Nasarawa suke sanyawa, asalinta suturar mutanen kasar Turkiyya ce, wanda wani mutum ne da ake kira Mustafa Kemal Ataturk yake sanyawa. Wanda da ma na fada a baya cewa mutanen kasar Turkiyya sun fi Nasarawa wayewa da ilmi da kuma sanin duniya, don haka a sakamakon yawon bude idanu da mutanen kasar Turkiyya suke yi, ya sanya da suka je kasashen Nasarawa, sai Nasarawa suka kwaikwayi sanya coat ko suit, wanda yanzu matane da yawa suka dauka cewa coat ko suit suturar Nasarawa ce. Mai karatu ka rike wannan zai zo a gaba.
                                                  Mustafa Kemal Ataturk da 'yan tawagarsa
 

                                       Mustafa Kemal Ataturk sanye da kwat
 
Bayan mutanen Turkiyya sun jaddada musulunci a kasar Hausa ne, sai kuma Wangarawa suka sake jaddada shi. Sai dai duk da wannan jan aiki da suka yi, ba su fitar da daudar maguzanci a cikin kasar Hausa ba, wadanda suka hada da: rawar bori da camfe-camfe da zuwan wajen boka da kuma sauran ayyukan al’ada. Wadannan ayyukan al’adar sun ci gaba da faruwa ne, har zuwa lokacin da Mujaddadi Shehu Usman Dan Fodiyo, ya fara Jihadi cikin shekarar 1804, inda ya fara da Gobir, wanda ya yi ta yi har ya ci garuruwa irin su Kano da Gwandu da Daura da Zamfara da Katsina da Bauci, wanda a lokacin jihadin Jihar Bauci ta samu tutocin Shehu guda 5, wadanda suka kunshi Bauci da Gombe da Katagum da Misau da kuma Jama’are. Haka dai ya ci sauran garuruwan kasashen Hausa, da yawansu ba tare da an yi yaki ba.
Yanzu zan dawo jihadin da aka yi a Kano saboda mahimmancin da yake da shi a wannan rubutun. Cikin shekarun 1805-1806 ne, Mujaddadi Shehu ya ci kasar Kano, wanda a nan aka nada Sarki Suleiman sarautar Kasar Kano, inda cikin shekaru biyu, wato (1807-1808) aka gina masallaci da kuma makarantar islamiyya. Kuma tarihi ya nuna mutanen kasar Turkiyya ne suka kafa harsashin masallaci da makarantar.
Daga nan ne, Mujaddadi Shehu ya ci gaba da jihadi, wanda hakan ya kawo kifewar duk wata dauda ta maguzanci. Musulunci mai inganci ya samu harsashin kafuwa. Duk da cewa an samu matsaloli amma abubuwa sun yi ta gudana har zuwa shekarar 1903, wato karni na 19 ke nan, lokacin da Nasarawa (Turawan Mulkin Mallaka), suka ci kasar Hausa ke nan. Matsaloli biyu ne suka janyo Nasarawa suka ci kasar Hausa, wato matsalar cikin gida (Internal Factors) da kuma matsalar waje (External Factors).
Matsalar cikin gida ta faru ne, sakamakon kara dawowa da sha’anin mulkin masarautu da aka yi, wanda ake yi tun kafin jihadi. Inda sarakuna suke gabatar da mulki bisa ga abin da ya kwanta musu a rai, maimakon bin tafarkin shari’a. Wasunsu ma ba su da karatun addini irin na su Halifa Muhammadu Bello, bugu da kari, an mayar da Halifanci gado, maimakon karatun addininka da dacewarka ya baka Halifanci. Misali a Sakkwato bayan mutuwar Aliyu Babba, sai kawunsa Abubakar Atiku ya gaje shi. Haka a Kano, bayan mutuwar Sarki Ibrahim Dabo (1816-1846), sai ‘ya’yansa uku suka gaje shi, daya-bayan-daya. Tarihi ya kuma nuna cewa, a dukkan masarautun da aka yi jihadi an samu wadannan matsalolin, wanda hakan ya janyo ake mulkin kama karya maimakon mulki bisa tafarkin shari’a.
Hakan ya kawo aka fara fadan karon-battar-karfe, gami da fito-na-fito don neman sarauta, misali a Kano da Gombe da Muri da Hadejiya duk hakan ya faru. Ire-iren wadannan matsalolin cikin gidan da suka dabaibaye kasar Hausa ne, suka sanya Nasarawa yin nasara a kasar Hausa, tun da sun yi amfani da rarrabuwar kai wajen karya sarakunan kasar Hausa. Da ma kowa ya sani rashin hadin kai na jawo a farraka al’umma komai yawanta.
Idan muka koma matsalolin waje (External Factors) kuma, sai mu gane cewa, Nasarawa irin su Mango Park da William Lander da kuma Letitra Strode Landern waxanda ake kira Landern Brothers da Clapperton da Barth da Overweg da Vogel, suka tura wa Nasarawa bayanan leken asiri. Haka akwai rohoto daga mutanen kasar Jamus da Dokta Gerhard Rolfs ya yi a Tafiya Mabudin Ilmin da ya yi daga Tripoli (kasar Libya) zuwa Legas ta Najeriya. Har ila yau an samu bayanai a kan kasar Hausa daga Gustav Nactigal, wanda Sarki William na Prussia ya turo da kyaututtuka zuwa wajen Shehu Omar a Kukawa, wanda bayanin takardar da aka turo Nactigal tana kunshe da wani ihsani da aka yi wa Shehu Umar din, wanda hakan ya samu ne, a dalilin tarba da karramawar da ya yi wa ‘yan hakar ma’adanan kasar Jamus. Bugu da kari an samu rahotannin daga ‘yan hakar ma’adanan kasar Faransa.
 
                    Landern Brothers a lokacin da suka ziyarci Sarkin Badagiri a Legas
 
                                              Zanen hoton Mungo Park
 
Rahotannin suna dauke da al’adu da noma da kiwo da tattalin arziki da muhalli da masarautu da nazarin kasa da yanayi da kuma sauran hanyoyin rayuwar al’ummar Hausawa. Da wadannan rahotannin Nasarawa suka yi amfani, wanda daga karshen-karshe suka ci kasar Hausa, wanda tarihi ya nuna sun shigo kasar Hausa bayan zuwan mutanen kasar Turkiyya ne.
 
An bar mutanen kasar Ingila sun shigo kasar Hausa ne cikin ruwan sanyi, ba tare da sa-toka-sa-katsi ko kai-wa-ruwa-rana ba, kafin daga bisani aka fara yake-yake, dalilin da ya sa aka bar su suka shiga kasar Hausa cikin ruwan sanyi shi ne, su ma an gan su sanye da suit ko coat, wanda kuma da ma an ga mutanen kasar Turkiyya suna sanya irin ta. Mutanen Turkiyya kuwa Bahaushe ya san mutanen kirki ne, wannnan sai ya sanya Nasarawa suka sakata, suka bararraje, suka kuma wala, ba tare da wani ya lakuci hancinsu ba! Wanda hakan ya sanya suka nemi wuce makadi da rawa, ta hanyar fitowa da manufofinsu ta son yada addinin Kiristanci, da kuma son kwashe dukiyar da take arewa, sai aka yi musu tawaye, ta hanyar taka musu burki, bayan an nuna su da yatsa, a lokaci guda kuma aka shirya yakar su, wanda hakan ya kawo aka yi ta gwajin kwanjin yake-yake tsakanin mutanen Hausa da kuma masu jajayen kunnuwa.
Kada ka gaji, biyo ni kadan zuwa baya, lokacin da mutanen kasar Turkiyya suka shigo kasar Hausa, sun shaida cewa daga kasar Turkiyya suke, wanda daga nan ne, Hausawa suka fara kiransu da Turkawa, ma’ana suka Hausantar da sunan. Wannan al’ada da dabi’a ce ta Malam Bahaushe wato ya hausantar da duk wani abu da ya ji an ambata, don yarensa ya zama ya hadiye shi, don kuma ya samu saukin iya furtawa da kuma gane shi. Misali, ya hausantar da sunan Khadijah zuwa Hadiza karshe da ya ga sunan yana ba shi wuya sai ya hausantar zuwa Dija ko Dije. Haka ya Hausantar da sunan Usman zuwa Usmanu karshe zuwa Manu. Wannnan ga fannin sunayen mutane ke nan.
Malam Bahaushe ya hausantar da kalmar Din zuwa Addini, Ilmu zuwa Ilimi, Al-khair zuwa Alheri da sauran batutuwa da Bahaushe yake hausantarwa. Wannan dalili ne, ya sanya Bahaushe ya Hausantar da sunan kasar Turkey zuwa Turkiyya, mutanen kasar Turkiyya kuma zuwa Turkawa, karshe da ya ga hakan yana yi wa harshensa tsauri, sai ya sake hausantarwa zuwa Turawa. Namiji Bature maimakon Baturke; ta mace, Baturiya maimakon Baturkiya.
Wannan ta sa da Bahaushe ya ga Nasarawa da irin kayan Turkawa, sai ya fara kiran su da Turawa, maimakon ya tambayi sunansu. Bayan Nasarawa sun ci kasar Hausa da yaki ne (1903-1906), sai suka bi diddigin dalilin da ya sa Hausawa suke kiran su da Turawa, a nan suka fahimci tsatson sunan ya samo asali a ta dalilin sunan da ake kiran mutanen kasar Turkiyya ne, daga nan sai suka nemi a daina kiran su da Turawa, a nan kilu-ta-ja-bau! Maimakon a daina kiran su da Turawa, sai kuma abin ya zama a garin gyaran gira aka rasa ido, domin an dawo ana kiran su da kafirai. Wannan ce ta sanya Nasarawa suka yi ruwa, suka tsaki, suka yi uwa- da–makarbiya, wajen janyo hankalin Hausawa da cewa, ku musulmi ne, masu bin Kur’ani, idan kuka duba littafinku za ku ga an kira mu da Nasara ne ba kafirai ba, wannan ce ta sanya wadanda suka hankalta suka Hausantar da sunan Nasara zuwa Nasarawa, wannan ne ma kuma ya sanya ake kiran sunan unguwar da Nasara suka zauna a Kano da sunan Nasarawa.
Sai dai ko a wancan lokacin an samu wadanda ba ruwansu, in dai mutum farar fata, mai jan kunnuwa da kuma gashi yana yalki kuma sanye da suit ko coat, to sunansa Bature, jam’insu kuma Turawa. Wanda har zuwa yanzu da na yi rubutun nan, wasu ba ruwansu don tantance Turawa da Nasarawa. Kuma wasu ma ba su san ko akwai bambamci tsakanin Turawa da kuma Nasarawa ba. Ko Bature da Banasare ba.
A karshe ina fata wannan mukala za ta zama sila da za ta sanya a fahimci bambancin da ke tsakanin Turawa da Nasarawa.

Bashir Musa Liman
Marubuci, Manazarci da kuma sharhi a kan al’amuran yau da kullum.
07036925654
 
 

No comments:

Post a Comment