Waqar Najeriya
Sakamakon halin da Najeriya ta kasance a ciki, sai
na yi nazari haxe da fito da hanyar da komai zai daidaita, a samu zaman lafiya
a qasa. Waqa ce da ta bayyana matsalolin da suka yi cacukwi da kwalar Najeriya
har suke neman farraqa ta. Ina fata za a yi nazarin waqar don a samun romon
darussan da take koyarwa. A sha karatu lafiya:
1 Godiya ga Jallah Sarki xaya,
Da ake bauta masa Shi xaya,
Shi Ya haskaka rana a duniya,
Taimake ni a waqar Najeriya.
2 Salati dubu ga Angon Aisha,
Wanda ya hana aikata alfasha,Kaqi bin sa ka zama shashasha,
A qarshe ka yi kuka da idaniya.
3 A yanzu na kasance cikin qunci,
Idanuna na zafi sun gaza barci,Zuciyata kuwa cike da takaici,
Da na kalli qasata Najeriya.
4 Abubuwa sun sukurkuce,
Tabbas al’amura sun rikice,
Najeriya kuwa ta valvalce,
Ya Ubangiji ceci Najeriya.
5 Yanzu gani ina cikin kuka,
Rayuka na salwanta babu iyaka,Saboda tashin bam babu iyaka,
Haka za a ci gaba a Najeriya?
6 Shugabanni kamar almajirai,
Sun maida‘yan Naija sakarkarai?Kuma tabbas duk sun sani sarai,
Suna ta walawa da kwalliya.
7 Yanzu Arewa ta koma baya,
Tattalin arziqi ya samu karaya,Shugabanninta sun juya baya,
Ga taruka amma babu matsaya.
8 Cacai da baki suna furtawa,
Hanyoyin da zai magantawa,Amma sun kasa aiwatarwa,
Sun koma gefe suna dariya.
9 Al’amarin gobara daga kogi,
Shugabanni sun shiga sabgogi,Sai tarukan banza da na bogi,
To ko yaushe za a yi dariya?
10 Wadatar zuciya, tafi dukiya,
Farin cikin zuciya, yafi dukiya,Ramuwar gayya baya sa dariya,
Zaman lafiya, yafi zama sarauniya.
11 Zuciyata ta shiga harbawa,
Idanuna sun yi ja har da kaxawa,Qwaqwalwata ta shiga sarawa,
Ina ta gudu, ina ta haxa hanya.
12 Idan na tuna sai na ji hawaye,
Annunshuwa da murna sun yaye,Tafiya ta yi tafiya babu tsimaye,
Abubuwa za su daidaita a Najeriya?
13 Yanzu ana barci da ido xaya,
Gudun kada a aikata maka tsiya,An kasa zama tsintsiya guda xaya,
Hakan ya sanya Turawa dariya.
14 Ka shiga mota za ka yi tafiya,
Ga jami’an tsaro sun cika hanya, Riqe da bindiga suna zare idaniya,
Sai su yi harbi su kuma yi dariya.
15 Masu babura suna yin turi,
Wai da babura ake kaiwa hari,Duk da hakan ana kaiwa hari,
Hakan zalunci ko qin gaskiya?
16 Gwamnati ta ce ai tattaunawa,
Boko Haram sun zam amincewa,Qarshe aka sharar da sulhuntawa,
Anya ana so a yi zaman lafiya?
17 Boko Haram za ta zam vacewa,
Inji Jonathan ko me ya yi takawa?Yanzu ga hare-hare na ta qaruwa,
Shugaba ne ko karan-kaxa-miya?
18 A yanzu hankali a tashe yake,
Ta ko’ina ka duba a tsaye ake,Idanun mutane kalle-kalle suke,
Kasancewar qasa ba zama lafiya.
19 Ba ta wutar lantarki ake yi ba,
Ko ruwan sha mai sanyi ake yi ba,Ko a samu hanyoyin motoci ba,
Kai dai a samu zaman lafiya.
20 Mai cin qasa kiyayi ta shuri,
A dava wuqa a ciki ana kirari,Tabbas abubuwa ba sa cikin tsari,
Ana ta yin qwan-gaba-qwan-baya.
21 Idan na kalli wannan duniya,
Samanta rufe yake da samaniya,Ciki har da babban kogin maliya,
An vata komai don rashin gaskiya.
22 Bakuna sun zam rabuwa,
Kan yadda za ai shawowa,Matsalar da ta-qi-cinyewa,
Wayyo Allah! Qasata Najeriya.
23 Cin hanci har da rashawa,
Ka yi aiki har
da gamawa,Kuxin fansho an hanawa,
Har mutuwa babu naira xaya.
24 Jaridu ku tsayar da gaskiya,
Kada ku ba da labarin waskiya,Ko ku riqa goyon bayan qarya,
Kullum ku riqa watsa gaskiya.
25 Amurka mai faxa da ta’addanci,
Har yanzu tana cikin halin firgici,Kasancewar ba ta samun sassauci,
Sai ma barci take yi da ido xaya.
26 Kada ta zuga ‘yan Najeriya,
Har su tsokalo babbar zuliya-Ta dodo mai tsananin qarfin tsiya,
A qarshe a yi ta kuka da idaniya.
27 ‘Yan Kudu suna kira a raba qasa,
Domin Arewa ba ta bunqasa qasa,‘Yan Arewa sun qi yarda a raba qasa,
Sai sharar gara suna sheqa dariya.
28 Jama’a a koma ga Allah,
A tsayar da azumi da Sallah,Da yin nafila don samun falalah,
Allah Zai bada zaman lafiya.
29 Tawassali da Annabin qarshe,
Mai kyawun fata har da harshe,Mai furta kalamai a tausashe,
Allah Ya kawo mana zama lafiya.
30 Bashirun jaridar Aminiya,
Da ya je Kano har da Zariya,Yayan Ahmad da Shamsiyya,
‘Yan Najeriya a zauna lafiya.
31 Tammat a nan zan sa aya,
A waqa mai baiti talatin da xaya,Wadda take kira a zauna lafiya,
Cikin shekarar 2012 aka shirya.
Salam, ina maraba da gyara ko shawara, kasancewar hannu marubuci wane lokaci tamkar makaho yake, sai ya fada wani waje bai sani ba. Na gode.
ReplyDeleteTafdi jam, MANAZARCI, MARUBUCI, KUMA GA BASIRAR WAKA. Mashaallahu barakallahu. Allah ya kara basira.
ReplyDeleteNa gode@Nasir Babi
ReplyDelete