Monday, August 13, 2012

Wakar Zaman Lafiya


WAKAR ZAMAN LAFIYA

Na gabatar da wannan wakar yayin taron da Kungiyar NOA ta yi a dakin taro na Multipurpose da ke Bauchi kan zaben 2011.



Ina farawa da sunan Jallah,
Mai rahama, jin kai da falalah,
Wanda Ya umarci a yi Sallah,
       Taimake ni a wakar zaman lafiya.
 
Dubun salati ga Baban Zara,
Ta hannunsa aka sauke Tabara,
Tawassali da shi a wakar da na tsara,
       A yi ji na fahimta don zaman lafiya.
 
Ina kira a gare ku ‘yan Najeriya,
Ga ni gare ku da zazzakar murya,
Kawace da matsananciyar soyayya,
       Don kira a gare mu a zauna lafiya.
 
Ina tuna kasata, nakan ji takaici,
Zuciyata na kasancewa cikin kunci,
Har na ji na kasa yin daddadan bacci,
       Saboda rikice-rikicen hana zaman lafiya.

A Kudu-maso-Gabas ana ta hatsaniya,
Suna fasa bututun mai da hauragiya,
Tattalin arziki ya zama koma baya,
       Muna cikin talauci, ba zaman lafiya.

Jihohin Najeriya ana sace mutane,
Sai an bayar da kudi a fanshi mutane,
Fargaba ta darsu ga zuciyar mutane,
       Wanda ta haifar da rashin zaman lafiya.
 
A Arewacin kasata har da Maiduguri,
Ana ta rikici na Addini, babu tsari,
Rayuka da dukiya sun bata ba ikrari,
       Wanda hakan ya haifar da kiyayya.
 
A Najeriya ga rikicin Boko-Haram!
Ana cikin garari da garam-garam!
Ga kayan fada ana ta ham-ham!
       Wannan ma ya hana zaman lafiya.
 
Tukunyar zabe na bararrakowa,
‘Yan siyasa suna ta kara sabawa,
Karaf-karaf! Ana ta kara yakewa,
       Bayan zabe za a yi zaman lafiya?
 
Masu iko sun yi ki-mudu-gus,
Wajen bai wa talaka hatsin gus-gus,
Su kuwa suna ta tauna gurus-gus,
       Hakan ya haifar zaman kiyayya.
 
‘Yan siyasa suna alkawartawa,
Idan sun ci zabe za ai morewa,
Suna ci sai su zam bacewa,
       Hakan ma na jawo hatsaniya.

Masu mulki suna sheka mulki,
Wanda ya sa wasu ke take hakki,
Almundahana, danniya da zulaki,
       Wanda ta sa talaka yin gogayya.

Najeriya ta zam tsumman cuta,
Mazalunta, matsafa da macuta,
Kura, damisa har da kwarkwata,
       Sun yawaita a kasata Najeriya.
 
Yawaitar irin wadannan mutane,
Ya haddasa rudani ga mutane,
Har ya zamanto an kasa zaune,
       Face tashin hankali a cikin zuciya.
 
Rayuwa ta zam tabarbarewa,
Al’amura sun zam rikirkicewa,
Komai-da-komai yai kazancewa,
       Sai Lahaula a kasata Najeriya.
 
Talakan kasata yana cikin kunci,
Rayuwarsa tana cikin garari,
Ya kuma kasa samun inganci,
       To, ya za a yi ya zauna lafiya?
 
Masu iko na fashi-da-mukami,
An bar talakawa cikin jimami,
Da warin jiki mai tsabar hamami,
       Ga ruwan hawaye na zuba a idaniya.

Talauci ya sanya fashi-da-makami,
Kana gida ka ga barayi da makami,
A kan hanyar tafiya ma da makami,
       Ka bayar da kudi ka zauna lafiya.
 
Matasa ba aikin yi sai zaga gari,
Ba su da ko sule, balle zancen dari,
Hakan kuwa ya sa su cikin garari,
       Wanda ya sa suke ta hatsaniya.
 
Kuntatawa, makurewa, kassarawa,
Bangajewa, tozartawa, karkashewa,
Tafarfasawa, gasawa da bindigewa,
       An yi wa talakan kasata Najeriya.
 
Addinai sun koyar da zaman lafiya,
To, me ya sa muke ta nuna kiyayya,
Wanda ta sa ga juna ake ta bugayya,
     Me ya sa ga addinanmu  muke juya baya?
 
Ca-cai, ca-cai, a bakunanmu,
Muna kira da mu so junanmu,
 A aikace muna kashe junanmu,
       Da martani irin na ramuwar gayya.
 

Yanzu ga Bashiru dauke da shawari,
Mai kunshe da kyakkyawan tsari,
Wanda zai fisshe mu daga fita garari,
       Mu bi shawarin don mu zauna lafiya.
 
Talakawa su mike don kallawa,
A zabe, a kasa, har da rakawa,
Don ya zamo a kasa an yi walawa,
       Don kuma tabbatuwar zaman lafiya.
 
‘Yan siyasa su san cewa,
A zabe, akwai ci da faduwa,
In sun fadi su zam hukurewa,
       Hakan zai haifar da zaman lafiya.
 
Su kuma wadanda su kai ga dalewa,
Ga mukami, kujera suna masu lilawa,
To, su sauke nauyi da hakkin talakawa,
       Don a samu kyakkyawan zaman lafiya.
 
Matune su tashi don dubawa,
Don hangowa da kuma lekawa,
Don  kiyayewa da kuma gujewa,
       Abubuwan da ke haifar da kiyayya.
 
Masu kudi ku zam taimakawa,
Kayan masarufi ku zam bayarwa,
Taimkon talaka ku ci gaba da yowa,
       Wannan zai sa a samu zaman lafiya.
 
Idan kuka zam kirmishewa,
Kuna ci gaba da kin tallafawa,
Da yin kallo-uku-saura-kwatawa,
       Wa talaka, to za a samu jayayya.
 
Mu so juna, mu kaunaci juna,
Mu ji tausayi, mu taimaki juna,
Mu agaza, mu kyautata wa juna,
       Yin hakan zai sa a zauna lafiya.
 
Idan muna so mu zam walawa,
Bangaranci ya zamto mun wullarwa,
Yarenci da kabilanci, mu zam kaucewa,
              Hakan zai sa a yi daddadar dariya. 
 
Mu ankara da makircin Nasarawa,
Masu hadawa a yi ta gwabzawa,
Su koma gefe, suna ta darawa,
       Burinsu ya cika, ba zaman lafiya.

Jama’a mu guji rudin budurwa Duniya,
Kazamiya, Mamugunciya, Makauniya,
Ashararriya, Iblishiya, Mayaudariya,
       Makaryaciya, Mahillaciya, Mazambaciya.
 
Rudinta ke haifar da kiyayya,
Har ya zamanto ana ta bugayya,
Yaudararta  ta wuce sanayya,
       Ta wani, bare a yi zancen dubayya.
 
Ya kamata mu yo tunani,
Don tantance yanayin zamani,
Don gujewa sharrin Shaidani,
       Wanda ba ya son zaman lafiya.
 
Ya kamata mu zamo nagari,
Don fita daga cikin garari,
Mu kuma tabbata an ci gari,
       Wanda zai sa mu kyakyata dariya.
 
A yi ilmin Addini da na Kimiyya,
Kuma a kasa, idan aka samu tarbiyya,
Mu lura kasa za ta zauna lami-lafiya,
       Da rayuwa ba kwan-gaba, kwan-baya!
 
Kun sai dai Bashiru na fadar gaskiya?
Don a zam an kauce wa son zuciya,
Gaskiya da karya babu a waje daya,
       Tsorona kada a zo, a yi kuka da idaniya.
 

Rokona ga Ubangiji Makadaici,
Mai hallita har da iccen madaci,
Wanda Ya sa har abinci nakan ci,
       Ya sa a kasata a yi zaman lafiya.
 
Tammat a wake na zo karshe,
Don alfamar Annabin karshe,
Dace da ganinsa shi ne karshe,
       Allah Ya sa a samu zaman lafiya.


Ni ne Bashiru Dan Musa ne,
Na Jama’are, Gandun Mashi ne,
Ke ta yin roko a gare ku matane,
       Da ku daure mu zauna lafiya.
 

Jallah Sarki nan nai nufin tsayawa,
A wake mai baituka arba’in da biywa,
Allah tsare ni mugun ji da ganowa,
       Abubuwan da za su haddasa hatsaniya.
 

 Idanuna sun gaza barci
 Rayuwa tana cikin kunci
 Zuciya dauke da takaici
 Ga shi an kasa kaiwa gaci
 Kasa ana ta nuna bambanci
        Ana cikin rayuwa mai muni 
                       

                        Bashir Musa Liman

                   Marubuci, Manazarci da Sharhi kan Adabi.

                   080525255817, 08036925654.

                   diddigi@yahoo.com, gandunmashi@gmail.com.

No comments:

Post a Comment