Tuesday, August 28, 2012

Tarahin kafuwar garin Gombe


 YADDA AKA RADA SUNAN GARIN GOMBE
  Kafin na yi cikakken bayanin yadda aka samu sunan garin Gombe, yana da kyau na yi waiwaye, wanda masu hikimar zance kan ce, shi waiwayen adon tafiya ne. Kwarai kuwa waiwayen da zan yi yanzu yana da matukar muhimmanci, zai kuma zama kamar wata fitila mai haske da zai haska abubuwan da zan zayyano daki-daki cikin makunshiyar sakin layukan da za su biyo baya.
Tarihi ya nuna cikin karni na 14 (14 Century) aka fara sanin garin Gombe, sai dai kafin wannan lokacin an yi wasu mutane masu karama da sarauta da ake kira ‘Soninke Mandigos’, wadannan mutane su ne suka samar da tsatson garin Gombe, kuma ‘Tarekh-el-Sudan’ (mutanen yankin Sudan) ke musu lakabi da ‘Fararen Shugabanni’. Wadannan mutane ana kuma kiran su da ‘Kaya-Manga’. Sun mulki yammacin Sudan na wasu karnoni da dama. A cikin Kaya-Mangan an samu wani mutum da ake kira Bin-Kaya Mob, wanda sarki ne a wata masarauta da ake kira Mande, a dai yammacin Sudan din, wanda kuma wannan sarki ya ci zamaninsa a cikin karni na 10 ne. Sarki Bin-Kaya Mob yana matukar ji da jikansa Bin-Abubakar, wanda har ta kai ko kuda ba ya so ya taba shi. Ya mayar da shi dan lelensa kuma shafaffe da mansa. Hakan ce ma ta sanya Kaya Mob ya bai wa jikan nasa wani bangare na masarautar tasa da ake kira Ukuba.
Bin-Abubakar kaka ne ga Aliyu Ukuba, wanda shi kuma yake mahaifi ga Usman. Aliyu Ukuba shahararren malami ne, ya haddace Al-kur'ani, wanda daga baya aka hada shi aure da 'yar gidan wani attajiri a garin Tibati, inda kuma suka haifi Usman. Usman ya zauna a kauyen Lakumma kusa da garin Shellen, a nan kuma ya ci gaba da wa’azi don a bi addinin musulunci.
Da na yi waiwaye ne  kan tarihinsu game da addinin musulunci, sai na gano masarautar Kaya-Manga sun karbi musulunci daga Abubakar Almarobid (Sanha-ja-Imam) tun a shekara ta 1077, bayan Almarobid ya kafa daular musulunci a wajen.
   Usman Ukuba  ya auri Janaba 'yar gidan Gongon (Amna), wanda shi ne sarkin Shellen. Sun haifi da namiji da aka radawa suna Abubakar a garin Mada (tsohon garin Shellen) a shekarar 1762. Zuri'ar da ake kira KAMBARIJO ke nan. Ma'anar kalmar Kambarijo ita ce zuri'a daga Kaya-Manga da kuma mutanen garin Shellen. Mahaifin Abubakar ya mutu yana yada addinin musulunci a garin da daga baya aka san shi da Gombe, a lokacin wajen yana karkashin masarautar Adamawa ne.
   Bayan mahaifin Abubakar ya rasu ne, sai mahaifiyarsa ta mayar da shi wajen kakansa, wanda a nan ne kakan nasa ya yi masa lakabin 'Buba Yero'. Kalmar Buba na nufin Abubakar yayin da Yero ta samo tsatsonta daga Kanakuru Janafalu, wanda take nufin Manyan ko dara-daran idanu. Kasancewar da ma yana da manya idanuwa. Sannu a hankali, sai lakabin Buba Yero ya danne asalin sunansa na Abubakar Bin-Usmanu. Ya fara karatun Muhammadiyarsa a wajen mahaifinsa, sai dai kuma bayan rasuwar mahaifinsa, sai ya tafi Kukawa a cikin masarautar Barno, inda ya ci gaba da karatun addini.
   A shekarar 1810 ya ziyarci mujaddadi Shehu Usman Dan Fodiyo a garin Degel. Sai dai kafin ya karasa Degel ne ya yada zango a Katsina, inda a nan sarkin Katsina ya ba shi auren 'yarsa Zulai. An yi biki har ma Allah Ya azurta su da da namiji aka masa suna Sulaiman (sarkin Gombe na farko, 1842-1844). Ya sake zuwa a tarihi lokacin da Buba Yero yake zuwa Degel ya yada zango a Daura, inda a nan ma sarkin Daura ya hada shi aure da 'yarsa Hauwa, wadda ita ce mahaifiyar Muhammadu Kwairanga (sarkin Gombe na 2).
    Tarihi ya nuna in ka dauke sarki Sulaimanu da yake da tsatso daga Katsina, sauran sarakunan Gombe tsatson masarautar Daura ne. Buba Yero ya shafe shekaru goma a wajen Shehu Dan Fodiyo, wanda a shekarar 1820 Shehu ya ba shi Tuta ta 5 daga cikin tutoci 12 da ya fara rabawa. Buba Yero ya dawo Shellen daga nan ya ci gaba da Jihadi, har lokacin da Shehu ya dakatar da shi. Daga nan kuma Shehu ya bayar da Kabilar Lala da Yungur da kuma Hona ga Modibbo Adama na Adamawa.
   Daga baya Buba Yero da dan uwansa sun hada hannu da kuma karfi da karfe wajen ci gaba da Jihadi, inda suka ci kabilar Fali da yaki, bayan an yi gwajin kwanji da kuma dauki-ba-dadi a garin Burmi (wanda ake kiran yakin da suna Yakin Burmi na 1). Sun shiga garin Kororofa babban birnin masarautar Jukun, inda a nan Buba Yero ya dora lura da wajen a hannun Hammaruwa, sakamakon zargi da Buba Yero ya yi na cewa za su iya daukar fansa.
   Daga nan sai Buba Yero ya zauna a wani waje da ake kira Gumbol Ribadu, wanda yanzu yake karkashin masarautar Nafada, a cikin shekarar 1814. Ya zauna har tsawon shekara 7. Daga nan ya koma yamma da Dukku, aka rada wa garin suna Gombe-Abba, wanda har yanzu ana kiran garin da haka.
Daga nan Buba Yero ya aiki Magajin Garin Gombe-Abba, da ya nemo masa wajen da zai yi dadin zama. Bayan ya fita nema ne ya samo wani waje kusa da wani tsauni da yake yamma da Dukku, nisan wajen daga Dukku Mil 19 ne.
A nan Buba Yero ya gina gida kusa da wata bishiyar kuka da 'yan kabilar Bolewa masu bauta mata ke kiran ta da Gombe-Memositi. Wasu daga cikin Bolewa sun sauko daga tsaunikansu, suka kuma zauna tare da Fulani (su Buba Yero), daga nan kuma aka fara kiran garin da Guru-Gombe-Memositi. Ana cikin haka kuma sai auratayya ta shiga tsakanin Bolewa da kuma Fulani. Da tafiya ta yi tafiya, sai suka fara kiran garin da suna Gombe.
Bayan an gina garin Gombe ne, sai kuma ya ci gaba da Jihadinsa, inda da shi da dakarunsa, suka karkata gami da sa gabansu arewa. A karshe suka hadu da dakarun Shehu Dan Fodiyo, sannan suka tunkari birnin Ngazargamu (babban birnin masarautar Barno), wanda sun yi hakan ne bayan sun yi galaba a garin Darazo da kuma Logo.
Bayan wannan lokacin ne sai Buba Yero ya samu sabani da dan uwansa Hammaruwa (sarkin Muri 1883), wanda hakan ne ya zama ummul'aba'isin da al'ummar Jalingo suka mika kukansu ga Shehu kan a ba su 'yancin kansu daga kasar Gombe.
Shehu ya karbi kukansu, ya kuma share musu hawaye, inda ya ce da su cikin 'Kirdi' (Fulfulde), cewa ya ba su 'yanci, amma har yanzu sun kasa karbar tutar Jihadi, wannan dalilin ne ya sa har yanzu ake kiran fulanin Jalingo da sunan 'Fulani-Kiri'. Buba Yero ya mutu a shekarar 1841. Buba Yero bai yi mulki ba, ya dai kafa masarautar Gombe ne. Bayan ya rasu ne, aka fara mulkin sarauta, wanda ake kiran sarki da 'Modibbo Gombe'.
Kamar yadda na yi bayani a baya cewa, Buba Yero ya auri Zulai 'yar gidan sarkin Katsina, wanda a kan hanyar sa ta dawowa ne, aka haifa masa Sulaimanu a wani waje da ake kira Shani karkashin ikon Biu, wani gari a masarautar Barno. Sulaimanu ne ya zama sarkin Gombe na farko.
  Bayan Buba Yero ya bar garin Shani ya koma Gulani ne, matarsa ta biyu Hauwa ('Yar sarkin Daura), ta haifa masa da namiji, wanda aka sanyawa suna Muhammadu Kwairanga, wanda kuma shi ne ya zama sarkin Gombe na biyu. Wannan shi ne dalilin da ya sa ake kiran masarautar Gombe da 'Shanima Gulanima Fulbe Janafulu'.

YAKIN BURMI NA BIYU (2/ga watan Jimada Akir,1320 H  daidai da 27-Juli, 1903)
 Wannan yakin yana da matukar mahimmanci a tarihin kafuwar garin Gombe, kasancewar bayan yakin ne garin Gombe ya hau wata turba har zuwa yau. Sai dai kafin nan bari na dan yi baya da mai karatu.
   A zamanin sarkin Gombe na shida wato Umaru (1899-1922), an samu hauhawar kaurar mutane zuwa Gombe, ciki har da korarru da tubabbun sarakunan Arewa, wadanda Nasara masu jajayen kunnuwa suka hambarar. Wadanda suka hada da: sarkin Misau Ahmadu na biyu (1900-1902) da sarkin Keffi Magaji Dan Musa da sarkin Malle Basiru da sarkin Bida da dai sauran masu fada a ji da talakawan da suka sha alwashin ba za su zauna karkashin mulkin Nasara ba. Wadannan mutane sun yi kaura daga garuruwa irin su Kano da Gombe da Bauci da Misau da Bida da sauransu. Sun ce ba za su zauna karkashin gwamnatin Sa Fredrick Lugard ba.
Bayan sojojin Nasara a qarqashin Lugard sun ci karfin Kano da Hadejiya ne, sai suka tattaro hankalinsu garin Gombe, kasancewar sun samu labarin kusan dukkan tubabbu da korarrun sarakuna sun hadu a garin Burmi. Kamar yadda ruwa ba ya tsami a banza haka Nasara ya san tun da wadannan sarakuna suka taru a waje daya, to sun san ko badade, ko ba jima komai zai iya faruwa. Bugu da kari ga Sultan Attahiru ma na garin Burmi. Kuma dama Sultan Attahiru ya samu labarin Faransawa suna jiran sa a tafkin Chadi, kasancewar ita ce hanyar da yake bi, idan zai je aikin Hajji ko Ummara ke nan. Wani zafi-a-kan-zafi kuma shi ne, ga Fadel-Allah (dan gidan Rabeh) da mutanensa suna jiran sa a kudancin Burmi.
Kasancewar garin Burmi ne da yawancin wadanda suka yi Jihadi suke, sai suka yi ittifakin ko da sama da kasa za su hadu, to sun shirya kare Burmi. Wannan shi ne dalilin da Sultan Attahiru ya shirya wata tawaga ta malamai da sojojin yaki da aka sanya wa suna 'Ferol'.
   A ranar 27 ga watan Yulin 1903 Manjo F.C Marsh ya iso garin  Burmi, sannan ya yi sansaninsa a kusa da shiga garin. Bayan ya yi kwanaki uku ne, sai kazamin yaki ya barke a wajen, inda aka yi ta karon-battar-karfe, fito-na-fito da kuma dauki-ba-dadi. Jinin mayaka sun zuba. Inda a karshe sojojin Nasarawa suka yi galaba. Sai dai kuma Sultan Attahiru da kuma Manjo F. C Marsh duka sun rasa rayukansu a yakin da aka yi a garin Burmi. Wanda har a yanzu kuma kaburburansu suna garin na Burmi.
                                          Kabarin Manjo F. C. Marsh da ke garin Burmi
                                            Kabarin Sultan Attahiru da ke garin Burmi
A cikin shekarar 1913 Hedikwatar Gombe ta tashi daga garin Gombe zuwa Nafada, wanda a cewar Nasarawa Nafada ta fi saukin zuwa daga manyan garuruwan Arewa irin su Kano da Bauci da Maiduguri da sauransu. Har ila yau a wannan shekarar aka girke sojoji masu lura da shige-da-fice a kan iyaka.
     Sarkin Gombe Umaru ya halarci wani hawan daba da aka yi a Kano, lokacin da sarki Edward na III ya kawo ziyara Kano. Bayan sarki Umaru ya dawo daga Kano ne, ya sake zabar wani gari da ake kira Doma karkashin Akko. Inda a shekarar 1919 aka sake rada wa garin suna Gombe-Doma. A kuma wannan shekarar ce aka mayar da Gombe-Doma zuwa masarautar Bauci, sannan aka rage mata dagatai zuwa 3, wanda a da take da 13. Daga nan kuma sai aka dawo garin Gombe na yanzu. A karshe ta zama karamar hukuma, a karshen-karshe kuma cikin shekarar 1996 masarautar Gombe ta samu jiha.

 Bashir Musa Liman
 Marubuci, manazarci da kuma sharhi kan al'amuran yau da kullum.
07036925654
diddigi@yahoo.com; ko gandunmashi@gmail.com

No comments:

Post a Comment